Almizan :Shekaru 4 da rasuwar Malam Adam Usman Suleja ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
WAIWAYE

Shekaru 4 da rasuwar Malam Adam Usman Suleja

Daga Zakariyya Umar Sanda

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, wannan da ya sa mutuwa ta zama hanyar komawa zuwa gare shi, ya kuma sanya shahada ta zama mafificiyar hanyar komawa zuwa gare shi. Godiya ta musamman ga Malikul Mulk, wannan da nake numfasawa da izini da kuma yardarsa. Ubangijin da ya sanya dadin dandanon daukar rai ga Shahidi, INNA LILAHI WA INNA ILLAIHI RAJI’UN. Allah (T) ka ji kan Shahidan gwagwarmayar Musulunci da sauran muminan da suka riga mu gidan gaskiya da imani tare da kalmar La’ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah (S). Allah (T) shi ne Sarkin da ya yi halitta cikin mahaifa ba tare da ya yi shawara da wacce dan tayin ke cikin cikinta ba.

Shaikh Hasan Saffar

DUKKAN MAI RAI MAMACI NE

Dukkan mai rai, watan wata rana mamaci ne, ko da bai yi imani da Allah ba, ganin a kan idonsa, watakila mahaifansa, ’ya’yansa, malamansa, masoyansa da ya rayu a gabansu, amma ya wayi gari babu su, mutuwa ta dauke rayuwarsu.

Da farko dai kar na je da nisa, ina mai mika gaisuwar ta’aziyyata ga Shugaban Harkar gwagwarmayar Musulunci a wannan nahiya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a bisa dimbin hidimar da ya yi wa Malam Adamu Usman Suleja. Wannan dalibi nasa (mamaci), kama daga yi masa salla har zuwa rakiya zuwa babban gida (makwanci a makabarta). Haka nan kuma ina mai mika gaisuwar jaje da ta’aziyyata ga ’yan uwa da iyalan Marigayi Malam Adamu Suleja. Sannan babbar gaisuwar ta’aziyya ga Da’irar ’yan uwa Musulmi na garuruwan Minna da Suleja, ma’abota amsa kiran gwagwarmayar Musulunci, bisa cika shekaru hudu da rasuwar Malam Adamu Usman Suleja.

A yau muna makokin cika shekaru hudu ne da zubewar daya daga cikin katangar gwagwarmaya a yankin Suleja da Minna, marigayi Malam Adamu Usman Suleja ta hanyar rubuta ta’aziyya a madadin ’yan uwa Musulmi na wannan yankin. A wannan shekarar zan so na dan tabo yanayin kankan da kai (tawali’unsa) nasa. Manzon Allah (S) yana cewa, “ka mori abubuwa biyar kafin abubuwa biyar su riske ka. Na daya kuruciyarka kafin tsufanka. Na biyu lafiyarka kafin cutarka. Na uku wadatarka kafin talaucinka. Na hudu rayuwarka kafin mutuwarka. Na biyar damarka kafin shagalarka.” Wadannan matakai guda biyar, lalle wannan bawan Allah, Marigayi Malam Adamu Usman ya same su.

Yana daga cikin halayen wannan dan talikin, kankan da kai. Malam Adamu ya fi so ya ga komai shi yake yin abinsa da kansa. Yakan so a kodawane lokaci ya kasance mai hidima ga al’umma. A wannan misalin kankan da kansa na ganin ya himmatu da bai wa al’umma agaji da ceton rai a dakin shan magani na Batula Kemis, Malam Adamu Usman shi da kansa yakan dauko mani kwanon abincina daga gidansa har zuwa Batula Kemis, inda nake, ko kuma ya dauki kwano ya zame ya je ya sayo mani abinci da kansa. A lura fa duk da yake ni almajirinsa ne, amma shi ne ya kasance mai mani hidima don kankan da kai.

Daga cikin saukin kansa yakan ce mu ci abinci tare a wasu lokuta, wanda ta nan ne na ma sami ilimi da tarbiyyar ladabin cin abinci. Har ya kai ga na saba in zan ci abinci sai na tankwashe kafafuna ina rike da kwano da hannun hagu. Allah Sarki sabawa da haka ne ya sa da na zo cin abinci da wasu ’yan uwana a gidan wani attajiri sai kawai na zama abin kallo da dariya.

NA KASANCE DA SHI HAR DAUKAR RAI

Lalle duk da matsanancin ciwon da ke tare da shi bai taba nuna kasala ko rauni wajen ibada ba, musamman ma dai ga lamarin Harkar gwagwarmayar Musulunci. Masali a shekarar idin bankwana (idin karshe) ya yi, ya yi yunkurin rubuta takardar sakon goron salla wanda za a raba a idi. Amma ina, sai dai kawai yana fadi ana rubutawa kawai. Allah Sarki, akwai lokacin da ake shirye-shiryen mu’utamar din Minna, amma da jin labarin Amirai na taro a Zariya ya ce a dauke shi zuwa wajen buga waya a Batula Kemist don a tuna masu maganar Minna. A haka dai muka rungume shi gefe da gefe.

