Almizan :Hanyoyin da Harka Islamiyya za ta sami kudi (2) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Fifita kaburburan Turawa a kan na Sarakunan Musulunci

Gwamnatin Kogi ba ta yi adalci ba

In ji Malam Zakzaky
Daga Musa Muhammad Awwal da Aliyu Saleh

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Ranar Asabar din da ta gabata ne Malam Ibraheem Zakzaky da tawagarsa suka je garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi domin ziyarar Kaburburan Sarakunan Musulunci wadanda Turawan mulkin-mallaka la’anannu suka tattaro su daga wurare daban-daban suka tara su a garin na Lokoja har Allah ya yi ajalinsu a can.

Wadannan Sarakuna dai wadanda suke kwance a can wadanda kuma Malam Zakzaky da tawagar tasa suka ziyarta, sun hada da Sarkin Zazzau Kwasau, Sarkin Zazzau Alu Dan Sidi, Sarkin Kano Alu, Sarkin Bida Abubakar, Sarkin Gwandu Muhammad Aliyu, Sarkin Gumel Ahmadu Dan Abubakar, sai kuma wani Malami wanda shi ma Faransawa suka kamo shi daga kasar Mali suka kai shi kasar Borno, sannan daga bisani suka kawo shi Lokoja, kuma Allah ya yi ajalinsa a can, wato Malam Muhammad Bashir Ibn Umarul Futy.

Wannan ziyara ta Malam Zakzaky ta yi tasiri matuka a zukatan jama’ar wannan gari, musamman ganin cewa ba su taba ganin wani Malami ya kai irin wannan ziyara ba. Wannan ne ma ya sa duk wuraren da Malam ya je, Dattawan da ke wurin sai sanya masa albarka suke yi tare da yi masa fatan alheri. “Allah ya saka maka, Allah ya kara daukaka ka,” in ji wani Dattajo a daya daga cikin wadannan wurare.

Wakilanmu da suke cikin wannan tawaga ta Malam Zakzaky, sun shaida mana cewa Malam Zakzaky ya kai wadannan ziyarori ne a safiyar Lahadi, bayan da ya gabatar da wani wa’azi mai ratsa jiki ga al’ummar garin da dare ran Asabar da ya isa garin.

A cikin wa’azin da Malam ya gabatar, ya bayyana dalilan zuwansa wannan gari. Sannan Malam ya bayar da takaitaccen tarihin abin da ya faru ga wadannan bayin Allah, da abin bakin cikin da ya faru a lokacin da Turawan suka tattara Sarakunan suka wulakanta Alku’ani a gabansu suka daga tutar Ingila tare da nuna cewa daga wannan rana an kawo karshen mulkin Musulunci a wannan kasa.

Saboda haka Malam Zakzaky bai bar jama’a cikin wannan bakin cikin ba, sai da ya yi masu albishirin cewa watan wata rana za a zo wannan gari a yi bikin daga tutar Musulunci, wanda zai kawo karshen mulkin kafirci. Malam na yin wannan abishir sai wuri ya rude da kabbara, ana fadin, “Insha Allahu, Allah ya nuna mana.”

Wakilanmu, Musa Muhammad Awwal da Aliyu Saleh sun sami zantawa da Malam Ibraheem Zakzaky (H) a masaukinsa da garin na Lokoja domin jin karin bayani game da wannan ziyara

Wannan hirar tasu ta tabo batutuwa da dama wanda sai mutum ya karanta zai ji abubuwan da ta kunsa masu ilimantarwa. A ciki Malam ya nuna takaicinsa bisa yadda gwamnatin jihar ta Kogi take ware makudan kudade don kula da Kaburburan Turawa, amma ta bar na Sarakunan Musulunci cikin bola da kazanta. Kada dai mu cika ku da surutai, ga yadda hirar tasu ta kasance kamar yadda Musa Muhammad Awwal ya rubuta mana daga kaset. Allah ya sa mu amfana. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Allah gafarta Malam, za mu so mu ji menene makasudin kawo wannan ziyara a wannan gari daidai wannan lokaci?

