Almizan :Shugaban mabiya Mazhabar ‘Duruz’ ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Duniya Labari

Shugaban mabiya Mazhabar ‘Duruz’

Ya fara fada tarkon makiya

A wani abu da ake ganin kamar wani nau’in yin shataletale ne ga dan Majalisar nan, kuma Shugaban mabiya Mazhabar ‘Duruz’ a Lebanon, Walid Jamblatt ya fito fili yana kiran Kungiyar jihadi ta Hizbullah da ta daukaka gwamnatin Lebanon a kan ta Syria.

Rahoton tashar talabijin ta AL-JAZEERA ta bayyana cewa a wata ganawa da shi Walid Jamblatt din ya yi da wata tawaga a gidansa ne ya kirayi Kungiyar ta Hizbullah da ta soma tabbatar da biyayyarta ga kasar ta Lebanon kafin ta nuna goyon bayanta ga kasar Syria.

Tashar talabijin din ta AL-JAZEERA har ila yau ta hikaito jawabin da Sayyid Hasan Nasrullah ya yi a lokacin hirar da ya gabatar, kuma aka watsa kai tsaye ta tashar AL-MANAR, inda yake cewa; “duk wanda ya dauke mu a kan yaki da kasar Syria ya kamata ya sani cewa wanda zai fara asara kasar Lebanon ce.”

Saboda haka ne ma a nan shi Jamblatt yake nuna cewa dole ne Kungiyar ta Hizbullah ta tabbatar da matsayinta ta ’yar kasar Lebanon kafin ta zama mai biyayya ga Syria.

Masu bin diddigin lamurran kasar Lebanon sun bayyana cewa Walid Jamblatt ya fara juyawa ne tun bayan kisan da aka yi wa wani dan Majalisa, kuma dan jarida mai kin jinin Syria, Gebran Tueni a makon shekaranjiya.

Kamar yadda aka sani ne dai a halin da ake ciki, Ministocin da ke wakiltar Kungiyar 'Amal' da kuma Hizbullah ta Sayyid Hasan Nasrullah duk sun fita daga Majalisa saboda nuna fushinsu kan wasu matakai da gwamnatin Lebanon take dauka.

A wani labarin mai kama da wannan kuma, Shugaban Kungiyar Hizbullah, Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana matsayin kungiyar kan janyewar da wasu Ministoci suka yi daga gwamnatin kasar.

A lokacin da yake ba da amsa kan tambayar ko Minstocin da suka fice daga gwamnati daga bangaren Kungiyar Hizbullah za su koma da gidan talabijin na AL-MANAR ya yi da shi, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa wannan abu ne da za a ga natijarsa mafi yawa cikin kwanaki biyu masu zuwa, amma ya nuna cewa cikin tattaunawar da aka yi kan wannan akwai ci gaba mai yawa.

Haka nan kuma Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, Hizbullah da Amal duk sun shardanta ci gaba da zama cikin gwamnati ne idan an yi gyara kan kudurin da ’yan Majalisa suka dauka a zamansu na ranar 12 ga watan Disamba a kan fadada ikon kotun Majalisar Dinkin Duniya mai gudanar da bincike kan kisan Rafik Hariri, ta yadda za ta hada da wasu ma da aka kashe a bayansa.

A wani bangare na hirar da aka yi da shi, Sayyid Hasan Nasrullah ya yi magana kan kudurin nan mai lamba 1559, wanda ya tanadi ficewar kasar Syria baki daya daga kasar ta Lebanon da kuma ajiye makamin Kungiyar ta Hzibulla da Palastinawa da suke da sansani a kasar ta Lebanon.

Sayyid Hasan Nasrullah ya nuna cewa bangare na biyu na kudurin ba shi da farko, kuma dole ne gwamnatin ta Lebanon ta fito ta bayyana wa Majalisar Dinkin Duniya wannan.

Tun bayan kashe tsohon Firaministan kasar ta Lebanon Rafik Hariri ne dai Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suke ta matsa lamba suna amfani da wannan abu wajen ganin sun rage karfin Syria da Kungiyar Hizbullah a kasar ta Lebanon.

A wani ci gaban kuma, a halin da ake ciki gwamnatin kasar Lebanon ta ki amincewa da bukatar kasar Amurka na mika mata wani dan kasar dan Kungiyar jihadi ta Hizbullah, wanda aka saki daga gidan kaso a makon da ya gabata daga kasar Jamus.

Shi dai wannan jarumi dan Kungiyar jihadi ta Hizbullah, Muhammad Ali Hammadi ya kwashe tsawon shekaru 16 a gidan kaso na kasar Jamus bayan an tuhume shi da laifin kashe wani sojan Amurka, yayin da ya yi awon gaba da wani jirgin saman yaki a Beirut a shekara ta 1985.

Ita dai gwamnatin kasar ta Amurka tana so ne ta sake tsare shi a gidan kaso na kasarta bayan wanda ya sha a kasar Jamus.

Sai dai kuma hukumomi a kasar Lebanon sun ki yarda da wannan neman, suna kafa hujja da cewa ai shi Hammadi ya riga ya kammala hukuncin da aka yanke masa a kasar Jamus.

Da ma dai Amurka da Lebanon ba su sanya hannu kan yarjejeniyar nan da ake ce wa , ‘Extradition treaty’ da ta tanadi mika mai laifi a tsakaninsu ba, saboda haka suka nuna cewa me ya sa Amurka ba ta nemi karbar Hammadi tun yana Jamus ba?

