Almizan :Za mu kafa dokar yin gwajin jini kafin a yi aure ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Za mu kafa dokar yin gwajin jini kafin a yi aure

In ji Shugaban Karamar Hukumar Ganjuwa

Daga Lawal K/Madaki

H

Majalisar Karamar Hukumar Ganjuwa cikin jihar Bauci, karkashin shugabancin Alhaji Yahya Muhammad Miya za ta bullo da dokar gwajin jini na ma’aurata a yayin da suka zo aure domin gujewa yaduwar cutar kanjamau (AIDS). Shugaban ya furta haka ne ga dimbin jama’ar da suka taru a dakin taro na Karamar Hukumar a yayin da uwargidan Gwamnan jihar Bauci, Hajiya A’isha Adamu Mu’azu ta ziyarci Karamar Hukumar domin wayar da kan jama’a kan cutar kanjamau a ranar wata Talata da ta gabata.

Alhaji Yahya Miya ya ci ga da cewa, Karamar Hukumarsa za ta bullo da wannan doka ne cikin sabuwar shekara mai zuwa, “babu shakka bullo da wannan doka zai taimaka gaya a fagen yaki da wannan mummunar cuta,” ya jaddada.

Har ila yau, Shugaban na Karamar Hukumar Ganjuwa ya ce, suna nan suna shirin nan gaba ya zama magani kyauta ne ga wadanda suka kamu da cutar, kanjamau.

Sannan daga bisani sai ya yi kira ga Sarakuna da masu unguwanni da su gaggauta kawo rahoton duk wani mai dauke da wannan cutar domin daukar matakin gaggawa a kansa.

Sai dai tun farko Shugaban na Karamar Hukumar Ganjuwa, sai da ya danganta cutar kanjamau da cewa tana kara yaduwa ne sakamakon rashin aikin yi daga bangaren su kansu mata, don haka sai ya kuduri aniyar samar da ayyukan yi ga matasa.

Ita ma a nata jawabin, uwargidan Gwamnan jihar Bauci, Hajiya A’isha, godiyarta ta nuna ga Karamar Hukumar Ganjuwa na ganin ta rungumi wannan shiri na yaki da cutar ta kanjamau, wanda take wa jagoranci, kuma ma tuni gwannatin jihar Bauci ta ware tsabar kudi har Naira miliyan 10 domin yaki da wannan cutar.

Jama’a su daina kyamar mai cutar AIDS

In ji Dakta Yusuf Ali

Daga Ali Kakaki (alikakaki2001@yahoo.com)

Wannan ita ce zantawar da ALMIZAN ta yi da Shehin Malami, Shaikh Dakta Yusuf Ali a ranar Talatar da ta gabata a kan ranar bikin masu dauke da cutar (HIV/AIDS) da Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta yi a kwanakin baya domin fadakarwa da wayar da kan jama’a a kan wannan cuta ta alakakai, kanjamau ko Sida da kalmar Faransanci domin kauce wa kamuwa da ita.

Wakilinmu Aliyu Yusuf Kakaki ya shirya hirar a gidan Malamin da ke unguwar Tudun Maliki a Birnin Kano, sannan kuma ya kalato mana daga cikin kaset. Allah ya sa mu amfana, amin. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Wane irin jawo hankali za ka yi a kan mazaje masu yawo suna dauko wannan cuta suna saka wa matayensu kamammu, bayin Allah nagari, musamman ganin yadda cutar ke yaduwa kamar wutar daji a cikin al’umma?

DAKTA YUSUF ALI: ’Yan uwana Assalamu alaikum. To babu shakka a musulunce kuma a kowane irin addini mai wannan hali na zinace-zinace, ya sani yin hakan bai halatta ba, don kuwa saboda ko ma wanda ba su yi imani da addinin Musulunci ba suna kiraye-kiraye kowa ya tsaya tare da abokiyar huldarsa ko wace iri ce, ta aure ce, ko ba ta aure bace. To don menene kai Musulmi ya kasance ka je ka dauko cuta ka sanya wa iyalinka na gida wadanda suna ga Allah suna gare ka kawai? Rayuwarsu gaba daya a kanka take, tunda Allah (SWT ) shi ya dora maka inda yake cewa: “Ya ku wadanda kuka yi imani! Ku tseratar da kanku da iyalanku daga wuta.”