MALAM ZAKZAKY: Bismillahir rahmanir raheem. Da ma akwai wani taron da aka yi a wannan shiyya, wata kamar uku da suka wuce a Anyingba, wanda a lokacin an yi domin wannan sashe ne na kasa, wanda ’yan uwa da dama suka halarta. To a lokacin su sun so daidai wannan lokacin mu zo nan Lokoja a ziyarci wadansu kaburbura, to amma lokacin suna ’yan gyare-gyare a kaburburan saboda haka wannan bai yiwu ba. Suka ce zuwa Disamba za su kammala aikin insha Allahu. Shi ya sa daidai wannan lokacin sai muka sake dawowa. Ka ga dai wato manufar zuwanmu dai shi ne wannan ziyara din.

Sai dai kuma ’yan uwa sun yi amfani da damar sun shirya wata ‘Seminer,’ ta wani taron na daban na kara wa juna ilimi din har walayau. Don dai a yi amfani da damar a lokaci guda kan gina shakhsiyyar Dan uwa musulmi, wanda aka yi galiba da Ingilishi, saboda mutanen wannan sashe, shi ma dai a lokaci guda.

Saboda haka ka ga daidai wannan lokaci sai ya zama akwai rufe wannan taro da kuma wannan ziyara kenan na kaburburar wadannan Sarakunan da Turawa suka ciccire suka zo da su suka tara a nan Lokoja, kuma duka suka rasu a nan Lokoja aka rurrufe su a nan Lokoja din.

ALMIZAN: Gafarta Malam wani abu ne na musamman da wannan gari yake da shi da har aka kawo wannan ziyara baya ga wadannan kaburbura?

MALAM ZAKZAKY: Eh mana! Akwai batun cewa su Turawa sun zo ne suka tumbuke wani nizami namu suka kafa nasu. A daidai wannan lokacin, kamar wadancan da suka cire sune ragowar alamomin wancan nizamin da Bature ya tumbuke. Ka ga shi ya sa ma in ka lura shi nizamin yanzu bai kula da su ba.

Kamar yadda muka gani yanzu mun je mun ga kaburburan nasu, baya ga ’yan gyare-gyaren da ’yan uwa suka yi, wato sam ba a kula da su ba. Ka ga wato kenan ana nufin kamar an rufe babin tarihinsu kenan. Amma yanzu ka ga har suna kula da kaburburan Turawan mulkin-mallaka da suke nan. Har ma mun ji an ce gwamnatin jihar nan tana ware Naira miliyan 24 a kowace shekara don kula da su, alhali ba ta ware ko kwabo domin gyaran kaburburan su wadannan Sarakunan.

Ka ga abin da yake an fi kenan, wadancan rufaffen babi ne, wadannan budadden babi. To kuma tun lokacin da Bature ya ci kasar nan da yaki ya kafa abin da ya kafa, shi wannan abin da ya kafa shi ake a kai har yanzu, yau sama da shekara 100.

To mu ka ga yanzu zuwanmu da nuna wadannan mutane, ya nuna kamar abin da muke nufi shi ne za mu bude babin kenan, wannan wanda suka rufe.

ALMIZAN: Akramakallahu da yake duk Sarakunan kowanne ya zo daga wurare ne daban-daban ne. Ko Malam zai gaya mana ya aka yi suka zo da su nan?

MALAM ZAKZAKY: Duk dai Turawa suka kawo su a nan, shi ne abin da ya tara su gaba daya. Turawa suka same su suna sarautu a inda suke, da wadanda suka yake su, kamar mun ga akwai kabarin wani mai suna Muhammad Ibn Umarul Futy, wanda shi ba Sarki bane, amma ya fafata da Turawa, faransawa a kasar Mali. To shi ma sai suka kamo shi suka zo da shi cikin bangaren Borno a wancan lokacin. Daga nan kuma suka dauko shi suka kawo shi nan Lokoja. To shi ma ya zauna dai nan, haka ya zauna dai har Allah ya yi masa rasuwa.

To akwai kuma wasu sarakuna ne da suka cire su daga saurauta, kamar irin Sarkin zazzau, ko kuma a ce Sarakunan Zazzau biyu, Kwasau da Alu. Shi Alu su suka nada shi, amma sun cire shi, shi ma suka kawo shi nan. Sannan kuma akwai Sarkin Kano Alu wanda shi ma sun kama shi ne a yayin da shi ma ya yi fada da su, shi ma suka kawo shi nan. Sannan kuma akwai Sarkin Gwandu, Muhammad Aliyu da sauran dai wasu Sarakuna kamar yadda muka zazzagaya.

