Almizan :Wakilcin addini da al’ada a fima-fiman Hausa (3) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Wakilcin addini da al’ada a fima-fiman Hausa (3)

Daga Nasiru Wada Khalil na kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci da ke Kano (Shari’a Court Of Appeal, Kano) (nasiruwada@yahoo.co.uk ).

CI GABA DAGA MAKON JIYA

ZANE: Zannuwan da matan suke sawa akasari matsattsu masu bayyana surar ’ya mace ne, dama yawancin lokuta siket ne. Misali Maryam da ake wa lakabi da Maryam Jan Kunne, ta saka siket matsattse a fim din GIDAUNIYA wanda har shatar kamfanta ana gani. In kuma ba matsattse bane, to kasansa ya sha yanka har zuwa gwiwa, ko kuma in babu yankan ya zamana wani ha’ili (yanki) aka saka mai shara-sharar saka kamar ta abin tatar koko wanda ba zai rufe fata ba, shi za ka ga an sa a kasan Siket din daga gwiwa zuwa kasa. Wannan irin siket din shi mutanen gari suke kira jahannama ga fasinja. Bayan fitowar wannan zani na zamani an samu mata ’yan fim suna amfani da shi a cikin fima-fimansu. Misali Hawwa da ake yi wa lakabi da Hauwa Katanga ta saka irin wannan zanin a fim din KATANGA.

DANKWALI: Mafi yawancin lokuta mata ’yan fim suna karin gashi, kuma su bar kansu babu dankwali. Karin gashin ya tashi kamar a matsayin dankwali ke nan, ko kuma in ba a yi karin gashi ba, to a kona gashin na ainihi a kwantar da shi baya, a bar kan haka a bude gashin shi ne dankwalin. Kadan ake samun masu sa dankwali na yadi su rufe gashinsu.

Dukkanin yanayin da muka ambata guda biyu da na karin gashi da na barin gashi a bude, duk abu ne da Musulunci bai yarda da su ba, kuma tsinuwa ke bin duk mai yin su.

Abin da Alkur’ani ya ambata na yanayin shiga ta ’ya mace shi ne kamar yadda ya zo a cikin Suratul Ahzab aya ta 59, cewa: “Ya Annabi (S.A.W.) ka fada ga matayenka da ’ya’yayenka mata da matayen muminai su kusanta a kansu daga mayafansu.”

Baya ga haka an sami hadisi daga wajen Manzon Allah (S.A.W.) cewa mutum biyu ba za su shiga Aljanna ba, kuma ba za su jiyo kanshin Aljannar ba. Daga ciki akwai matayen da suke sun sa tufa, amma kuma a tsiraice suke, kawuwansu kamar kan tozon rakumi.

Yawanci haka ake samun wasu fima-fiman tun daga farkonsu, kusan har karshensu shiga ce ake yi wacce ta saba wa yanayin shiga ta addinin Musulunci, wadannan fima-fiman sun hada da JIGO da GIDAUNIYA da sauransu. Amma duk da haka a kan sami fima-fiman da sun kubuta daga irin wadanan shigar, sai dai kalilan ne kamar irin su ADDINI KO AL’ADA ? da wasunsu.

Saboda irin wannan shigar da mata suke yi yau da gobe, yanzu ya zamana wajibi ga teloli su rika kallon fim don daukar samfurin dinki da za su rika dinka wa mutanen gari. Baya ga haka akwai wakoki da aka yi su da shiga irin wadannan marasa kyau, baya ga sigar wakar, ga samfurin wadansu nan a kasa cikin jadawali:

No. Sunan Fim Sunan Waka

1. Guda Guda

2. Kwarjini Sa Kamshi

3. Dukiya Hillo

4. Numfashi Soyayya

5. Jigo So jiki da Kamshi

6. Kamala Dokin na Malaitu

7. Rijiya Lajiga Lajiga

8. Bakar Ashana Seminai da wakar goro fari

9. Jahilci ya fi Hauka Salawaitu

2. Bin Iyaye

An sha samu a cikin fima-fimai ka ji ’ya’ya suna yi wa iyayensu gatsali ko martani mai zafi, wannan ba tada ce ta Musulunci ba. Domin Musulunci ya yi hani ga yi wa iyaye furuci mai gautsi ko da uffan ne kuwa, kamar yadda Allah (S.W.T.) ya ce: “Ubangiji ya hukunta kada ku bauta wa kowa sai shi. Ubangiji ya yi umurni da kyautata wa iyaye kyautatawa. Idan dayansu ya isa girma nan gare ka, ko dukkansu su biyu, to, kada ka ce da su affafairan, kada kuma ka yi musu tsawa, ka gaya musu magana mai girma mai taushi. (Surah Al- Isra’i :23).

Misalin irin wadannan maganganu shi ne akwai wani wuri a fim din TUBALI da Ali Nuhu yake cewa da mahaifinsa da yake kokarin ya sakar masa matarsa, shi ne shi Alin ya mike tsaye yake cewa da mahaifin nasa: babu wani addini Yahudiyya ko Nasariyya balle Islam da ya yarda uba ya kashe wa dansa aure. A nan a yanayin da aka yi maganar babu karamci a cikinsa wanda hakan addinin Musulunci ya yi hani a kai, kuma ba za a ce larurar labarin ce fadar hakan ba, domin shi Ali Nuhun ba a marar tarbiyya ya fito a fim din ba.

