Almizan :Yadda aka bincki gidan Malam Mukhtar Sahabi ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Wakilanmu

Yadda aka bincki gidan Malam Mukhtar Sahabi


Ga kuma cikakkiyar hirar da muka yi da Jagoran 'yan uwa musulmi na garin Kaduna, Malam Muhammad Mukhtar Sahabi, inda ya yi mana cikakken bayanin yadda abin ya faru.

ALMIZAN: Da yake Allah ya sa Malam yana gida lokacin da aka kawo wannan hari. Za mu so mu ji yadda al'amarin ya faru?

MALAM MUKHTAR: To ni dai ranar Juma'a da safe bayan sallar asuba, na dan dade nan cikin masallacin kofar gidana. Bayan na fito ina tsaye ina magana da wani dan uwa, ban ankara ba sai na ji guje-guje. In duba sai na ga sojoji ne da bindiga. Sai da suka zo kusa ne ma sai na ga ashe har da 'yan sanda da kuma 'official' na NDLEA. Da yake ina ganin suna wani dan aiki na kama 'yan kwaya ko masu wiwi ko wani abu da ya yi kama da haka.

To sun zo ta nan Zango, a zahiri abin da ya bayyana gare mu. Suka biyo ta nan Zango. To kuma da yake ni gidana, daga 'Primary' na zango sai gidana. To da suka biyo su a guje, yaran dai da suka biyo sun riga sun wuce, amma sun kama wani yaro a can Zango din, sun ce sun kama shi da 'Exibit,' ko wiwi ne?

Da suka zo nan, 'yan uwa suna nan, wadanda suke zaune nan masallaci, kuma dama an fito salla ne. Sai dai sun hada wuta nan saboda sanyi. Dama 'Naturally' ka ji mutane a guje da bindiga sun zo kanka kana zaune, za ka mike.

Da zuwa kawai sai suka ga samari, sai suka shiga dukan su. To su kuma 'yan uwa suka yi ta kare kansu. To da yake ina gun, sai na zo ina cewa wanene 'Commanding officer' dinsu, ina son in yi magana da shi. Saboda wani lokaci kananan ba hankali gare su ba, da gangan ake sa su su yi haka din.

To a cikin wannan, kafin in san wanene 'in Command,' an yi ta buge-buge. 'Yan uwa in na ce su daina, to amma mutum sai a yi ta dukan sa har a kai shi kasa. Ka ga wani ba zai san lokacin da zai rama ba, ko abin da ake cema 'Responding stimuli' kamar a tsunguli mutum da tsinke, bai san lokacin da zai zabura ba.

Sai wani yake ce mani akwai Shugabansu wani 'Kaftin Amadu,' to shi ne har muka yi magana da shi. Na ce menene ke faruwa? Ya ke ce mani suna 'Joint patrol' na neman kaza. Na ce, to ai mu sanannun mutane ne. Mu ko ala titas ka ba mu wiwi ba za mu sha ba, ballantana ma kana neman 'yan wiwi ka fado nan. Na ce kuma wadannan yaran gidana ne, kuma mu ba boyayyun mutane bane.

Na ce kuma a kan wannan 'Exercise' din, Sarkin Zango ya zo nan gidana ya ce min, wannan yaran dasuke damun mu da sace-sace da shaye-shaye da abubuwa, har da yi wa 'yan mata fyade, wata yarinya an taba yi a nan bayan Firamare din. Sai muka ce mu ma suna takura mana, amma kila mu in mun ce kaza, sai a ce ai dama mu fitinannu ne, don haka muke ta hakuri muna addu'a Allah ya ba mu mafita.

Don haka mu, abin da ba za mu yi, ba za mu taimaki wani azzalumi ya zalunci wani ba, amma in za a hana mugun dabi'ar da yaran nan suke yi, to mune ma aka taimakawa. Na ce, to zan yi mamakin a ce yanzu kuma an zo ana neman wadannan mutanen, sai a zo gidana.

To shi ne suke cewa ai abin da ya kawo mishkila, ko da hakan ne, in an ga mutum da 'Uniform' kuma ya zo, ai ya kamata a tambaye shi ne. Sai na ce, to ai mai 'Uniform' shi kuma in ya zo sai ya shiga dukan mutane da bidiga? To ka tambaye shi mene? Ba tambaya kawai sai duka. To abin da ya kawo wannan hayaniyar kenan.

ALMIZAN: Allah gafarta Malam mun ji an ce har sun biciki gidanka.

MALAM MUKHTAR: Eh, bayan an gama wannan, sun nemi su kama wasu 'yan uwa da suka fafata da su, don sun ji wa 'yan uwa; wani sai da aka yi masa dinki a ka. Wani ya ce mani ma wani soja ya zo ta bayana zai buge ni da bidiga. To shi yas a ma wani dan uwa ya zo ya shiga tsakani, suka shiga dukan sa. Har nake cewa da ka bari su buge ni, ka ga sai ta bayyana cewa dama ga abin da suka zo yi.