Ka ga kenan kai Maigida ba ma wai masifar duniya ba aka nemi ka tseratar da iyalanka ba, har ma da azabar lahira. To idan ya kasance ka je ka dauko cuta, kuma ka zo ka saka wa iyalanka, babu shakka idan wannan mace ta sha wahala, zunubin yana kanka. Idan ta mutu kuma Allah (SWT) zai dora maka hukuncin kisa. Saboda da gangan mutum ya je ya yi zina, ya kamu da cutar. Allah yana cewa: “Wanda ya kashe mumini da gangan sakamakonsa wutar jahannama ce, zai dawwama a ciki, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa tare da azaba mai girma.” Sannan kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Da a yi sanadiyyar mutuwar mumuni, gara gushewar duniya a wurin Allah.”

Kuma har yanzu Allah (SWT) yana cewa: “Wanda ya kashe mutum daya kamar ya kashe duk mutanen duniya ne.” Saboda haka ya wajaba ga su mazaje muminai su kula da wannan masifa, don ko da ma alhakin kashe macijiya ne, ya yi sanadiyyar kai ta lahira ba tare da hakkinta ba, mutum zai gamu da Allah, to ballantana hakkin kashe mutum.

ALMIZAN: Akwai kiraye-kirayen da ake yi cewa idan mtum ba zai iya kauce wa yin zina ba, to ya rinka amfani da kwaroron roba. Yaya wannan kiraye-kirayen a mahanga ta Musuluci?

DAKTA YUSUF ALI: To ai shi addinin Musulunci, da ma ya san akwai wanda zai shiga wani hali na bukatar yin jima’i , amma ba shi da iko. To in ba shi da iko, yaya zai yi? Annabi (SAW) yana cewa: “Ya ku matasa! Wanda yake da abin aure, sai ya yi aure. Wanda kuma ba shi da hali ya rinka yin azumi, saboda akwai rage sha’awa a cikinsa. To ka ga da da wata hanyar, to da Manzon Allah sai ya fade ta. Saboda haka a cikin wannan hali da ake ciki na wannan cuta ta kanjamau din nan, lalle ne ya kame kansa daga zinace-zinace. Kuma tunda dadewa Malamai sun ce ita ce kadai magani da kuma rage yaduwar wannan cuta.

An samu wani babban Malami, Dakta Muhammad Bar shi ne Likita na farko a duniyar Musulmi da ya yi bincike mai zurfi a kan wannan cuta. Yake cewa ya yi mafarki da Manzon Allah (SAW), sai Allah ya hada shi da Manzo a mafarki ya ce wai menene kariya daga wannan cuta? Sai Manzon Allah ya ce masa kamewa kawai. To in dai namiji ya kame kansa, mace ta kame kanta, to babu shakka wadanda suka kamu da cutar iyakacin cutar kansu za ta tsaya, su warke ko su mutu. Wadanda suka kame kansu ba su kamu ba, to har abada ba za su kamu ba.

Wannan cuta, cuta ce wacce kamuwa da ita sai an ga dama, akwai tsautsayi a kan samu, amma dai-dai ne, jifa-jifa. Amma dai hanyoyin da aka fi yada wannan cuta ta hanyar jima’i ne tsakanin namiji da mace, ko hanyar luwadi tsakanin namiji da namiji, ko ta hanyar madigo tsakanin mace da mace. To wadannan sune hanyoyin da aka fi kamuwa da wannan cuta, amma sauran hanyoyin kamuwa kalilan ne, kamar karin jini, allura da yanke farce. Kuma su maza wadanda suka kamu da cutar, ko su mata in dai mutum ya san yana da cutar, to ya kaurace wa iyalansa ya zama mai tsoron Allah mai gaskiya tsakanin su.

Su ma iyalai su zama masu tsoron Allah, su zama masu gaskiya tsakanin su da mazajensu. Sannan na biyu kuma shi ne sai ka ga yarinya budurwa wacce an auna an ga tana da wannan cuta, amma sai ka ga cewa iyayenta sun zo sun boye, sai a zo a neme ta da aure, amma ba za su gaya wa mutumin ba, kawai sai an daura aure sai mutumin nan ya kamu. Mun sha samun irin wadannan sun zo wajenmu da irin wannan maganar suna da yawan gaske. Ko kuma aurenta ne ya mutu mijin nan wannan cuta ita ta zama ajalinsa, amma ya kasance iyaye su ce, to za mu yi ta zama da ita ne tunda ta samu manema? Sai a matsa mata a zo a daura mata aure.