Har ila yau ana samun fima-fimai da suka nuna biyayya ga iyaye tsantsa kuma ba za ka ga wani rashin karamci a lafazi ko a aikace ba. Misali fim din MADADI da Ibrahim Mai Shinku shi ma mahaifiyarsa take takura masa a kan aurensa, amma babu wani wuri da ya fada mata magana marar dadi, sai dai kullum addu’a yake yi mata. Bayan wannan akwai fima-fimai da dama irin su GASHIN KUMA da ire-irensu.

3. Shari’a

Kotu a fima-fiman Hausa ba a fiya amfani da ita wajen rabon gado, ko sulhu tsakanin ma’aurata, ko zancen shayarwa da sauran abubuwan rayuwar dan Adam na yau da gobe suka kunsa ba. Akasari haddi za a yanke na kisa, sai a jawo aya 45 cikin suratul Al-Ma’idah babu wata maganar binciken yanayin kisan, kamar kisan kuskure ko mai kama da shi ba. A’a sai kisan da ake yi masa kisa, kuma ba za ka ji a hukunci an fito da wani abu na ilimi da ya danganci wannan maganar ba, kamar a kisa in uba ya kashe dansa, babu kisa a kansa da sauran ire-iren wadannan. Kamar su sata da aka yi ba a cikin hirzi ba da sauransu.

Magana irin ta yankan hanzari ba a taba yin ta a kotunan cikin wasan Hausa ba, sai dai hukuncin tsurarsa. Saboda haka ba a nuna yanayin yadda ake tafiyar da shari’ar Musulunci ba.

WAKILCI NA AKIDA

A nan akwai fima-fiman da suka wakilci akida ko koyarwa irin ta addinin Musulunci, musamman a tsofafffin fima-fiman da. Misali; NI MA INA SO (2000) wanda Kwabon Masoyi Production suka yi, ya yi magana ne a kan yadda aure yake a Musulunci. Ma’ana ya fito da illolin dora wa kai a cikin aure abin da bai wajaba ba ko ba rukunin auren ba ne, wadannan fima-fimai sun hada da:

No. Sunan Fim Kamfani koyarwa

1. Farhan Home Alone Kyautatawa miji, iyaye da ’yan uwa

2. Gashin Kuma Iyan Tama Amfanin hakuri

3. Kadaura Jigon Hausa Larurar ilimin ’ya mace a addini da rayuwa

4. Tafarki Al-tablig/Fasaha Bin iyaye

5. Al’umma Al’umma Tawakkali

6. Wata Rana Iyan Tama Illar shan giya

7. Nima Ina So Kwabon Masoyi Aure a Musulunci

8. Addini Ko Al’ada Binta Investment Al’adun Bahaushe da suka saba wa addini 9. Munkar Jigon Hausa Umarni da kyakkyawan aiki

10. Idan Kunne Ya ji Jigon Hausa Tarbiyyar yara da zumunci

NADEWA

Wakilcin Addini da Al’ada a fima-fimai ya karanta saboda kasancewar yawancin masu shirya fima-fiman a yanzu yara ne wadanda shekarunsu ba su kai su iya hango musu illolin abin da suke kwaikwayo ba (Indiyanci, Amerikanci da sauransu). Kuma shekarun nasu ba su isa su tara musu karatu na addinin har da za su fadakar ba ko su wakilci al’adarsu ba. Shi ya sa in ka gama kallon fima-fiman sai ka ga shi ba addini ba, kuma ba al’ada ba, shi ba jemage ba, kuma ba balbela ba, wani abin can dai daban.

IN AN GA TA BARAWO…

Duk idan muka waiwayi wadannan abubuwa da suke faruwa a cikin fima-fiman Hausa na karancin wakilcin Al’ada da Addini a fima-fiman, kuma muka dubi dabi’ar mutane a kan fima-fiman nan, za mu ga cewa mutanen gari su suka saka ko suke tallafa wa yin irin wadannan fima-fimai. Domin irin su suka fi saya, nagarin ba saya suke ba. Irin wannan rashin kasuwar ya sa wani Furodusa da yake fima-fimai masu ma’ana, amma saboda ba riba ya hakura ya komo masu shiriritar. Shi ma ya bi yarima ya sha kida. Sai dai wannan ba zai zama hujja abar dogaro wajen Ubangiji (SWT) ba, don ba za a rasa wata sana’ar ba.

Alal hakika wasu abubuwa da dama da ake nunawa a fima-fimai suna faruwa a gari. To amma duk da haka ba hakkinka bane kai mai shirya fim ka ce sai ka nuna domin nunawar ita kanta tallafa wa aikata mummunar ne. Domin wanda bai san abin ba ko bai iya ba sai ya nemi ya iya. Ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa, “ya ishi mutum zunubi ya zantar da duk abin da ya ji.”

Mun kammala.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International