Almizan :Ina hukuncin matar da take fita ba da izinin mijinta ba? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tambaya da amsa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Maimaitawa

Ina hukuncin matar da take fita ba da izinin mijinta ba?

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.
Ya na amsa tambayoyinku

Malam ina halascin ci abincin nan da ake ce wa karafish (crayfish) ne?

Daga Sani Karamu badawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Akwai wasu ’yan kananan kifaye wadanda yake dama haka nan suke, akan kira su ‘crayfish,.’ Akwai kuma wasu kifayen da ake ce masu ‘shrimp,’ ’yan kanana suna da dan jiki haka marar karfi; duk dai babu laifi da cin su, illa iyyaka kifaye ne wadanda ya halatta a ci.

TAMbAYA: Malam ya halatta na yi aski alhali ina da janaba?

Daga Dawwud Yola 0803 311 4260

SHAIKH ZAKZAKY: babu laifi da haka nan. ba inda aka ce in kana da janaba ba za ka yi aski ba, ko yankan farce, ko abin da ya yi kama da haka nan.

TAMbAYA: Malam mutum zai iya yin sallar Juma’a kawai ko kuwa sai wajibi ne ya sallaci Azahur a ranar Juma’a?

Daga 0803 653 4276

SHAIKH ZAKZAKY: A zamanin ‘gaiba’, lazim ne mutum ya sallaci Azuhur, ya yi Juma’a ko bai yi ba.

TAMbAYA: Malam yara kanana da suka rasu, idan an je lahira za su shiga aljannarsu ne ko dai sai ta iyayensu tunda ba su yi wani aiki ba a duniya?

Daga Muhammad Sani benin Nijeriya 0802 704 3450

SHAIKH ZAKZAKY: Hukuncinsu yana wajen Allah. Allah (T) shi ya san yadda zai yi da su. Amma batun cewa ta hanyar iyayensu, ai ba mu san wannan ba. Da ma ka ce min iyayensu ne za su shiga Aljanna ta hanyarsu. Tunda yake ba su yi wani laifi ba, tana iya yiwu ma su zama maceta ga iyaye, tunda kamar yadda ya zo a cikin addu’ar da akan yi masu, akan ce Allah ya sa su zama mana wadanda za su rigaye mu da rahama. Sai ya zama kenan albarkacinsu mu ma mun samu.

TAMbAYA: Malam wane masallaci ne ya halatta musulmi ya yi sallar Juma’a a cikinsa?

Daga 0802 871 1238

SHAIKH ZAKZAKY: Masallacin da ake ce masa ‘jami’i’ shi ne dama masallacin da ake yin Juma’a din kenan. Ana cewa kamar a gari ya kamata ya zama guda daya ne, kuma kar ya zama tsakaninsa da wani masallacin da nisan da yake da mil shida. Har kuma in aka samu wani masallaci kasa da mil shida, to wanda ya riga yin Juma’a din, to sauran tasu Juma’ar ta fadi, ko sun yi kuma ba su da Juma’a.

TAMbAYA: Malam wani ne ya dauki yarinya ya kama mata gida ya sanya ta yana kwana da ita har ta samu ciki, daga baya iyayenta da ke ta neman ta suka gano inda take, sai suka kai karar mutumin da ya dauke ta kotu. Da aka kama mutumin sai ya tabbatarwa da kotu cewa lalle ya bai wa yarinyar nan sadakinta a hannunta shi da ita, ita ma yarinyar ta tabbatar da hakan. To Malam menene matsayin wannan auren nasu? Shin akwai auren ko babu? Kuma menene matsayin dan da za su haifa? Za a kira shi dan halak, ko kuwa ba dan sunna bane?

Daga Sa’adatu Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: Ga dukkan alamu wannan kes ne yake gaban kotu, kila kotun za su bi matakai su gano tabbaci da kuma ingancin wannan auren, amma ni in ba su aka kawo gabana ba, lalle wannan wani kes ne da ba za ka iya fadin sa da ka ba. Sai idan sune aka kawo min, ni ma na bincika na ga yaya? Yaya aka yi aka yi auren, da kuma sharuddan auren da sauransu.