To shi ne sai suka ce mani wai cikin 'Report' din da aka ba su wai akwai wani Shaikh a nan Tudun Wada dan Shi'a wanda aka ce yana tara makamai a gidansa kuma yana ta da hankali. Sai yake cewa bai sani ba ko nine. Sai na ce, to ai wadanda suka gaya maka sai su gaya maka sunansa da inda yake, ka ga in nine sai ka yi duk abin da aka ba ka umurni. Sai ya yi waya, ya ce mene sunana? Na ce ba ka ma san sunana ba ka zo gidana? Ai ya kamata ka sani. Kuma ni na san ka san sunana.

Sai ya yi waya ya ce an ce masa shi wannan Shaikh din sunansa Mukhtar, na ce to lallai sunana Mukhtar, amma ni ba Shaikh bane. To shi ne a karshe ya ce daman an yi maganar makamai da ta da hankali, kaza-kaza. Don har ma yake cewa har da su Gwamna Makarfi duk an yi wannan taron da su, kamar yadda yake fada dai. An nuna cewa akwai wani Shaikh mai ta da hankali, suna da makamai kaza-kaza. Na ce, to lallai ban san shi ba, amma sunana Mukhtar, kuma ban yi zaton wannan Shaikh din bane.

Sai ya ce tunda na ce haka ne, yanzu zan yarda su shiga su yi bincike? Na ce zan yarda idan suka ba ni waranti, “search warant.” Sai ya ce lallai ba su da 'Search warant' sai na ce in ba 'search warant' lallai ba zan yarda ba.

Sai yake cewa, to shi saboda labarin da ake bayarwa na karya, kuma yadda ya gan ni tuntuni yadda muke maganar nan, shi ya zama ya rude, ya san abubuwan da aka fada kamar ba haka bane. Nake cewa su ma masu fadan sun san ba haka bane, suna fada ne kawai. Sai ya ce in dai na yarda, sai ya yi wa Ogansa waya, ina ji.

Sai na ce, to amma banda 'Junior Officers' dinka masu haukar nan. Na ce lallai in dai da su ne, to sai dai in ko da karfi. To sai muka shiga da shi Ahmad da wani Abdul-Azee na NDLEA da kuma wani, ko soja ne ko mobayil, ba dai suna a jikinsa, su uku muka je suka duba falona da dakin baki da Bedroom dina da Toilet. To falon iyali daman ba komai. Sai dakin yara. Suka dudduba suka dawo. Dayan dai yana ta surutan banza, amma shi Ogan nasa yana hana shi.

To ya dan rubuta sunana da lambar gida da sauransu. Kuma na ga ya rubuta su gaskiya ba su ga komai ba, kaza-kaza. Har dayan ma yake cewa, “Oga ya za kai wannan, alhali gobe suna iya canzawa su zama wasu abubuwa daban?” Sai na ce, to wa ya gaya maka da kai da ni da shi da kai din za mu kai gobe? Ai komai za ka yi, za ka yi ne kan abin da ka gani. In gobe ta canza sai wani ya ba da 'report.' Kuma kai ana iya yi maka 'Transifer' a mai da kai wata jiha, ko ma wajen Nijeriya. Amma ni ina nan.

To suka gama dai sai suka fita. Kafin nan, a waje an dan samu hayya-hayya. Saboda lokacin da muke magana da su sun baro wadansu wadanda suke can kan titi inda su ka yi fakin, Zango. Sai Malam Mustafa Potiskum ya shigo ya ce yaranka fa sun zo, kuma lokacin 'yan uwa sun taru, an yi yawa. To sai ya fita ya yi masu magana suka koma can baya.

Da muka gama kuma sai ya ce, to mu raka su. Shi ne muka raka su har mota. To amma wannan dan uwan, Usman sai ya zama sun tafi da shi saboda sun ce wai ya balla masu bindiga. Ina ganin wajen dukan sa ne suka balla bindigarsu. To sai suka ce saboda haka dole su tafi da shi. Kuma wai ya doki sojoji. To amma ni dai ban gani ba. Saboda an yi yawa. In ba wannan hakuri, in ba wannan hakuri, in ba 'yan uwa hakuri, in ba su.

Na ce su zauna mu yi magana, mu fahimci meye. Tun da ba hauka bane abin. To daga baya su manyan sun dan sa hankali, wanda ya taimaka abin ya tsaya, domin su yaran nasa sun yi mana rashin kunya sosai. Kuma sun nuna mana rashin mutunci. Kuma lallai irin wannan in dai yana faruwa! To mu dai daga baya muna tunanin za mu tambaya mu yi bincike, ina abin ya samo?