Wani abu guda da su shi ne, Sarakunan ba su tafi tare da Turawa bane, wato sun bata da Bature. Saboda haka Bature ya tattaro su ya zo ya zuba su a nan.

Kuma sune ya yi bikin nuna masu cewa karshen wannan nizamin da ya zo. Sune ya nuna masu Alkur’anin da yake iko a da yanzu ba shi bane, har ya masa abin da ya yi masa (na wulakanci). Sannan kuma a gabansu ya dauko tuta ta da mai La’ilaha illallah ya kona, ya daga tutar Ingila mai Kuros, mai sakandamin nan da ake ce ma ‘Union Jack,’ aka buga bajudala aka hura begiloli, shekara 101 da suka wuce. Ka ga wato kenan kamar yadda nake fadi, wannan ka ga an nuna kenan su an rufe babi da su.

ALMIZAN: Akramakallahu, wadannan kaburbura, sai ya zamanto ba Hukuma ce kadai ba ta kulawa da su ba, hatta al’umma ma sun yi watsi da su. Me Malam yake jin ya kawo haka?

MALAM ZAKZAKY: To na farko dai su na Hukuma da gangan ne, kamar yadda muke gani. Tun da yake mutumin da ya ware miliyan 24 ya ce don kula da kabari, ai ya san akwai wadansu kaburburan. Ta janibin Hukuma kenan. Muna iya cewa da gangan ne. Sai dai muna kokarin yanzu mu nuna masu cewa wannan kuskure ne. In ma sun ce ba da gangan bane sun manta ne, to muna tuna masu.

To amma janibin al’umma, muna iya cewa yau da kullum an mantar da su ne. Da yawa za ka sami yara su ba su san wannan labarin ba. Ko da ma sun sani, to ba su dauka mutanen ma akwai su ba. Ba su kuma kula da ina ne kabarin ba? Kodayake su ma ba ina wanke su al’umma bane. Inda ana tunatar da su yau da kullum, zai iya rayuwa a tare da su. Amma yau da kullum dai sun manta ne kawai.

Saboda haka ka ga wato kenan muna iya cewa kowanne dai yana da laifi. Kuma yanzu kusan aikinmu shi ne fadakar da kowanne, al’umma din da kuma Hukumomi din.

Ta janibin Hukumomi, kudaden nan da suke warewa don kula da kaburburan Turawa, to su ware wanda ya fi shi don kulawa da wadannan kaburbura din.

Su kuma ga janibin al’umma sai mu ce, musamman wadanda suke jinainan wadannan bayin Allah ne da suke kwance a nan, su kuma su yi yunkuri su yi wani abu. A kuma a fadakar da al’umma cewa wadannan wadansu gwaraza ne suke tara da ku.

Ko ba komai ko janibin Hukuma ba su damu da komai ba akwai bangare biyu da za su yi la’akari da su. Na daya tarihi, na biyu wannan lokaci ne da suka damu da abin da suke ce wa yawon bude ido, ‘Tourism’. To ka ga wannan wurare ne na bubbude idanu da kula da tarihi. Kuma ka san suna son kudaden shiga. To ka ga in ba ba su yin don Allah, ko don kudin shiga ma sa yi.

ALMIZAN: Akramakallahu, duk cikin wadannan kaburbura din Sarkin Bida ne kawai ya damu da kabarin Tsohon Sarkin Bida din har yake ba shi kulawa ta musamman. Malamn yana ganin wannan wani ci gaba ne?