TAMbAYA: Malam, mutum ne ya yi wa budurwarsa ciki kafin su yi aure, sai kuma ya aure ta da cikin, yanzu haka ’ya’yansu uku. Yaya matsayin auren nasu da kuma ’ya’yan nasu a Musulunci?

Daga Ibrahim Mai Sobo El-Tafseer Potiskum ibsmait@yahoo.com 0803 207 6472

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da muka sani shi ne ba a aure cikin idda. Idan mace tana da ciki, sawa’un ta same shi ta hanyar aure ne, ko ma ta wace hanya ce, lalle sai ta haife za a iya daura mata aure. Kuma idan a wannan hali tana sane, ko kuma wanda ya aure ta yana sane, to lalle shi kenan ba aure a tsakanin su har abada. Saboda haka wannan kes din shi ma irin wanda ya gabata ne, wanda ya kamata a kai shi kotu, a kawo dukkan bayanai da hujjoji. Abin da za mu iya fadi kawai shi ne matsayin shari’a, ba matsayin wannan kes din ba.

TAMbAYA: Malam ina matsayin mutumin da yake karatun Alkur’ani da kuma addu’o’i, amma lebensa ba ya motsawa. Ina matsayin ibadar tasa?

Daga Shu’aibu Dantireda Yako Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: Karatun asirce, ana yin karatu ne ya zama ba a fitar da murya ba, amma lalle zai zama ana karatun, ya zama kamar ana rada, masalan, da shi, radar ba lalle ne ta zama tana da tsanani ba, ta yadda shi dai mutum zai ji yana fadi. Amma ba a yi a zuciya. Saboda haka idan mutum ya yi a zuciya bai fade shi da baki ba, to tamkar bai yi karatu bane.

TAMbAYA: Malam menene hukuncin aske gemu ga Musulmi ?

Daga bashir Y. Sadik K/Mazugal Kano 0803 232 8805

SHAIKH ZAKZAKY: Haramun ne.

TAMbAYA: Rage shi fa?

SHAIKH ZAKZAKY: Shi ma haramun ne, in dai ba ya je ga gemun da kyautatawa bane. Don yakan kasance gemu yakan yi wani irin gaja-gaja haka, masalan, ya zama kwakkwafa shi shi ne gyara gare shi. In ya zama gyara ne, to babu laifi. ba rage shi a kan ba ya so ba.

TAMbAYA: Malam ina hukuncin matar da take fita ba tare da izinin mijinta ba?

Daga 0802 574 3265

SHAIKH ZAKZAKY: Haramun ne, don saboda ita fitar mace sai da izinin mijinta. Amma izini na iya zama ‘ami’, yana iya zama ‘khasi’. Alal misali in ya yi mata izini budadde cewa, in zuwa makaranta ne da zuwa kaza ba ma sai ta tambaye shi ba, ya zama ya halatta ta fita ta tafi kenan.

TAMbAYA: Malam gaskiya ne idan mutum bai fid da zakatul fidiri ba azuminsa zai makale a sama?

Daga Yahya Maye 082 946 2133

SHAIKH ZAKZAKY: Da yawa ya zo haka nan cewa azumi yana lilo ne har sai an yi zakkar fidiri, sannan sai ya hau sama. Wannan ka ga ya nuna cewa zakkar komo ba ta faduwa kenan. In bai fitar ba, sai ya yi gaggawar fitarwa.

TAMbAYA: Idan mutum bai bayar ba na kamar shekaru biyu, zai iya faitarwa?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh mana, ba zai fadi ba sam, sai ya fitar.