Wani abin mamaki da na kara la’akari da shi na tsananin sallamawarsa ga jagorancin Malam Zakzaky (H) shi ne duk da yake a kwance yake salla don tsananin ciwo, ana kawo masa sakon wata addu’a da ta zo masa daga Malam Zakzaky (H), yana budewa ya ga daga Malam ne, kawai sai ya yi birgima ya yi murnar sako daga Malam.

Lalle babu shakka wannan rashin (mutuwa), wata shiyya ce ga ’yan uwa a duk yadda muke, musamman dai mu ’yan uwan da’irorin jihar Neja. Don a gaskiya mu ma wannan aya ta “Lahaula wala kuwwata illa billahil azeem,” Wallahi duk mai rai ya shiga uku matukar bai kyautata dabi’unsa ya bi Allah (T) ba, ya nemi kyakktawar makoma. Mutuwa kadai ta isa bawa tunani. Yanzu kake tinkaho a doron kasa, yanzu ne za ka zama gawa, sai yadda aka juya ka. Lalle tunanin tsayuwar ranar ‘mahshar’ a ranar sakamako ya ishi bawa ya shagaltu da kansa.

WAKIYOYIN DA BA ZA A MANTA DA SU BA

Daga cikin wasiyyoyin da faruwarsu ta jawo wa kiran Malam Zakzaky (H) karin farin jini a garin Suleja a lokacin rayuwar Marigayi (Mallam Adamu), wadanda kuma a sakamakon hakan tare da juriya da sabati da aka samu ta hanyar mika wuya ga dokokin Allah (T), tare da tsayuwa kan abin da yake na kiran gaskiya da shiriya da Malam Zakzaky (H) ke kira a kai, ta hada da wasiyyar dokokin shara (sanitation) a shekarun 1993 wanda a sakamakon watsi da ’yan uwa suka yi da tsattsaurar dokar da Hukumar kafircin kasar nan ta sa a lokacin don ta takura wa al’umma ta hanyar ba su lokacin fitowa, wanda nan take ’yan uwa suka take wannan dokar tare da mutsuttsuke ta, abin da ya sa aka kulle ’yan uwa 15 a gidan yari. Wannan kamun da aka yi wa ’yan uwan ne ya sa aka yi muzaharar kin yarda da wannan doka ta kayyade lokacin sharar. Lalle wannan muzaharar wacce ita ce ta farko da ta fara ratsa zukatan mutane, ta bayyana wannan kiran na Malam Zakzaky a garin Suleja tare da jawo masa farin jini a wajen jama’a.

Sai kuma muzaharar garin Kucillo, wanda ’yan Izala suka dinga aukawa tare da raunata ’yan uwa a sakamakon hare-haren da suke ta kai wa ’yan uwa. Daga karshe aka yi jerin gwano cikin sahu zuwa garin na Kucillo don yin jawabin gargadi ga wadanda suke da hannu wajen shirya wa kiran Malam Zakzaky zagon kasa a garin. Lalle ba za mu manta da wannan muzaharar da aka yi ba.

Domin muzaharar da aka yi ta a shekara 1996, daga garin Suleja tana da tsawon tafiyar mil 12 a kafa, tare da makarori, wanda a sakamakon haka sai da majalisar masarautar gargajiyar Suleja, tare da hukumomin tsaro suka nemi a yi suluhu, wanda ya sa ’yan Izalar garin suka yi hijira har na tsawon kwanaki gaba daya daga garin na Kucillo.

Wannan bawan Allah (Marigayi Malam Adamu Usman) ne ya dinga wayarwa da al’umnar Suleja kai a masallaci wajen ‘firi-huduba’ a lokacin rigimar sarautar Suleja, wanda ta kwashe tsahon shekaru 10 da ta jawo wasu ’yan uwa na jini da dangin jini suka yi gaba da juna don goyon bayan da kowane bangare ke yi wa wanda yake so. Wanda a wannan lokaci dukkanin illahirin Malamai masu wa’azozi a masallacin Juma’a fadar Suleja sun zama marayu. Wasu kuma sun yi hijira ta yadda Juma’a kawai ya zama suke zuwa, sai dai ka ji sautin sakon gwagwarmaya ne kawai ke ta tashi duk da ’yan sandan farin kaya da na kwantar da tarzoma da aka jibgo a karkashin umurnin gwamnatin jihar Neja.