MALAM ZAKZAKY: Eh to, yadda na lura kamar akwai dan bambanci tsakanin na Sarki Bida da sauran Sarakuna din. Domin shi kamar zuri’ar gidan sun zauna tare da kabarin, don a gidansu yake. In ka lura su suna zaune a wurin ne, a cikin gida muka same shi; gidan kuma, kodayake ba shi kadai yake a gida ba. Amma shi wannan su zuri’ar wannan mutumin ne suke zaune a wurin. To akwai wannan. Amma dai ko ba komai sanadiyyar fadakarwar da ALMIZAN ta yi bayan da wani ‘Task Force’ na su Malam Ibrahim Potiskum da suka zo suka zazzagaya suka ba da bayanan abin da suka gani, ya sa wasu sun yi tunanin su yi wani abu. Har shi ya sa suka yi wadannan ’yan gyare-gyaren. Wasu kuma mun ji sun yi yunkuri su yi, amma ba mu ga sun yi ba. To ala ayyi halin, abubuwan da muka gani yau, mu a ganinmu kamar an bar su a yashe, amma ba mu gan su ’yan watannin baya bane, da mun san me ake nufi da yasarwa. Wannan fa an gaggyara ne, ’yan uwa ne suka yi yunkuri suka gyaggyara wuraren. Don wadansu wuraren, juji ne, aka share jujin. Sannan wadansu wuraren kuma duk ramukan gafiyoyi ne, aka kakkawar. Wani wurin ma ba zai shigu ba, duk aka yi hanyar da har muka bi yau da mota muka shiga. Duk ’yan uwa suka yi wadannan.

Akwai ma kabarin da ba a san shi ba, ba a san ma waye ma’abocinsa ba, duk ’yan uwa da aka ba su misali, suka tona wani juji, sai suka ga alamar kabari, suka ce to shi ne din, sannan suka kewaye shi.

ALMIZAN: Da yake wannan abin ya kwana biyu, ta yaya Malam zai tuna al’umma yadda abin ya faru har kuma Turawa suka zabi Lokoja a matsayin wurin da za su ajiye wadannan sarakuna da suka tsige?

MALAM ZAKZAKY: Su dai kamar yadda na ce maka an tuttube su ne a Sarauta. Kuma kasantuwar an kawo su nan, dalili guda ne, nan ne Hedikwatar Bature a wancan lokacin. Kuma nan yake da rundunar soja da manya-manyan makamai. Saboda haka idan abin a kawo hari ne, to nan ne zai iya yaki kenan.

To kuma dalilin da ya sa nan ya zama masa Hedikwata saboda nan bakin ruwa ne, don yana zuwa ta jirgin ruwa ne. Lokacin shi ne muhimmin hanyar tafiya. In sun shigo ruwa a tekun Atlantika sai su su zo karshen kogin Neja, sai su biyo shi, sai ya zo har nan da isasshen ruwan da jirgin ruwa zai iya zuwa nan.

Bar ganin Neja yadda take yanzu, ta dan tsuke a bisa yadda take a da, tana dada tsukewa ne in dai ba yashe ta aka yi ba.

To a da can jiragen na zuwa har nan lafiya lau. Daga baya ne ya tashi hedikwata daga nan ya kai Zungeru, sannan Zariya, sannan Kaduna. Amma dalilin kawo su nan, saboda nan ne Hedikwata. Ka ji dalili kenan.

ALMIZAN: Ko wadannan ziyarori da wannan farfado da wadannan kaburbura da aka yi, wata alama ce ta cewa wancan babin da aka rufe za a bude shi kenan?

MALAM ZAKZAKY: Na riga na fadi wannan ai. Wato kamar abin da aka manta ne muke tunatar da al’umma. Abin da aka rufe ne muke kokarin budewa, ko ma in ce budau, an bude kawai insha Allahu.

ALMIZAN: Akwai masu ganin cewa Turawa sun kawo masu adalci ne sun tumbuke Sarakunan da ke zaluntar su sun kawo masu adalci. Ba mu san karin hasken da Malam zai yi wa al’umma a kan hakikanin abin da ke tafe da Turawa da kuma manufar zuwansu a nan ba?

MALAM ZAKZAKY: To ba za mu ce Bature zuwansa bai yi wani amfani ba sam-sam, ba za mu ce haka nan ba. Illa iyaka abin da muka sani shi ne (Bature) bai zo domin ya amfane mu ba, ko da zuwansa ya yi mana amfani. Shi ya zo ne don ya amfani kansa, ko da ya yi maka wani abu ka ga ka amfana da shi, to ba domin ka amfana ya yi ba. Alal misali, in ya koya maka karatu, ba don yana son ka iya ilimi bane, yana son ka iya yi masa aiki ne, shi ya amfana da kai.