TAMbAYA: Malam ina matsayin yara kanana ’yan shekara shida zuwa kasa, domin ina jin idan sun rasu mutane sun je ta’aziyyarsu, sai su ce Allah ya sanya su a kafalar Annabi Ibrahim. Wasu kuma su ce Allah ya hada yaron da uwa ta gari. Malam ya wannan maganar take ne?

Daga Alhaji Aminu Muhammad Shinkafi jihar Zamfara 0804 222 0812

SHAIKH ZAKZAKY: Eh a cikin Ma’athur akwai haka nan, cewa ana cewa Allah sa shi a cikin kafalar Annabi Ibraheem. Amma batun uwa ta gari shi ne ba mu sani ba. Sai dai illa iyaka akan fadi batun Kafalar Ibraheem (AS).

TAMbAYA: Malam ina matsayin azumin mutumin da ya kunna turaren wuta a daki?

Daga Musa Mujahid Unguwar Azara Gwagwalada Abuja 0806 571 9146

SHAIKH ZAKZAKY: Makaruhi ne sa turaren wuta a lokacin azumi. Amma bai karya azumi ba, ya rage masa lada. Turaren wuta ne aka ce, ba a ce hayaki ‘Generally’ ba.

TAMbAYA: Malam ina azumi, zan iya shafa ‘Taiga’ (maganin mura) saboda mura da nake yi?

Daga Musa Mujahid Unguwar Azara Gwagwalada Abuja 08065719146

SHAIKH ZAKZAKY: In dai zai shaka a hancinsa ya wuce masa makoshi, to ba zai yiwu ba. Amma idan misali zai shafa a goshi ne, ko a kirji, babu laifi.

TAMbAYA: Malam da yake ya halatta mutum idan yana azumi ya goge baki da makilin, to Malam zan iya karyar asuwakin dalbejiya danye in goge bakina da shi?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh shi ma ba laifi. Sai dai yi da busasshe ne aka ce ya fi. Amma yi da danyen ma bai baci ba. Illa iyaka dai ya tabbatar da cewa dai bai hadiye ba. TAMbAYA: Malam nakan ga mata idan yara sun yi masu fitsari, sai su yayyafa ruwa su yi salla da kayan. Shin hakan yana halatta?

Daga ’yan uwa na Jahun.

SHAIKH ZAKZAKY: To, akwai dai batun cewa an yi rangwame ga mai shayarwa wadda ba ta da sutura sai guda daya. An yi mata ruhusa ita Khasatan, uwa take ko mai reno. Amma in tana da wani suturar daban banda wannan, zai zama wajibi ta canza shi. Ko kuma ko da ma suturun da yawa, amma tana da bukatar su duka. Alal misali kamar akwai tufar ciki da kuma na waje wanda kuma dole gaba daya ake sa su. Saboda haka ita an yi mata rangwame akan cewa yini guda na fitsarin ya zama ko ta yi salla da shi babu komai. Cikin abin da aka yi rangwame ba a ce yanzu in za ta wanke, in ta yayyafa masa ruwa ya fita ba kenan. ba a ce ana yayyafa ruwa ne ba, wanke shi za ta yi sosai. In tana da wani suturar, dole ta cire wannan ta sa mai tsarki, wancan kuma ta wanke shi fes ya fita, ba ta yayyafa nasa ruwa ba.

TAMbAYA: Allah gafarta Malam, mace ce tana da ciki kuma tana haila sai mijinta ya sake ta. Shin sakin ya yiwu kuwa?

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan wata maga ce wadda Malamai har yanzu ba su tsaya duk gaba daya sun tabbata a kan cewa yana iya yiwuwa mai ciki ta yi haila ba. Wasu na cewa ba zai yiwu ta yi ba, wasu na ganin cewa tana iya yiwuwa ta yi. To amma tana iya yiwuwa ta yi din. Saboda haka abin da dai muka sani shi ne saki a haila bai inganta ba. Saboda haka in ya tabbata haila ne, tabbas haila ne, to bai inganta ba.

Sai mun hadu a mako na gaba da wata tambayar insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International