Haka kuma ta san cewa tana dauke da wannan cuta, su ma sun sani. Wannan yana da yawan gaske. Wallahi tallahi wannan abin takaici ne. Su zo mu ce kar ku yi aure, har sai mun auna mun tabbatar da cewa babu, ana warkewa, kar ku yi da zuci, amma sai mu samu labarin har sun yi aure.

Sai aka samu kuma mace ta san tana dauke da wannan cuta, amma kawai daga ta zo ta karbi magani ta ji ba inda yake mata ciwo, komai ya warke, kuraje babu siffarsu, ta dawo kamar wacce babu wannan cutar tare da ita (HIV) din nan tana nan tare da ita, amma dai duk da haka ta ce aure za ta yi. Kuma za ka samu wasu maza ne suna dauke da cutar, amma dai tunda an riga an sanya masu ranar aure, su da kunya ba za su fasa ba, mu yi, mu yi da su, kawai sai mu samu labarin sun yi auren.

ALMIZAN: Wanne kira kake da shi ga jama’a kan yadda suke gujewa masu dauke da wannan cutar alakakai?

DAKTA YUSUF ALI: Kiran da zan yi ga jama’a shi ne da su ji tsoron Allah su daina kyamar masu dauke da wannan cuta, domin su ceto rayukansu da matsananciyar damuwar da ke damun su a kodayaushe na bakin cikin kamuwa da cutar.

ALMIZAN: Mun gode.

DAKTA YUSUF ALI: Madalla Malam Kakaki, ni ma na gode.

Burinmu shi ne mu sake lashe zabe a Kano

In ji sabon Shugaban jam’iyyar ANPP

“Daukaka jam’iyyar ANPP a jihar Kano da ma kasa baki daya ita ce a gabanmu, musamman ganin shekara ta 2007 tana tinkarowa.”

Wannan kalami ya fito ne daga bakin sabon Shugaban jam’iyyar ANPP ta jihar Kano, Alhaji Sani Hashim a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida kwanakin baya.

Alhaji Sani Hashim ya kara da cewa, “kulen da ke gaban sabbin shugabannin shi ne mu yi kokari mu ga cewa mun hade kan ’ya’yan jam’iyyar wuri guda a Kano da kuma ganin mun sake cin zabe a jihar ta Kano.”

Sabon Shugaban na ANPP ya kara da cewa za su mara wa gwamnati baya don ganin ta kai ga nasara a dukkan aikace-aikacenta na alheri da tasa gaba don taimaka wa al’umma. “Za mu kuma yaki duk wanda yake so ya kawo mana batanci.”

Alhaji Sani Hashim ya jaddada cewa da dan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar ANPP, Alhaji Muhammad Buhari shi ke mulkin kasar nan da ba a samu wahalhalun da al’ummar kasar nan suke ciki a halin yanzu ba, “domin Alhaji Muhammad Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana.”

Ya ce, “idan Allah ya so a matsayina na sabon Shugaban jam’iyyar ANPP ta jihar Kano, za mu rike gaskiya da rikon amana.” Ya kuma yi wa masu gunaguni a kan zabensa da aka yi a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar da cewa shugabanci na Allah ne. “Maimakon haka su zo don hada kai da kuma ciyar da Kano da jam’iyyar ANPP gaba a Kano da ma kasa baki daya.”

Shugaban ya kuma yaba wa al’ummar jihar Kano game da yadda suke bai wa jam’iyyar ANPP goyon baya da kuma Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, “kuma da yardar Allah za mu daidaita sahun jam’iyyar ANPP a Kano.”

Da ya juya ga rigingimun da ke faruwa a jam’iyyar PDP kuwa, sabon Shugaban ya ce son zuciya ne ke kawo haka, kuma har ila yau ANPP a Kano tana mu’amala da dukkan sauran jam’iyyu.

Sai dai wasu mutanen da ALMIZAN ta ji ta bakinsu suna yin gunaguni game da matsayin Sani Hashim a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar ta ANPP a Kano, inda suke cewa sam bai kamata a ce shi ne Shugaban jam’iyyar ba.

Yayin da wasu ke ganin ya kamata a bar wa Alhaji Amadu Haruna Zago ya zama shi ne Shugaban jam’iyyar, yayin da wasu ke ganin kamata ya yi a bai wa Alhaji Ali Datti Yako.

Da’awar Malam Zakzaky ta taimaka mana

In ji Shaikh Ibrahim Gajale Gombe

Wani shahararen Malamin Darika Tijjaniya, wanda ke unguwar Pantami a garin Gombe mai suna Shaikh Ibrahim Gajale ya bayyana da’awar Malam Zakzaky da cewa ta taimaka wa ’yan Darika Tijjaniyya wajen wayar da kan al’umma kan su waye Iyalan gidan Annabi (Ahlul Baiti).