ALMIZAN: Wannan abu an ce an zo kama wasu kwaya ne, sai ga shi abin ya kai ga har da binciken gida. Me wannan yake nunawa kenan?

MALAM MUKHTAR: Yana nuna kila suna da shirin yin haka tuntuni, kuma sai suka samu fursa da kuma zaman ni ina nan, ina gida, kuma na nuna masu sassauci, tunda na ga kamar shi dayan, 'Officer' din na ga mutun ne wanda yake son a fahinci juna. Shi ya sa sai na ga ba wata matsala.

Amma kila daman suna da niyyar su yi hakan. Kuma ni na yarda din da kashin kaina su yi bincike din. Saboda fakam da yawa akan yi mana muguwar farfaganda a hannun mutane. To tunda haka ne mu ma sai mu nuna masu gaskiyar lamarin. Duk wanda yake da bukatar ya san ko mu su waye, sai mu ba shi dama ya zo har gidanmu, in yana son ya kwana zai kwana.

Akwai wani wanda Kirista ne ma dan SSS, wanda ya taba zuwa, farko muka sayo masa Minaral ma ya kasa sha. Sai da ya ga mun sha sai ya sha. A karshe sai ya mike kafa. Ya ce ai shi da tsoro yake ji, an ce masa mu kaza-kaza-kaza ne. Har ya ba ni sunansa da lambar gidansa, ya ce ina iya kai masa ziyara a gidansa. Kuma shi ba ma musulmi bane. To ka ga a kan wannan, duk wani abu da ake gaya masu, to su shiga su gani. Na ce masa mu yaki muke yi balle mu zo mu kawo makamai mu ajiye a cikin gida? Muna fa wa'azi ne, ku ma kun sani. Amma dai ba mu sani ba, ta yiwu wata shiryayyiya ce. Amma dai ga dukkan alamu, don dan uwan ma sun kai shi hedikwatar NDLEA ne a Zariya wanda suka tafi da shi. To ka ga ni sai na ga abin ya zama shirme-shirme. Ya za a yi, ana kama masu wiwi a kama dan uwa? Ai ya zama hauka, kuma a Markaz.

ALMIZAN: Akwai masu ganin cewa harin umurni nr daga sama. Ko haka Malam yake gani?

MALAM MUKHTAR: To an bugo mani waya. Da yake ranar da aka yi abin dama zan yi tafiya, sai na baro, ina nan (Lokoja). To sai ya zama an ce mani, an bugo mani waya an ce Ciyaman ya zo da ko Sakatare ne na Local Government, suna nema na. Aka ce ba na nan. Suka ce ko za su mani waya? Aka ce su bari sai na dawo, saboda ba a san halin da nake ciki ba na tafiya din.

Sune suke gaya wa 'yan uwan da suka taru a wurin (Markaz) cewa lallai sun je wajen SSS Director, sun je wajen Kwamishinan 'yan sanda, amma su sun ce ba su sani ba. To ai wannan ba shi bane karo na farko. Ko lokacin da su Shahid Sabi'u suka yi Shahada su hudu, Gwamna ma ya ce bai sani ba, Kwamishina 'yan Sanda ya ce bai sani ba. Kuma 'yan sanda ne suka zo suka kashe 'yan uwa.

Wani karo da suka taba zuwa kuma suka yi harbe-harbe a nan, an je wajen DPO na Gidan Gayu, an je wajen 'Metro,' kowa ya ce bai sani ba.

To ka ga nan tunda an taba kashe mana mutane, to ka ga kenan kowane lokaci ake so a zo a ci mana mutunci sai a zo a ci mana mutunci, sai kuma kowa ya ce bai sani ba. To ka ga nan gaba, kila idan wani abu ya faru, ai ka ga za mu san wanda ya aiko su ko? Yawwa! Ka ga idan misali, wani ya aika wani wani wuri ya je ya wani abu aka kama wancan din, misali, ka ga ai wanda ya tura shi ya zo ya ce ai shi ne.

Don haka aka ma ni da aka ce dan uwan, NDLEA ne suka tafi da shi, na bar shi in ga me za su yi. Ai na san shi Ogan da ya zo, kuma ya san a gidana aka zo, kuma ko da laifi ya yi, kotu za a kai shi don ba dan kwaya bane, kuma ba a kama shi da wata hujja ba. In mun ga dama ma muna iya kai su kotu mu nemi hakkinmu na cin mutuncin da aka yi. To yana iya yiwuwa suna da wata boyayya ce. Ko kuma bare-barensu ne kawai da zumudi. Ko ma dai menene, duk abin da suka yi, mu dai dama dai ba baya za mu ci ba a kan wadannan abubuwan.

ALMIZAN: To da yake Malam ya ce an sha kawo irin wannan hari, amma su Hukuma suna cewa ba da yawunsu ne ba, ko wane kira Malam zai yi ga Hukuma?