Daga cikin waki’a mafi tsananin da Da’irar Suleja ta fada, ita ce kama Malam Adamu da aka yi a lokacin da aka kame tare da kulle Shugabanmu Malam Zakzaky (H), a makaranta (kurukuku) a kamun da Janar Ta-zarce ya yi masa a shekara 1996. A wannan lokacin Marigayi Malam Adamu yana yi wa al’umma bayani a masallacin Juma’a, a kan dalilin kama Jagoran gwagwarmaya da kuma irin ta’addancin da gwamnati ta yi wa ’yan uwa a sakamakon muzaharar da ’yan uwa suka yi bayan kama Malam Zakzaky (H) da kuma yin Allah wadai da bayanin da Shugaban rundunar ’yan sanda na jihar Kaduna, Alhaji Yakubu Shu’aibu ya yi, inda ya fito fili a gidajen rediyo ya musanta duk wani ta’addancin da aka ce sun yi wa ’yan uwa.

Allahu Akabar! A wannan rana ce Marigayi Malam Adamu ya musanta abubuwan da Kwamishinan ’yan sanda ya fada, ya kuma ce, “muna kira ga al’umma’a, da su zo su gane wa idanunsu harin ta’addancin da gwamnati ta yi wa ’yan uwa Musulmi a Zariya da Kaduna.” Wannan jawabin nasa ya yi shi ne a ranar Juma’a farkon makon, inda ya karyata gwamnatin da ’yan barandanta.

’Yan uwa sun sanya kaset din bidiyo na ta’addancin da aka yi wa ’yan uwa a Zariya a masallacin Juma’a bayan sallar Isha’i ta yadda al’umma’a suka gane wa idonsu abin da gwamnati ta yi. Daga nan ne fa gwamnatin jihar Neja da ’yan barandanta (jami’an tsaro) suka dauki matakin dirar wa Malam Adamu da kuma ’yan uwa na garin Suleja. Daga nan dai sai waki’a ta bude wani sabon salo a Suleja.

ALHAIRIN DA AL’UMMA KE TUNAWA

Yana daga cikin alherai da wannan bawan Allah ya assasa a lokacin rayuwansa ta yadda har yau al’umman garin Suleja ba za su iya mantawa da wannan ba. A shekarar 2000 ne al’ummar garin Suleja suka fada wani hali na lahaula ta yadda ruwan sha ya zama kamar wani lu’u-lu’u, sakamakon yadda garin na Suleja ya zama ba ya samun ruwa daga “Water Board.” Da zarar suna bin Karamar Hukumar Suleja bashi sai su hana jama’a ruwan sha. Dukkan famfuna da aka sa a unguwannin da gefen tituna don amfanin al’umma sun zama sanduna kawai domin ba ruwa, amma sakamakon wani kira da Malam Adamu ya yi a masallacin Juma’a na cewa ruwan famfon nan da aka hana, rayuwar al’ummar garin Suleja na cikin kunci ta yadda matan aure da yara ke ta yawo da kwanoni a unguwanni kamar ’yan gudun hijira, sannan kuma ya kara da cewa ruwan famfon nan fa ba fa nonon uwar wani bane, don haka za a hada famfon nan a gobe, don masu hannu da shuni ba su damu da halin da talakawa ke ciki ba.

A kan haka ’yan uwa suka shiga hada kudi ana sayen kan famfo ana hadawa. Akwai wani yabo da ya fito daga wajen taron ’yan siyasa. Suka ce, “wannan aikin da ’yan Shi’a suka yi sun yake mu, kuma mun kunyata.”

Uwa-uba ga Cibiyar shan magani a cikin rahusa na Batula Chemist da ’yan uwa suka bude don shayar da musakai magani kyauta. A yayin da aka ba su magani sai a ce su yi wa Manzon Allah salati, kuma da wannan ma dai akan yi amfani da ranar mauludodin Imamai, musanman ma dai ranar 20 ga Jimada Thani ta kowace shekara don nuna masu mahimmancin wannan ranar ta farin ciki ga Manzon Allah ta samun Fatima (AS).

Allahu Akbar! A kullum burin da muke da shi bai wuce na kasancewa tare da kai a wajen da kai kake yanzun ba. Muna da yakini tare da tabbacin cewa a yanzu haka kana cikin Aljana madaukakiya, kana girbar abin da ka shuka a zamanka na duniya na shekaru 42. Idan muka tuna irin hidimar da ka rika yi wa Harkar gwagwarmayar Musulunci a karkashin jagorancin Malam Zakzaky (H), tare da sallama wa jagorancin Malam Zakzaky (H) a yayin rayuwarka, ko muka kalli irin tasiri da ci gaban da ka kawo wa Harka a Da’irar Suleja, da ma jihar Neja gaba daya, sai mu kasance cikin bakin ciki da juyayin rabuwa da kai.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da lullube ka da rahamarsa da kara daukaka matsayinka a wajensa, albarkacin Manzo da lyalan gidansa tsarkaka. “Rai, ki koma zuwa ga Ubangijinki, alhali kina mai yarda da abin da ya kaddara maki a duniya abar yardarwa (da sakamakon da za a baki a lahira). Saboda haka ki shiga cikin bayina masu bin umurni a duniya. Kuma ki shiga Aljananta a lahira.”

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International