Malamin ya yi wannan tsokacin ne yayin da wasu sashin ’yan uwa suka kai masa ziyara a gidansa da ke Pantami karkashin jagorancin Shugaban Halkar Pantami, Malam Abubakar Pantami.

Tun da farko Malamin ya shawarci ’yan uwa Musulmi da suka ziyarce shi da cewa su kara yin riko kam-kam da Iyalan gidan Annabi. Malam ya ci gaba da cewa, yin riko da Ahlin gidan Annabi shi ne riko da Musulunci.

Daga nan Shaikh Ibrahim Gajale ya fadi silsilar wasu Waliyai, wanda kuma ya ce dukkansu sun hadu ne a wajen Imam Ali (AS) da Fatima (AS). Haka kuma ya fado tarihin wasu daga cikin Imamai, inda ya yi dogon bayani kan falalarsu da kuma yadda suka fuskanci gallazawa daga wajen mahukuntan zamaninsu, musamman irin musiba da bala’in da Imam Husaini ya fuskanta a hannun Yazidu dan Mu’awiya. Daga bisani ’yan uwa sun yi wa Shaikh Gajale tambayoyi, inda shi kuwa ya ba su amsa mai gamsarwa. Daga cikin tambayoyin wani dan uwa ya tambayi Shehin Malamin shin ko yaya zai kwatanta da’war Malam Zakzaky (H) da ta Shaikh Ahmadu Tijjani (RA) ganin yadda dukkansu sun yi riko da Iyalan gidan Annabi da kuma Jikokin Annabi? Sai Malamin ya kada baki ya ce, “da’awar Malam Zakzaky (H) da ta Shaikh Tijjani jirgi daya ne ya dauko su, domin kamar yadda Malam Zakzaky (H) ke alfahari da Jikokin Annabi, haka shi ma Shehu Tijjani ke alfahari da su.”

Ya kara da cewa, akwai ma inda Shehu Ahmadu Tijjani ya yi tawassuli da Jikokin Annabi guda 11. Ya ce kuma wannan shi ne babban abin da ke alamta cewa Malam Zakzaky waliyyi ne domin duk wani Waliyi, to takamarsa Jikokin Annabi.

Don haka Shaikh Ibrahim Gajale ya yi addu’ar fatan alheri ga ’yan uwan da suka kai masa ziyarar, yana mai cewa wannan (ziyara) karantarwa ce irin ta Annabawa. Wani mummunan hatsarin mota ya girgiza Gwambawa

Mutanen garin Gombe sun shiga cikin juyayi da nuna alhini ga iyalan wasu dalibai ’yan asalin jihar ta Gombe, sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya janyo hasarar rayukan mutane 12, ciki har da shahararren matashin Malamin addinin Musulunci nan, kuma Malami a Jami’ar Maiduguri, Dakta Ibrahim Alkali.

Rahotannin da muka samu daga inda hatsarin ya faru, ya nuna cewa hadarin ya faru ne a garin Dadin-Kowa daidai kan gada.

Wata majiya ta shaida wa ALMIZAN cewa farfelar motar ce ta tsinke inda ta caki kwalta, abin da ya sa motar ta daga sama ta wancankalar da ita gefe daya, inda ta yi ta mirginawa dauke da fasinjoji 18. Nan take mutum tara suka ce ga garinku nan, yayin da sauran taran suka tsira da munanan raunuka, daga bisani uku daga cikinsu su ma suka cika. Ita dai wannan motar mallaka gwamnatin jihar Gombe ce wato ‘Gombe Line.’

Da yake amsa tambayar da Wakilinmu ya yi masa kan cewa ba ya ganin gudu ne mai tsanani ya janyo wannan hatsarin? Wani babban Jami’i a Ma’aikatar sufuri ta jihar Gombe, ya ce “ko kusa wannan hatsari ne Allah ya kawo. Idan ana neman direbobi masu natsuwa, to wannan direba yana ciki, saboda yadda kowa ke yaba masa a kan yadda yake tuki.”

To sai dai a cikin wannan hatsari babban abin da ya fi girgiza Gombawa shi ne rasuwar Dakta Ibrahim Alkali, saboda yadda ya zama mutum daya tilo wanda kullum burinsa shi ne hadin kan Musulmi, don haka ne ma ya zama kowace kungiya daga cikin kungiyoyin Musulmi suka halarci jana’izarsa. Sai dai wata majiya ta shaida mana cewa su Izalawan bangaren Jos ne kawai ba su halarta ba, domin sun ce ba nasu bane.