MALAM MUKHTAR: To kamar yadda yake fada an yi taro, kuma ya ce har da shi Gwamna na Kaduna ya sani, cewa akwai wani Shaikh yana tara makamai a gidansa Tudun Wada, Shaikh dan Shi'a. To ka ga kenan ai wannan farfaganda ce. Shi Gwmna na jihar Kaduna, tun kafin ya zama Kwamishina na san shi. Lokacin da yake Kwamishina zamanin Jafaru Isah, mun taba zuwa aka yi wani taro a gidan gwamnati, in ma bai san ni ba, ni na san shi. Kuma ko da yana Gwamna mukan hadu lokaci bayan lokaci a wurare daban-daban. Kuma ko kwanan nan mun hadu wajen jana'izar wasu 'yan uwa samari takwas da suka rasu a hadarin mota a Badiko, mun gaisa.

Saboda haka ni ban san dai menene ba. Sun san mu mun san su, in har akwai wani abu. Kuma misali ai akwai mutane da suke aiki da shi wadanda na sani kuma har yanzu ana gaisawa da su. To ka ga in akwai wani abu, in dai gaskiya ake so, ya kamata a zo a ce mana an ji kaza, a ji daga bagarenmu. Amma irin wannan ba zai yiwu ba, mutum na Shugaban tsaro na jiha a ce a zo gidan wani mutum a yi bincike. Ko a zo gidan wani mutum a yi harbe-harbe. Ko a zo gidan wani mutum a daki yaran gidansa a yi masu jina-jina a tafi da su, amma a ce wai ba wanda ya sani, Kwamishinan 'yan Sada bai sani ba, Darakta SSS bai sani ba, DPO din Unguwar bai sani ba, ba wanda ya sani. Wannan yana nuna kenan nan gaba sai su je su karkashe mutane su tafi abinsu, yadda 'yan fashi ke yi. Alhali ga motocinsu ga komai. Kuma 'Joint Patrol'ne, ga Soja ga 'yan sanda ga kuma NDLEA.

FILIN DANDALIN IYALI

UWA TA GARI

Daga Hajiya Bilkisu Yusif Ali Kano

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) tare da Iyalan gidansa tsarkaka. A duk lokacin da aka ce ‘uwa,’ to ana nufin mace, ba wai lalle sai ta haihu ba. Bil hasali ma yarinyar da aka haifa yau ana iya kiran ta uwa, don ana kyautata mata zato da tsawon rai. Uwa ta gari ita ce wadda kowane namiji yake fatan samu don samun al’umma ta gari.

Mace ta gari ko uwa ta gari ko ‘almar’atus saliha’ wadda Annabi Muhammad (SAW) ya ce “ta fi duniya da abin da ke cikinta,” lalle tana da muhimmanci a rayuwa, tana da rawar a zo a gani kuma a yaba. Kai ita ce ma ginshikin kowace al’umma. Mace, na da matsayi mai girma a addinin Musulunci.

Uwa ta gari ita ce wadda ke dakin mijinta, walau ta haihu ko ba ta haihu ba, amma a nan zan fi karkata zancena ga wadda ta haihu. Uwa ita ce hoton ’ya’yanta, ita ce mudubin ’ya’yanta, ita ce abar duban ’ya’yanta, ita ce makarantar ’ya’yanta, ita ce ke da sitiyarin tarbiyyar ’ya’yanta, ita ce rayuwar ’ya’yanta, ita ce rayuwar ’ya’yanta ta gaba. Don haka ashe dungurungum rayuwar al’umma tana hannunta, don kuwa duk abin nan da na lissafa haka yake ga uban ’ya’yanta. Ita ce mudubinsa, sitiyarinsa, hanyarsa da makamantansu.

To amma duk da matsayin uwa a wannan fanni, ita kadai zikau ba ta da karfin yin abin sai an taimaka mata, shi ne dai rauni da ake ta fada na mace. Da akwai matakai da uwa ta gari ta yi ta wucewa har ta kai da ta karbi wannan kambu nata na uwa ta gari. Haka kuma matakan dai ta yi ta takawa don ci gaba da kare wannan kambun nata na uwa ta gari.

Da akwai matakai da dama wadanda su ta yi ta bi, wasunsu kadai zan iya rubutawa, wasunsu kuwa ku masu karatu ku za ku taya ni don abu ne bayyananne. Haka shafin bai iya daukar abin, don kuwa abin da yawa, wai mutuwa ta shiga kasuwa.

Matakan sun hada da tarbiyya, addini, hakkin kanta, hakkin Maigida, hakkin wanda ke karkashinta,hakkin yaran gida da hakkin dangin miji. Wadannan da ma wasu da dama suna da muhimmanci wajen samar da uwa ta gari. Bari in dau abin daya bayan daya in yi abin a gurguje.

