Almizan : A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693 ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693

YAUSHE MALAM ZAKZAKY ZAI JE KAZAURE NE?

Assalamu alaikum. Don Allah ALMIZAN ina da tambaya ne. Ni kullum sai na ji an ce Malam Zakzaky zai je gari kaza, amma yau kusan shekara 11 kenan har yau Malam Zakzaky bai je garin Kazaure ba. Don Allah yaushe Malam Zakzaky zai je Kazaure ne?

Daga Aminu Kazaure 0802 407 8078

INA MALAM IBRAHIM LADAN GANYE

Assalamu alaikum. Nasiha nake dai ta ga Malam Ibrahim Ladan na garin Ganye a jihar Adamawa. Na fahimci tunda Shugaban Karamar Hukumar Ganye, Fasto Abila ya kai ka Hajji, kuma ya saya maka mota sai ka daina wa’azi a kan zaluncin azzalumai, sai ka kuma kana sukar ‘jilusus istarah’ da ‘kunuti’ da kuma ‘rukiyya’ da ’yan Izala suke yi. Gafarta Malam a ji tsoron Allah dai a ci gaba da yin abin da aka saba, kada kujerar Hajji da kuma mota su hana ka fadar gaskiya.

Daga Sa’idu Ganye Adamawa 0804 391 3924

IN DA HALI A SAN YADDA ZA A YI

Assalamu alaikum. Ina farin ciki da jin dadi da wannan jaridar ALMIZAN. Ina karuwa mai yawa game ga wannan jaridar, yanzu haka ina da kwafi sama da 400 na wannan jaridar, ko aro na bayar sai na san yadda na dawo da aba ta. ’Yan uwa da sauran dangina sun yi ta kokarin su raba ni da wannan Harkar, amma sun gaza, saboda na yi imani da cewa mafita tana hannun Malam Zakzaky. Sai dai kuma abubuwan da na ga kuna bugawa a rubutun da Bala Makosa yake yi sun sa masu sukar wannan Harkar sun kara kaimi. Don Allah in da hali a san yadda za a yi da rubutun. Amma wannan ra’ayina ne.

Daga Khalid Adam Tsamiyar Kara Gezawa jihar Kano

KASASHEN MUSULMI KU YI KOYI DA IRAN

Assalamu Alaikum. Kiran da zan yi ga sauran kasashen Musulmi shi ne; su yi koyi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen karya gwamnatocin danniya da zalunci. Ku karya su face sai sun mika wuya ga gaskiya. Irin wadannan gwamnatoci na-je-ka-na-yi-ka, ’yan kanzagin Amurka da Birtaniya duk su ke jefa kasashen Musulmi cikin bakar wahala da kaskanci, tare da taimakonsu ake bata wa addinin Musulminci suna, don su biya wa iyayengijinsu na Yammacin Turai bukata. Ku bar sauraron farfagandarsu ta karya ta kiyayya ga addinin Musulunci da sauran kasashen Musulmi, musamman kasar Iran, duk makirci ne irin na ’yan mulkin-mallaka.

Daga Hamza Djibo, Bakin babban masallacin babbar kasuwa Niyame, Jamhuriyar Nijar

(djibohamza@yahoo.fr)

ALLAH YA BA KU JURIYA KAN WANNAN AIKIN

Assalamu alaikum. Ina fatan kuna nan lafiya kamar yadda muke lafiya a cikin garin Niamey a Jamhuriyar Nijer. Yaya aiki? Kuma yaya hakuri? Kuma yaya sauran abokan aiki da dukkan ’yan uwa wadanda ake tare da su? Ina fatan dukkanku kuna lafiya tare da iyalanku. Allah ya sa haka, amin. Kuma muna fatan za ku ci gaba da hakuri kamar yadda kuka saba yi. Kuma Allah ya taimake ku, ya ba ku juriya da sabati da tabbata a kan tafarki madaidaci, ya kuma tabbatar da mu da ku gabaki daya a karkashin jagorancin Maulana Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H).

Daga Youssouf Oumarou Yamai Jamhuriyar Nijar (youssoufou80@yahoo.ca)

DON ALLAH KU TAIMAKA

Assalamu alaikum. Al’ummar Musulmi, Harka Islamiyya na da bukatar kudi don gudanar wasu aikace-aikace. Saboda haka don Allah don Annabi ku ba mu za mu yi wa addinin Musulunci aiki. Allah ya sa wadanda muka fadi domin su sun ji.