Da yake tsokaci kan halayen Marigayi Dakta Ibrahim Alkali, Wakilin ’yan uwa Musulmi a garin Gombe, Malam Muhammad Ibrahim cewa ya yi, dukkan Musulmi sun yi rashi saboda yadda yake ba da gudummawarsa ga Musulunci babu dare baba rana, kuma ya kare rayuwarsa kan yi wa addin Musulunci hidima.

Malam Muhammad Ibrahim ya kara da cewa, an yi ta kokarin a hada Dakta Alkali fada da ’yan uwa almajiran Malam Zakzaky (H) da sauran kungiyoyin da ke jihar, amma saboda hangen nesansa sai ya ki amincewa da haka. “Ya sha gaya min cewa shi ba ya goyon bayan haddasa rikici tsakanin Musulmi masu furta kalmar La’ilaha Illallahu,” in ji Malam Muhammad Ibrahim. Ya yi fatan Allah ya ji kan sa shi da sauran wadanda suka rasu a hatsarin.

Wani abu kuma da aka shaidi Marigayi Dakta Ibrahim Alkali da shi ne duk da cewa shi ba Haris bane, amma idan Harisawa sun fito ‘riyada’ (waro motsa jiki), shi ma yana shiga duk kuwa da ya dan manyanta.

Makarantar Fudiyyar Gombe ta yaye dalibai

A karo na bakwai makarantar Fudiyyar Gombe ta yaye dalibai 76. Duk da irin matsalolin da makarantar take fuskanta bai hana ta ci gaba da karantarwa ba, tare kuma da yaye dalibai 12 a bana. Wannan nasarori da makarantar ta samu ya samu ne saboda irin kwazo da sadaukar wa Malaman Fudiyyar, in ji Malam Muhammad Ibrahim, Wakilin ’yan uwa na Gombe.

Da yake jawabi a wurin bukin yaye daliban, Shugaban kwamitin iyaye da Malamai, Malam Sambo Liberty ya taya wadanda aka yayen murna ne, tare kuma da karfafa gwiwar sauran daliban don ganin su ma sun kara kokari don tafiya sakandire.

Haka kuma Malam Sambo ya yaba wa Malaman na Fudiyya saboda yadda suka sadaukar da lokutansu da kuma basirarsu don ganin sun ilmantar da yaran.

Ya kuma yi wa dukkan makarantu, walau na gwamnati ko kuma masu zaman kansu kule a game abubuwan da ake koyarwa a makarantun Fudiyya, inda ya ce ko kusa dalibansu ba su kama ko farcen ’yan Fudiyya ba.

Malam Sabo ya ci gaba da cewa, “ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ana kawo ’yan wasu makarantun don yin karatu a Fudiyya, amma idan aka ce dan aji biyar ne sai ka ga ba zai iya karatu da ’yan aji biyar din Fudiyya ba, sai dai a sa shi a aji biyu ko uku.” Don haka ya yi kira da babbar murya ga iyayen yara da su tabbatar sun ba da duk hakkokin da ya rataya a wuyansu don ganin dorewar wannan nagartaccen ilimi.

Da ya juya kan wasu ’yan uwa da suke hangen nagartaccen ilimi a makarantu masu zaman kansu kuwa, Malam Sabo Liberty cewa ya yi, “maimakon dan uwa ya je ya rika kashe makudan kudade, kuma babu ilimin, sannan ga gurbacewar tarbiyya, kamata ya yi ya kawo dansa Fudiyya, inda zai samu riba uku. Na farko ga nagartaccen ilmin. Na biyu ga kyakkyawar tarbiyya. Na uku ga kuma uwa-uba lada mai dimbin yawa.”

Shi kuwa a jawabinsa, babban bako mai jawabi, wanda kuma tsohon Hedimasta ne a makarantar, Malam Usman Kwadan ya yaba wa Malaman Fudiyyar ne, tare kuma da jawo hankalin iyayen yaran da su kula da Malaman. Ya kara da cewa duk nasarar da za a samu ta ta’allaka ne a kan tallafawar Malamai.

Haka kuma ya shawarci daliban da su dage su kuma mai da hankali wajen karatu domin bai kamata a ce iyaye suna ta kashe kudadensu, su kuma Malamai suna ba da lokutansu, amma su kuma daliban suna wasa ba.

Dokar sa sutura a ABU za ta yi aiki kuwa?