Haka kuma in ka ga ya shimfida hanyar dogo na jirgi, ba don kai ka amfana da shi bane, domin ya dibi kaya ne, kodayake kana iya amfana da shi ka yi tafiya.

Saboda haka ba mu ce sam-sam abin da suka yi bai amfane mu ba sam-sam. Amma ba su yi domin ya amfane mu ba. Kuma su suka fi mu amfana. In muna da amafani da za ka yi masa mikidari, ka ce masa kashi guda, to su suna da kashi dari. In ka ga mun amfana kashi daya, to sun amfana sau kashi dari ta wata fuska da wannan abin da kai ka amfana da shi din. Ka ga ba domin ka suka yi ba kenan.

Kamar misalin mutum ya debi dallakin masana’antu din nan, guggubin masana’antu ya amfana da shi. Ba a fid da gaggubin masana’antu saboda fitarwa. Ana fid da muhimmin abu ne, amma sai ya samar da guggubi. Alal misali idan kafinta yana yanka katako yana zubar da wadansu barbashi don ya yi kujera, to barbashin na iya amfani ta wata fuska, ka ga ba yana yanka katakon ne don ya samar da barbashin ba.

Saboda haka duk wani amfanunukan da muka yi da mukin-mallaka ta wannan janibin ne. Wato ta janibin barbashin abin da ya riga ya cire, wanda ba ya bukata mu muka amfana da shi. To ka ga ba dominmu ya yi ba kenan. Saboda haka bai kamata mu yaba masa ba.

Idan mutum ya ci kwai ya yar da kwasfa, sai kwasfan ka tsinta ka dan lasa, ba sai ka yi ta gode masa ba, don shi ba ya bukatar wannan kwasfa, ya watsar ne. Saboda haka ainihin ma ka taimake shi ne, ba shi ne ya taimake ba, da ka raba shi da juji.

Sannan wannan janibin kenan na amfani wanda shi mutane suke gani. To janibin cuta kuma wanda suka zo musamman don su yi, shi kuma ya fi yawa, wanda yake su suna da nufin su tabbatar da cewa sun kawar da mu daga addininmu da suka same mu a kai, kuma sun iya wannan, saboda yanzu ba addininmu ke iko da mu ba, alhali da shi ne.

Na’am ana iya cewa Sarakuna kafin su iso, Sarakuna sun karkace daga kan hanya suna zalunci, mun yarda haka nan. Abin da Bature ya zo da shi ya fi wannan zaluncin da suke yi, saboda shi ya zo da kofirci ne. Ka ga gara zalunci da musulmi zai yi karkashin nizamin da ya yarda Musulunci ne. In ana son gyara shi, sai a kawar da mai zaluncin a zo da mai adalcin. Da a kawar da Musuluncin gaba daya a kawo kafirci, wanda shi ne Bature ya yi, wanda kuma shi ne mutane ba su lura da wannan ba.

Ka ga idan muka kwatanta da cewa na farko in mun amfana ba domin amfaninmu ya yi ba, shi ne ya fi mu amfana, in mun sami kashi daya, shi ya sami kashi dari.

Na biyu in muka lura ya kuma zo ya cuce mu. In muka tattara wadannan da amfaninsa ta bangare guda da cutar da mu ta wani bangare guda da dan guntun amfaninmu muka auna a mizani, za mu ga karshe abin gaba daya ya cuce mu ne. Saboda uwa-uba ya cuce mu ne ya maishe mu bayi, har yanzu kuma wannan nizamin haka yake, cewa yanzu dukiyar kasar nan ana diba ba ne su suna amfana da ita. Shi ya sa yanzu ga shi muna da kasa sunanta Nijeriya wadda tana daga cikin kasashe masu arziki a duniya, ana cewa ita ce kasa ta shida a cikin jerin kasashe masu arzikin mai a dunya. To sauran kas ashen, duk masu arzikin man fetur din nan idan ka je, sai ka ga tasirin man, za ka ga arzikin amma a nan babu. Nan ne kasa da take da arziki, amma mutanenta suna fama da talauci. Meye dalili? Wani wuri ake kai arzikin. Domin ba su kafa kasar nan domin amfaninmu ba. Sun yi domin amfanin kansu ne.