EFCC GA GWAMNA NYAME

Assalamu alaikum. Shin don Allah me Hukumar yaki da cin hanci da zarmiya, EFCC, take jira da Gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ne, alhali kuwa sun riga sun san irin ta'asar da ya tafka yake kuma ci gaba da tafkawa na zaluntar al’umman jihar Taraba?

To, EFCC ga ki nan ga shi.

Daga Musawa Hamza (musawahamsa@yahoo.com)

GABA DAI GABA DAI IRAN

Assalamu alaikum. Wannan karnin Sharifai ne, don haka ko an ki ko an so, su za su rike duniya a halin yanzu. Gaba dai, gaba dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Allah ya karya Yahudawa, amin.

Daga Alamin DSS Kano 0806 211 2880

INA MAGANAR BINCIKEN OBASANJO NE?

Assalamu alaikum. Abin dariya wai EFCC da binciken Obasanjo, ana wasan biri da dila dai, mu kuma an mayar da mu wawaye. Wai don Allah Nuhu Ribado ina maganar ta kwana ne? Yanzu dai lokaci ya yi da ya kamata mu gane.

Daga Muhammad Aliyu Erena 0805 776 8264

WAMAKKO BA A KAMFEN DA JININ BAYIN ALLAH

Assalamu alaikum. Magatakarda Wamakko kowa ya ja da Allah tasa ta kare, domin fada da addinin ja da Allah ne, kuma ba a kamfen din siyasa da jinin bayanin Allah.

Daga Muhammad Bello Muhammad Legas 0804 503 3596

..A YI WA ’YAN UWA NA SAKKWATO ADDU’A

Assalamu alaikum. Muna barar addu’a ga ’yan uwa na Sakkwato. Lalle na gaba ya yi gaba. Allah ya yi nufin ya faranta ran Maulana Shaikh Ibraheem Zakzaky. Lalle ’yan uwa na Sakkwato Allah ya zabe ku. Allah ya ba mu sabati, amin.

Daga 0804 503 3596

’YAN UWA MATA MU YI KOYI DA FATIMA AZ-ZAHRA

Assalamu alaikum. ’Yan uwa mata mu yi koyi da Nana Fatima da sauran ’ya’yanta Ithna Ashara.

Daga Ramatu PZ Minna 0805 776 8264

KARIN FARASHIN MAI BAI GIRGIZA MU BA

Assalamu alaikum. Karin farashin mai da gwamnatin Obasanjo ta yi bai girgiza mu ba, amma dai abin sani shi ne wannan gwamnatin ’yan koren ’yan mulkin-mallaka ce.

Daga 0805 776 8264

DON ALLAH A KULA DA MATASA

Don Allah gwamnatoci a dauki mataki mai karfi a kan lalacewar matasa. Shaye-shaye sun yi yawa, ga daba da zinace-zinace, sace-sace da sauransu.

Daga 0806 211 2880

ALMIZAN TA RIGA TA YI ZARRA

Assalamu ailaikum. ALMIZAN jaridar ce ta riga ta yi zarra, ba ta da ta daya, ba ta da ta biyu ko ta uku a fadar gaskiya a kan kowa, ga kuma rahusa. ALMIZAN kenan.

Daga 0805 776 8264

HANKALINMU YA DAWO JIKINMU

Assalamu alaikum.. ’Yan uwa Musulmi ya kamata hankalinmu ya dawo jikinmu, mu daina gewaye-gewaye, mu daina kame-kamen ’yan siyasa domin ba za mu samu tsira daga gare su ba. Allah ya taimake mu a kan bin gaskiya, amin.

Daga Shehu Dari Marabar Jos jihar Kaduna 0806 561 8170

MU YI ADDU’A SABODA 2007

Assalamu alaikum. ’Yan Nijeriya mu yi addu’a Allah ya fitar mana da Shugaba na kwarai a 2007. Babu wata addu’a ko dabara da ta fi wannan a ganina.

Daga Abdullahi Muhammad Alaba Rago Legas 0803 227 7253

YARIMA BA KIRA MAI ZAI CI GAWAYI?

Assalamu alaikum. Gwamnan jihar Zamfara, Yariman Bakura ka karbi Naira 10,000 daga jama’a ka ce za ka ba su bashin babura, amma har yanzu babu baburan, to in ba babu baburan ne a sanar da jama’a mana, in dai ba fitina kuma kake so ka haddasa ba a cikin jihar Zamfara.

Daga Aliyu Gusau jihar Zamfara

DA OBASANJO YA ZARCE, GARA SOJA SO DAWO

Mu dai da Obasanjo ya zarce a 2007, gara soja su dawo. Da ma ni ban ga amfanin wannan dimokuradyyar ba.