TARBIYYA

Uwa ta gari ba ta rike wannan kambun, sai ta samu asalin tarbiyya ita ma a wajen iyayenta. Ba ta sami matsayin da ta samu ba, sai da ita ma ta bi nata iyayen, haka ita ma nata iyayen sun yi mata tarbiyya ta gari. Don haka ginshikin uwa ta gari shi ne tarbiyya, ita ma ta samu gun nata iyayen, don haka al’umma take alfahari da ita, ’ya’ya, ’yan uwa, miji, al’umma suke murna da jin dadin ta shafe su.

ADDINI

Duk matsayin da uwa ta samu ta gari in har ba ta rike addini ba, to sam-sam bai dorewa don ba ta dora shi a mizani na shari’a ba. Addinin Musulunci shi kadai ne addini daya da ya ba mace ’yancin da take mafarkin samu a rayuwarta. Shi ya girmama ta, ya karrama ta, ya fifita ta fiye da duk inda wani addini ko wasu daidaikun jama’a suka yi mata. Uwa ta gari ita ce ke tsayawa tsayin daka ganin a kan kanta ta kiyaye dokokin Allah na wajibi da na farilla, ta kuma ci gaba da bincike kan addininta da kwadaitar da kanta neman ilimin addinin.

KIYAYE HAKKIN KANTA DA KANTA

Da akwai hakki wanda uwa ta gari take wa kanta da kanta, a takaice dai duk halin da take ciki ba ta yarda ta tauye wa kanta da kanta hakkinta ba. Ta san ita ma mace ce kuwa halitta ce wadda Allah ya halitta domin ta bauta masa. Haka jikinta a kan kansa yana da hakki, don haka shi ma uwa tagari tana ba shi hakkinsa.

HAKKIN MAIGIDA

Uwa ta gari ita ce mai kiyaye hakkin Maigida. Hakkin da ke kan uwargida na Maigida yana da yawan gaske, sai dai in fada a takaice.

TSAFTA: Muhimmiya ce, ita ce matakin farko da uwa ta gari take takawa don rike matsayinta. Tsafta ta hada da muhalli, kama daga dakinta, dakin maigida, shimfida, bandaki, tsakar gida. Yau duk wannan yana bukatar kulawarta, kallon wuraren tsaf yana kara wa maigida farin ciki. Haka tsaftar jiki, kama daga jikinta da jikin ’ya’yanta, tsaftar tufafinta da na ’ya’yanta.

Iya magana, hakuri, kissa, shagwaba, rufa wa maigida asiri, rage surutu, tarerayar maigida, yi wa maigida uziri, daukar zaman aure ibada, duk wani bacin rai da za a fuskanta kar a yi mamakinsa a dauka jarrabawa ce ta Ubangiji, kuma dama an tanadi faruwarsa. Abincin da zai ci a cikinsa ita ce mai kula da tsaftarsa, dandanonsa, ingancinsa da lafiyarsa.

Duk wani abin da zai faranta wa maigida rai a kullum shi take lalube, duk abin da maigida ya ce yana so, to fa sai inda karfinta ya kare. Haka in har maigida ya ce a’a, to ta bari kenan har abada. Duk wani hakkin da Ubangiji ya gindaya mata na mijinta ko na aure ta kare shi. To wannan mata ta fara cika mukamin uwa ta gari kenan, ita ce wadda idan mijinta ya gan ta zai shagalta duk kuwa da irin bacin ran da ke tattare da shi. In fita ya yi yana Allah-Allah ya dawo gida don ya gan ta komai nasa; natsuwarsa, tunaninsa na hannunta.

Haka uwa ta gari ita ce mai rungumar matar da maigida ya auro, ita ta same ta ta dauke ta ’yar uwa, tana faranta mata rai saboda maigidanta. Ta rungumi ’ya’yanta da na kishiyarta ta hada su ta rungume tsakani da Allah ba wai don kissa ko yaudara ba.

Makwabtanta da zama ya hada su tana kokarin kyautata musu tare da kare hakkokinsu. Duk wani abu na muzgunawa tana kokarin kauce masa ko da kalmominta ne, tana iya yin ta ta ga ba ta cutar da makwabtanta ba da su ba.

HAKKIN ’YA’YANTA

Uwa ta gari ita ce wadda ta dau tarbiyyar ’ya’yanta da muhimmancin gaske, duk wani shige-da-ficensu tun suna ’yan miramiransu a kan idonta suke yi. Haka ta sadaukar da kanta domin ’ya’yanta su tashi da tarbiyya ta gari. Uwa ta gari ita ce wadda ta dau ilimin ’ya’yanta da muhimmancin gaske, ta sa wa ’ya’yanta ido don ta ga me suke yi a makaranta tana ba su kwarin gwiwa da shawarwari don su zama ’ya’ya nagari, ta zama daf da su, ita ce abokiyar shawararsu.