Amurka dai na cikin jerin kasashen da suke sahun gaba wajen yayata kare hakkin dan Adam, amma abin da ke faruwa a kasa yana karo da wannan da’awar.

Tsananin Sharon yana kara mana karfin gwiwa ne

In ji Kungiyar Hamas

Daruruwan dubban ’yan Kungiyar jihadi ta Hamas ne suka yi wani gangami a Gazza, yayin da suke bukin tunawa da shekaru 18 da kafa Kungiyar, kuma Kakakin kungiyar ya tabbatar da cewa hare-haren Sharon ya kara masu karfin gwiwa da karbuwa ne a cikin al’umma.

’Ya’yan Kungiyar ta Hamas dai sun gabatar da wannan gangami ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan sallar Juma’a, inda suka yi dandazo a gaban wani dogon yaron soja da ya yi shahada a yankin Gazza.

Wadanda suka yi gangamin sun rika daga tutocin Kungiyar ta Hamas suna rera taken Kungiyar, tare da bayyana wasu take da ke nuna ci gabansu da gwagwarmaya har zuwa samun nasara kammalalliya.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Kakakin Kungiyar Hamas, Malam Mushir Al-misri, ya jaddada cewa dukkanin tsananin da gwamnatin Ariel Sharon ta rika nuna wa ’ya’yan Kungiyar tasu ta hanyar kai masu hare-hare da makamai masu linzami ba wani abu da ya kara masu face karfi da kuma kara karbuwa tsakanin al’umma.

A wani bangare na jawabin nasa, Kakakin ya mai da martani kan tsoma bakin da Amurka da Kungiyar hadin kan kasashen Turai suke yi kan zaben ’yan Majalisa na kasar ta Palastinu da za a soma daga ranar 25 ga watan Janairu na badi, inda ya nuna cewa wannan shiga harkar cikin gidan kasar ne.

Malam Al-misri ya tabbatar da cewa kungiyar ta Hamas ita ce zabin al’ummar kasar ta Palastinu. Ahmadinajad ya hana sa kade-kaden Turai a rediyo da talabijin

Shugaban kasar Iran, Dakta Ahmadinajad ya ba da umurnin kawo karshen sanya dukkanin kade-kaden kasashen Yammacin duniya a gidajen rediyo da telabijin na kasar, abin da zai tuna wa al’ummar kasar ranakun farko na Juyin Musulunci.

Dakta Ahmadinajad ya yi amfani da matsayinsa na Shugaban Hukumar kare al’adun Musulunci ta kasa ne ya ba da wannan umurni. Sannan ya bayyana cewa wannan wani abu ne da aka tabbatar da shi tun a watan Oktoban da ya gabata.

Da ma dai Hukumar gidan rediyo da talabijin ta kasar tun bayan cin nasarar juyin Musulunci a kasar ta fitar da ka’idojin da za a rika bi wajen amfani da dukkanin kade-kade a kafafen watsa labarai a duk fadin kasar.

Ana lura da yanayin shi kansa kidan da kuma yadda aka tsara shi, sannan a fitar da hukuncin da ya dace da shi karkashin koyarwa ta shari’a. Saboda haka ne ma aka sanya masu tace dukkannin wani kaset kafin ya shiga dakin watsa shirye-shirye.

A wannan karon abin da Shugaba Ahmadinajad yake nufi shi ne kara tsayawa a kan wadannan dokoki da kuma kara inganta su.

Shugaban HAMAS ya mai da martani

Kan matakin Kungiyar Turai ta EU

Shugaban kungiyar Hamas, bangaren siyasa, Khalid Mashal ya mai da martani kan matakin kungiyar hadin kan kasashen Turai na yanke dukkanin tallafin da take bai wa Palasdinawa in har kungiyar ta ci zabe, kuma ba ta bar kai wa Yahudawa hare-hare ba.

Khalid Mashal ya bayyana wannan mataki da kungiyar ta EU ta dauka a matsayin shiga harkokin cikin gidan kasar Palasdinu, sannan ya kirayi hukumomin Palasdinawa da kada su ba da kai bori ya hau.

A ranar Lahadin nan da ta gabata ne dai Shugaban tsara manufofin kungiyar ta EU, Javier Salona ya bayyana cewa kungiyar za ta dauki kwararan matakai kan kungiyoyin da suke ce wa ’yan ta’adda in har suka lashe zabe. Salona ya kara bayyana cewa zai masu wahala su ci gaba da ba da gudummuwar da suke bai wa Palasdinawa idan dai ba su bar kai hare-hare ba.

Kamar dai yadda aka sani ne cewa sakamakon zaben da aka gabatar na Kananan Hukumomi ya nuna irin yadda kungiyar Hamas ta sami gagarumar nasara. Wannan abu ya bai wa kasashen Turai da Amurka mamaki, kuma ya kara nuna irin yadda har yanzun al’umma suke tare da kungiyar Hamas.

Haka nan kuma masana sun tabbatar da cewa wannan ya kara fito da hakikanin yadda Yammacin duniya ke mummunan amfani da kalmar dimokradiyya ta fuska biyu, in ta yi daidai da burinsu; sunanta dimokradiyya, amma in ba ta yi ba, sunanta ta’addanci.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International