Daga Muhammad Almusfara (Mr. Indiya) T/Wada Zariya 0803 636 4526

KORAFI KAN RUBUTUN BALA MAKOSA

Assalamu alaikum. Ni ra’ayina shi ne Malam Bala Makosa ka tafi da karfin Allah, Allah na tare da kai Bala Makosa. Karatu kake koyarwa ba batanci ba. Idan mutum dan Sunna ne ya je ya duba a litattafi akwai shi, in kuma shi dan Shi’a ne ya je makaranta akwai shi.

Daga Ibrahim Teacher Funtuwa jihar Katsina

…KU DAINA SANYA RUBUTUN BALA MAKOSA

Assalamu alaikum. A gaskiya ALMIZAN bai dace ku dinga sanya rubutun Bala Makosa ba, saboda sukar Sahabban Annabi (S) yake yi karara. Na fuskaci maganarsa kiyayya ce kawai ba wani abu ba. Don haka mu dai babu abin da za mu ce wa Sahabbai sai dai godiya, domin sun gama yi mana komai.

Daga Mai Kishin Sahabbai Bashir Leda Mandawari jihar Kano 082 437 4173

ALLAH YA SA SUN HUTA

Assalamu alaikum. Allah ya ji kan Shaikh Mustafa Akka da Dakta Hadi Dahiru Bauci, wadanda suka rasu a hatsarin motar da suka yi kwanakin baya a Bauci. Allah ya su sun huta, amin. Muna kuma rokon Allah ya dada kare mana ALMIZAN daga sharrin masu sharri, amin.

Daga A.A.B. Yola 0805 328 0148

ATIKU LOKACI YA YI MANA

Ba zan mance da budaddiyar wasikar da Marigayi Alhaji Wada Nas ya rubuta maka a jaridar WEEKLY TRUST ba, inda a ciki ya yi maka gargadi a kan abin da zai-je-ya-komo a tsakanin ka da Obasanjo. To lokaci ya yi da abubuwa suka fito sarari, ina fatan ka gane kurenka yanzu. Shi kuma Alhaji Wada Nas, Allah ya kyauta makwancinsa, amin.

Daga Ashiru Azare 0806 224 9835

GWAMNA SHEKARAU MUNA GODIYA

Kanawa na godiya Gwamnan Shekarau game da ayyukan raya kasa da kake aiwatarwa a jihar Kano, domin ko dam din Tamburawa kawai ka yi, ai ka fi Daktan Jami’ar Maidugiri aiki.

Daga Abdullahi 0806 084 3285

INA MAI SON YIN MAGANIN ’YAN SHI’A?

Assalamu alaikum. Mai son maganin ’yan Shi’a me ya sa ba ka yi maganin arnan da suke Kano ba, ko kuma ka je ka yi maganin jaridar THISDAY wadda ta zagi Manzon Allah ba? Sai ’yan Shi’a kawai da ka raina. To wallahi ’yan Shi’a da ko ka ki, ko ka so sune gatanka a kasar nan. Don abubuwa da dama na cin zarafin addinin Musulunci ba a yin su ne saboda su. Ko ka yarda, ko ba ka yarda haka abin yake.

Daga Husaini Yahya Isa Gombe da ke zaune a Kurna Kano 0802 509 0472

…ME YA SA KA KASA BUDE WAYARKA

Assalamu alaikum. Mai neman ya yi maganin ’yan Shi’a nake so na tambaya, na ga maganar fatar baki ma kawai ya kasa yarda ya yi da dan Shi’a, ina kuma ga kwamawa?

Daga Hamisu Isa Kaduna

…KOWA YA DEBO DA ZAFI BAKINSA

Masu zagin ’yan Shi’a ku tuna fa su Musulmi ne ’yan uwanku, idan kun dauka su batattu ne, to ku nuna masu hanyar daidai da ya kamata su bi mana. To amma da yake ba manufarku Allah ba, kawai dai kuna so ne su bi ku a wajen yi wa azzalumai biyayya, sai kuka kau da kai ga barin haka, kuka dauki wani abin na daban. To ku mutu da bakin cikinku, kamar yadda magabatanku ba su iya yin komai da Manzon Allah da Iyalan gidansa ba, to haka kuma ku sani sai ’yan Shi’a sun rusa Yazidawan duniya insha Allah.

Daga Abdullahi Gambo Murna Katsina 0802 679 4453

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International