Haka siffa ce ta uwa ta gari kan nusar da ’ya’yanta a kan addinin Musulunci. Duk wani hakki na Ubangiji a gun ta ’ya’yanta za su fara gani tun ma kafin su shiga makaranta. Don haka duk wata doka ta Allah tun suna kanana ta riga ta fara nuna musu. Ladabi, biyayya, girmama na gaba, fadar gaskiya, rike amana da wasun wadannan sune uwa ta gari take ta nuna wa ’ya’yanta tun suna kanana.

Haka wasan banza, abokai barkatai, sutura marar ma’ana, kallace-kallace barkatai da wadansunsu da dama sai uwa ta gari take ta kwabar ’ya’yanta. Ba wai uwa ta gari a kan kanta kadai ba, al’umma kaf su yi alfahari da ’ya’yanta.

Uwa tagari ita ce wadda take kiyaye hakkin wadanda ke karkashinta, kamar dai masu aiki ko wadanda suka zo cin arziki ne tana iyakar iyawarta gun duk wanda ke karkashinta, ba ta zalunci. Hakan da take yi shi zai sa ’ya’yanta su ma su lura da yadda ake kyautata wa wanda ke karkashinta tunda dai ita ce ke yi musu jagorar duk abin da za su yi nan gaba.

DANGIN MIJI

Su ma uwa ta gari ba ta watsar da su ba, musamman iyayen miji. Uwa ta gari tana daukar iyayen miji tamkar iyayen da suka haife ta. Duk abin da ta san za ta yi don ta kyautata wa iyayenta, to irin su ne take bi don ta kyautata wa iyayen mijinta. Iyayen mijinta, uwa ta gari ba ta dauke su abokan gaba ba. Duk kuma abin da aka samu akasi ya faru, ta kaddara shi a matsayin rashin fahimta, don haka tana yi wa abin uziri. Girmamawa, ladabi, biyayya, kyautatawa shi ne uwa ta gari ke yi ga iyayen mijinta, da ma duk wanda ya rabi mijin nata.

Haka wanda duk ya yi ba daidai ba, wato a miji ko danginsa, uwa ta gari, cikin hikima da fasahar zance za ta fada musu cikin kwanciyar hankali. Uwa ta gari ta rike ’yan uwan mijinta hannu bibbiyu ba bambanci da nata. Don haka tana tsaye kan duk wani abu na ’yan uwan mijinta, haka a tsaye take a duk yayin da abin farin ciki ya samu dayan ’yan uwan mijinta ko a lokacin da abin bakin cikin ya same su, ta yi uwa ta yi makarbiya kamar dai yadda dan uwansu zai yi da shi.

Uwa ta gari ita ce idon maigida, yaran gida, dangin maigida, yara masu hidima a gida, abokiyar zama wadda miji ya auro, ’ya’yan miji da ma duk wanda ya rabe ta.

In kuwa haka ne, lalle uwa ta gari tana da muhimmanci a cikin al’umma kowacce. Mace za ta yi fatan a ce ita ce uwa ta gari. Don kuwa uwa ta gari wadda duk ta rike abubuwan da na fada tsakani da Allah, ba don yaudara ba, to tabbas za a same ta cikin natsuwa, zaman lafiya, kwanciyar hankali ita da ’ya’yanta da Maigida.

Ba na raba daya biyu, in har uwa ta gari ta rike wannan, to rabo mai tsanani shi zai ja mijinta ga yin wani auren. Ko kuma ya danganta da dabi’ar mijin. Duk wani hali da al’umma ta shiga a yau mafi rinjayen alkaluma rashin samun uwa ta gari ne ya sa ta shiga wannan mawuyacin halin. Uwa ta gari ita ce ta zabi kai wa Allah kara duk halin da ta shiga ciki, sabanin terere da yamadidi da abin da ya same ta. Duk abin da ya zo mata na alkhairi ko na sharri, ta iya bakinta, haka ta san abokin maganarta.

In har ana magana a kan uwa ta gari ita kadai lalle za a jima. Don uwa ta gari ita kadai aka tsaya aka kalle ta za a yi litattafai da dama a kan halinta. Don kuwa sukutum guda ita ce al’umma. Allah ya sa ni da ku ’yan uwa mata mu dawwama a zama uwa ta gari

Dalilai 6 da suka kai Amurka da kawayenta Iraki

Daga Muhammad Mansir (muhammadmansir@iranhotmail.com)

Akwai dalilai da daman gaske da aka dinga bayarwa game da abin da ya kai Amurka da kawayenta kasar Iraki. Amma nan ga guda shida na kawo. Su dai sun ce wai neman makaman nukiliya suka je yi, amma yanzu a zahiri take ba abin da ya kai su kasar ba kenan. Kodayake daga baya sun ce wai suna kokarin tabbatar da dimokradiyya ne a cikin kasar. Haka kuma tun bayan shigar su kasar munanan abubuwa da yawa sun faru wadanda suka bar duniya da alamomin tambaya. Misali daga ciki shi ne irin wulakanci da cin zarafin musulman kasar Iraki da sojojin na Amurka suka rinka yi a gidan kurkukun Abu Ghraib, baya ga kisan kare dangi da sunan suna fada da ’yan ta’adda, baya ga satar man kasar kuma da aka tabbatar da cewa Amurkawan suna yi.