Su suke amfana da dukiyar, su dora mutanen da suke ba su kamaso; kamashon ma a diba a kai masu. To ya ka gani Malam? Don me kuwa ba za mu ce wannan ya ishe mu, muna so mu koma ga abin da muka gada iyaye da kakanni, nizamin Musuluncin da yake shi ne mu, shi ne jininmu, shi ne tsokar jikinmu, shi ne akidar da ke cikin zuciyarmu, shi ne daukakarmu, shi ne mutuncinmu?

ALMIZAN: Wannan zai haifar da kishin kasar da ake ta magana a kai?

MALAM ZAKZAKY: To ka ga shi ma yana daga cikin abin da nake cewa. Ka ga yana da wuyan gaske a sami kishin kasa a Nijeriya, ganin cewa abin da ya mayar da Nijeriya kasa shi ne mulkin-mallakan da Bature ya yi mata. To kuma shi kishi akan same shi ne sakamakon mutum yana alfahari da abin da yake a kai. Kamar in kasarku ne kana alfahari da kai dan kasar ne. To ita Nijeriya ba ta ba ka abin da za ka yi alfahari da ita ba. Domin duk wanda ya yi tinkaho da alfaharin cewa shi dan Nijeriya ne, to abin da yake cewa (shi ne) yana alfaharin shi bawa ne. Ka ga kuwa ba a alfahari da mummunan tushe irin wannan. Shi ya hana wa ’yan Nijeriya kishi. Ko ka ji mutum yana ta ihun kishin kasa, kishin kasa, duk na fatar baki ne.

Amma hakikanin kishin kasa ba zai taba yiwuwa ba a Nijeriya, saboda ita Nijeriya ba al’umma ce da su mutanen al’umma suka kafa ta ba. Wani ne ya kafa masu domin amfanin kansa, ba su suka kafa al’ummarsu domin amfanin kansu ba.

ALMIZAN: Kamar yadda Bature ya zo ya yi zalunci a wannan wuri, wane albishir Malam zai yi wa al’umma na daukar fansa?

MALAM ZAKZAKY: To shi dai zalunci ba ya dawwama. Akwai batun cewa shi wancan nizamin, wani nizami ne wanda a da yake iko, wani kuma ya zo ya hau, saboda haka shi ma wata rana zai kau. Ba wani lokacin da aka taba kafa wani abu ya dawwama. Saboda haka wannan nizami da muke a ciki na kangin bauta shekara dari da ’yan kai ba kuma zai dawwama ba. Wata rana Allah zai kawo karshensa.

ALMIZAN: Ko akwai kira da Malam yake da shi?

MALAM ZAKZAKY: Ba mu ki ba mun sami kanmu a wata kasa sunanta Nijeriya. Ba mu ki ba kuma dai ko bisa hadari ne dai mun zama kasa. To amma ba yana nufin wai shi kenan sai a tafi a haka nan ba. Ba yana nufin kenan dole sai yadda Bature ya kafa abu haka za a yi ta zama ba, muna iya canza alkiblar ita Nijeriya din domin ta amfane mu.

Abin da ya rage wa ’yan kasar nan shi ne su zauna su yi na zari su ce, da can dai wani ne ya zo ya kafa mu don amfanin kansa, to yanzu mu mu kafa kanmu domin amfanin kanmu. Da can muna da nizaminmu, wanda yake shi ne muka yi imani da shi, wani ya zo ya dankara mana abin da shi ya yi imani da shi, yanzu lokaci ya yi da za mu koma kan abin da mu muka yi imani da shi. In suka yi wannan, in ya so kasar ta tsaya sunanta Nijeriya. In ya so sunan ma ya zama Nijeriya din, duk babu damuwa, amma dai dole nizamin ya zama ba wanda makiyinmu ya kafa don amfanin kansa bane. Wanda mu muka kafa ne domin amfanin kanmu. Wannan shi ne kawai zai sa mu iya amfani da shi, shi zai iya zaburantar da mutane kuma har su yi kishi, har su yi yaki domin kare shi, shi ne kuma kawai zai fitar da mu daga kangin da muke ciki.

ALMIZAN: Allah gafarta Malam, mun gode:

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International