Daga Sabo Ahmad

Ana gab da za a tafi hutun karshen zango na biyu na wannan shekarar, Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Shehu Usman Abdullahi ya kafa wani kwamiti wanda zai kula da da’ar sa sutura a harabar Jami’ar.

An sanar da kafa wannan kwamitin ne da irin abubuwan da zai kula da su a wata takarda ta musamman da mai yada labarun da suka shafi Jami’ar ya raba wa manema labarai.

ALMIZAN ta jiwo cewa akwai shiga ta rashin da’a nau’i 16 da kwamitin ya bayyana zai yi yaki da su, wanda matukar aka sami dalibi ko ma’aikacin wanan Jami’a da daya daga cikinsu a harabar Jami’ar, za a ladabtar da shi.

Shigar da ka iya zama laifi a harabar Jami’ar sun hada da:- Sa matsattsun kaya wadanda za su bayyanar da siffar jiki, ko sa guntun siket, ko sa kaya masu shara-shara, ko sa yankakkke, ko yaggen jins (wando), ko sa shat ba tare da an balle maballin ba, ko sa singileti kadai, ko barin gashi duguzunzun a ka, ko sa bakin tabarau a aji, ko sa dankunne, ko kitso ga namiji, ko matsattsen siket mai yanka a gaba, ko a gefe wanda ke bayyana tsaraici da dai sauran makamantan wadannan.

Wata dokar da ta kawo ka-ce-na-ce a cikin wadannan dokoki ita ce ta hana duk wani kaya wanda ba zai ba da damar a sa kayan da ake amfani da su a dakin gwajin kimiyya ba.

Tambayar da wasu suke yi ita ce shin wannan doka ta shafi mata masu sa hijabi da nikab kenan, ko kuwa?

Wadannan dokoki da Mataimakin Shugaban Jami’ar ta Ahmadu Bello ya yi tunanin aiwatar da su dokoki ne wadanda za su tabbatar da da’a a makarantar.

Sai dai masu lura da al’amura na ganin matukar Hukumar Jami’ar ba ta yi jan ido ba, to da wuya wadannan dokoki su tabbata. Don haka ana nan ana jiran dawowar dalibai a ga matakin da Hukumar za ta dauka don ta tabbatar da abin da aka fada.

An bude sabon shafi da ‘yahoogroups’ na Harkar Musulunci

Daga Muhammad Sakafa Kano

Sakamakon kiraye-kirayen da ake wa ’yan uwa don su bubbude shafin sakar sama (Website) da kuma zaurukan tattaunawa (Yahoogroups) a cikin Intanet, a yanzu haka an samu wani matashin dan uwa wanda ko gama sakandare bai yi ba, ya bude shafi da kansa wanda zai taimaka wajen yada Harka gwagwarmaryar Musulunci tare da mazhabin Ahlul Bait (AS) a duniya da ya yi masa suna da www.fatimiyyah.faithweb.com.

Shi dai wannan matashin mai hazaka dan shekara 15 da haihuwa, mai suna Shaheed, dalibi ne a makarantar BUK Staff Secondary School.

Kamar yadda suka zanta da Wakilinmu, Shaheed ya bayyana masa cewa ya kirkiri wannan shafi din ne don yada gwagwarmarya, tare da mazhabin Ahlul Bait (AS) a duniya, ganin yadda yanzu makiya Ahlul Bait suke bubbude shafuka a sakar sama inda suke yin karya da kire ga mazhabin da ma’abotanta.

Don haka dalibin ya yi kira ga ’yan uwa da su rinka ziyartar wannan shafin na sakar sama da ya bude mai adireshi www.fatimiyyah.faithweb.com, wanda a yanzu haka yake dauke da takaitaccen tarihin Imam Khomeini da Malam (H) da na Imam Husaini (AS), “wanda a yanzu haka ba a gama zuba masa abubuwa ba,” kamar yadda ya ce.

A wani labarin mai kama da wannan kuma, dan uwa Muhammad Sakafa ya bude zauren tattaunawa a cikin sakar sama (Internet) a kan gwwagwarmayar Musulunci a duniya da kuma sadar da zumunci tsakanin ’yan uwa mabiya mazhabin Ahlul Bait mai dauke da addreshi kamar haka; majalisarharkarmusulunci@yahoogroups.com, don haka yake jan hankalin ’yan uwa da su shiga wannan majalisa don tattauna al’amuran gwagwarmayar Musulunci da yada mazhabin Ahlul Bait (AS) a duniya.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International