Abubuwa da dama sun faru wadanda sakamakon shigar Amurkawan ne da kawayenta a kasar. Dadin dadawa ma akwai hujjoji kwarara da ke nuna a hakikanin gaskiya babu wasu ’yan ta’adda masu dasa bama-bamai a kasuwanni, ofisoshi, masallatai, makarantu da wuraren taruwar jama’a face su wadannan sojoji na ’yan mamaya, domin sojojin kasar Ingila da aka kama da bama-bamai sanye da kayan Larabawa ya kara tabbatar da wannan.

Wannan ba shi bane abin da nake son na yi magana a kai, a’a, shin wadanne dalilai ne suka kai kasar ta Amurka da kawayenta suka fada wa Iraki da yaki ta hanyar amfani da dalilan bogi? To, dalilan dai suna da yawa, kuma suna da tasiri a wajensu, shi ya sa ma duk da irin Allah wadan da suke fuskanta daga kasashen duniya da ma jama’arsu suka ki janyewa, ga kuma irin asarar kudi da rayukan sojojinsu da suke yi, amma sun ki su daddara. Don haka da walakin goro a miya, ruwa ba ya tsami banza.

Na daya. Kasashen Turai da Amurka suna da arzikin ma’adanai, musamman kuma ga fasahar kere-kere, sai dai Allah bai ba su wadatar arzikin man fetur ba ta yadda zai wadaci bukatar tarkacen kamfanoni da kere-kerensu, don haka sai dai su saya daga kasashen da suke da wannan baiwa ta mai. Haka kuma sun fi kasashen da ke da wannan arzikin bukatar man. Don haka yana daga cikin shirin su yin amfani da wannan dama ta mamaye kasar Iraki don cin garabasar man kasar. Mun ji labarurruka dangane da sojojin mamaya da aka kashe a wajen dibar fetur na kasar, ga kuma tankoki da jiragen dakon mai na ruwa da yawa da labarai suka gabata cewa an cinna masu wuta a kokarin fitar da man daga kasar.

Na biyu. Kowa ya sani cewar Haramtacciyar kasar Isra’ila ita ce uwargijiyar kasar Amurka da kawayenta. Domin tarihi ya nuna mafi yawan masu hawa karagar mulkin kasar Amurka ba su yi nasara ba sai da taimakon Yahudawa mazauna Amurka, musamman da yake su ke mamaye da tattalin arzikin kasar, ga shi kuma an ce jari-hujja. Sakamakon haka kafin su mara wa dan takara baya, sai sun baje masa bukatunsu a faifai ya gani ya yarje, sannan su kuma su shiga kulle-kulle da shige da fice domin dora shi a karagar mulkin kasar ta Amurka. Haka ma tarihi ya nuna Yahudawa suna da matukar tasiri a gidan sarautar Ingila da mahukuntan kasar; nan ma suna taka muhimmiyar rawa. Uwa-uba kasar Ingila ita ce ta jagoranci haihuwar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Haramtacciyar kasar Isra’ila suna da dadaddiya kuma tsararrar manufa ta mamaye yankin Gabas ta Tsakiya wurin da ya hada da kasar Iraki, Siriya, Jordan, Kuwait, Iran, Saudiyya da makamantansu. Tunda kuwa haka ne shigar ’yan mamaya wadanda dukkansu ’yan koren Isra’ila ne yana daya daga cikin cika alkawarin da suka yi wa Yahudawan na kama masu kasar ta Iraki.

Na uku. Wani kwakkwaran dalili da ya kai ’yan mamaya kasar Iraki, kuma suke ganin wajibcin dawwamarsu a wajen shi ne samun sansanin da za su iya amfani da shi nan gaba don fada wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sanannen abu ne cewa ’yan mamaya sun yi amfani da Saddam Husaini domin rusa Jamhuriyar Musulunci, tare da ba shi dimbin makamai, ciki har da masu masu guba, amma aka share shekaru takwas babu alamun nasara gare su, karshe suka janye ba don Allah ba. Haka kuma akwai lokacin da kasar Amurka ta shirya kai wa Iran hari bayan juyin Musulunci da dare, amma cikin hikima ta Allah jiragen suka dinga karo tsakaninsu suna fadowa kasa.

A kullum zullumin su karuwa yake game da ci gaba da kwarewa, tare da karin karfin da Jamhuriyar Musulunci take yi, suna kuma tunanin wannan barazana ce a gare su da komin dadewa ba makawa abin da suke gudu zai faru. Akalla suna tunanin samun sansani kusa da Iran da zai taimaka masu wajan leken asiri, saukin kai hari, tare da shiga Jamhuriyar Musulunci cikin sauki.

To sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, babu yadda za a iya hada mai neman mutuwa a tafarkin Allah da mai neman share wuri don jin dadin rayuwar duniya. Kuma tarihi ma ya nuna mutanen Iran suna kuka ne don a kai su filin daga, iyayensu na sumbatar su da fatan samun shahada, sabanin ’yan mamaya da ake rabo su da kasashensu da kuka don tunanin ba za su dawo ba, iyayensu kuma daga gida suna zanga-zangar a dawo masu da ’ya’yansu.

Na hudu. Baya ga Jamhuriyar Musulunci, kasar Iraki ita ce ke bi wa Iran a tarin Malamai masu tsoron Allah da dakewa a kan gaskiya. Da yawa saboda jajircewarsu ga zaluncin Saddam suka rasa rayukansu, kamar irin su Ayatullahi As-Sadr da makamantansu. ’Yan mamaya suna matukar tsoron Malamai irin wadannan wadanda ba sa kau da idonsu ga azzaluman shugabanni, don a tunaninsu irin wannan ne ya haifar da rushewar gwamnatin Sarki Shah na Iran, shi ya sa suka ga gara ma dai su shigo kasar su fafata da wadannan Malamai da kansu tunda Saddam ya gaza. Mun ga irin yadda suka yi kisan gilla ga Shahid Bakir Hakeem da wasu Malaman, ga kuma irin fafatawar da suka yi da Sayyid Muktada Sadr gaba-da-gaba, wanda har ta kai ga sun tunkari kabarin Imam Ali. Duk da matakan siyasa da Ayatullahi Sistani ya dauka sai da suka kai ga tilasta masa yin kiran al’umma zuwa hubbaren na Imam Ali. Har yau din nan suna dauki ba dadi da Malamai na addini, tare da kawo rarraba tsakaninsu da sunan Shi’a-Sunna, duk da yake sun kasa cin nasara a wannan janibin.

Na biyar. Kasar Iraki Allah ya albarkace ta da kaburburan Zuriyar Manzon Allah (S) da yawa, ciki kuwa ga kabarin Imam Husain (AS), Imam Musa Kazim (AS), Imam Ali bin Abi Talib (AS) , Hazrat Jafar Abul Fadl (AS), Hazrat Zainab bint Ali (AS) da makamantansu dai da yawa, don haka ’yan mamaya sun san irin kimar wadannan wurare a wajen masoya Iyalan Annabi da sauran Musulmi, sannan suna sane da irin dimbin dukiyar da ake tarawa don raba wa mabukata da kuma kula da kushewar ta wadannan bayin Allah.

Ana yi wa wuraren ado da zinari, saninsu da tarin wannan dukiya da kuma kasantuwarsu barayi (’yan mamaya) sai suka jarraba kai hari a wadannan wurare a matsayin gwaji, tunanin cewa idan har suka ci nasarar kai farmaki wadannan wurare ba tare da sun fuskanci mummunan bore ba, to za su iya kai hari hatta ma a masallacin Manzo (S) da Ka’aba babu abin da zai faru. To sun dai jarraba, kuma sun yaba wa aya zaki sun janye ba don Allah ba, don kuwa ko a Lebanon Sayyid Hasan Nasarullah cewa ya yi kowa ya saka likkaffaninsa ya fito.

Na shida. Har ila yau suna amfani da wannan dama ne domin cin mutunci ga al’ummar Musulmi. Wannan ne ma ya sa suka rinka yi wa Musulmi tsirara a gidan kurkukun Abu Ghraib, tare da yin dalarsu da ba su naman alade suna ci, ko giya suna sha. Wasu abin ma ba su fado. Musamman na bangaren mata Musulmi.

Zan kammala da cewa Allah ya yi alkawarin taimakon Musulmi, kuma alkawarin Allah tabbas ne. A baya ma wasu sun yi abin da ya fi abin da ’yan mamaya suke yi a yau, amma sai da Musulunci ya ga bayansu, ina manyan makiya Allah irin su Fir’auna da Hamana? Ina irin su Shah na Iran da shi kansa Saddam? Wannan dai ba komai bane face karin tabbaci ne na bayyanar Imam al-Hujja (ATF), Allah ya gaggauta bayyanarsa, ya kawo karshen makiya Musulunci a duk inda suke. Ya kara kare mana fitilar da muke hange da haskenta, Maulana Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), amin.

Malam Muhammad Mansir ya aiko mana da wanann sakon ne ta I-mel dinsa muhammadmansir@iranhotmail.com.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International