Almizan :Kwastam za su kona kayan Naira miliyan dubu 3 a Kano ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Kwastam za su kona kayan Naira miliyan dubu 3 a Kano

Daga Ali Kakaki (alikakaki2001@yahoo.com)

H

Yanzu haka shadda da leshi da kuma atamfofi na sama da Naira miliyan dubu uku ne Hukumar da ke kula da yadda ake shigo da kayayyaki da fitar da su a cikin kasar nan, ‘Nigerian Custom Services’ ke shirin kone su gaba daya.

Su dai wadannan kayayyaki Hukumar ta kwastam shiyyar Kano ce ta kama su, kuma take tsare da su a ma’ajiyarta da ke unguwar Sharada. babban jami’in Hukumar kwastom mai kula da shiyyar ta Kano, da yake zagayawa tare da manema labarai da kuma Shugaban Hukumar tattarawa Nijeriya kudin shiga, ‘Chairman Nigerian Tax Force,’ Malam Nasiru El-Rufa’i, sannan kuma Ministan babban birnin Tarayyar Abuja, ya nuna wa musu tarin tsubin kayan a wannan makeken sito. Wakilinmu ya shaida mana cewa diloli ne jibge iya ganin idanunka na shaddodi da leshi da kuma atamfofi.

Da yake zantawa da manema labarai, ciki har da ALMIZAN, jim kadan da kammala duba kamammun kayayyakin, El-Rufa’i cewa ya yi ya je Kano ne ziyarar gani da ido, haka kuma ya umurci jami’an Hukumar kwastom da su kona kayayyakin kamar yadda ya samu umarni daga Shugaban kasa, inda ya ce tuni har sun riga sun fara kona irin wadannan kayayyakin a shiyyar Abuja.

Sai dai kuma wani bincike da ALMIZAN ta gudanar, a sakamakon kama wadannan kayayyaki ’yan kasuwa da dama a Kanon Dabo da ma Arewacin kasar nan da ma kasar baki daya sun karye warwas.

Wasu da muka zanta da su, sun bayyana bacin rai da takaicinsu a kan yadda gwamnati take kona kayayyakin da ta kama, maimakon a yi gwanjonsu, ko kuma a raba wa mabukata da suke tsananin bukatar kayayyakin, amma talauci da fatara ta hana su samu.

Sai dai kuma Ministar kudi ta Nijeriya, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, ta shaida wa manema labarai a Abuja cewa, gwamnati tana kona wadannan kayayyakin da Hukumar kwastom take kamawa ne da nufin karya lagon masu fasa kwarin da ke shigo da kayayyaki ta barauniyar hanya. Tana mai cewa, yin hakan (shigo da kayayyakin) yana yi wa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa, da kuma yi wa ci gaban da ake fatan samu mahangurba.

Gobara ta kashe yara 4 a Bauci

Daga Mu’azu Hardawa

Gobara ta kone yara hudu kurmus har lahira a kauyen buzaye da ke kan hanyar bauci zuwa Jos, a sakamakon kwana da babur a daki da mahaifin yaran ke yi.

Malam Kasimu Abdu buzaye, dan acaba, wanda ya shafe fiye da shekara 20 yana sana’ar acaba shi ne mahaifin yaran da suka hada da Abubakar, 9, da Ishaka da Yakubu, ’yan shekara hudu-hudu, sai yayarsu mai shekara 12, wadanda suka kone kurmus cikin makon shekaranjiya da misalin karfe 9:00 na dare, kuma aka yi jana’izarsu a daren.

Yaran sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da tankin babur din mahaifin nasu ke zubar da man fetur bayan ya shigar da babur din cikin daki. A daidai wannan lokaci ne ya yi kokarin toshewa da sabulu, amma abin ya faskara, sai ya dauko jarka da tiyo ya fara janye man fetur din.

Lokacin da jarkar ta cika, sai ya yi kokarin jawo tiyon daga tanki, fitilar kwai kuma tana can nesa, sai man ya fantsama kanta, ta kama da wuta, babur shi ma ya kama da wuta. Kafin kiftawa da bismillah, shi kuma ya jawo babur don fito da shi, sai ya yi ranga-ranga a kofa, wuta ta kama, ta fantsama, yara na cikin daki suna barci.

Kafin a ceto su, daki ya kama, nan take yaran suka kone, aka yi suturarsu a daren, kamar yadda mahaifin yaran ya fada.

A wani labari makamancin wannan kuma, wani yaro ya rasa ransa a garin Hardawa da ke Karamar Hukumar Misau a lokacin da iyayensa mata suka tafi makarantar Islamiyya da dare suka bar shi cikin daki yana barci wuta ta kama.

Mahaifin yaron, Malam Mu’azu Sarkin Tike, wanda ma’aikaci ne a Karamar Hukumar Misau ya ce, Allah kadai Ya san musabbabin tashin gobarar wadda ta cinye sabon gidansa kurmus, tare da hasarar dukiya ta dubban daruruwan Naira.

Mazauna garin na Hardawa suka ce sun jima ba su ga ta’adin wuta cikin kankanin lokaci kamar na wannan gobara ba, wadda hatta ginin gidan sai da ya tsattsage.

Tuni dai Hukumar kashe gobara ta jihar bauci, karkashin jagorancin Alhaji Sabo Adamu Muhammad da kuma Manajan shiyya na Hukumar samar da hasken lantarki ta NEPA suka fara taron kara wa juna sani domin wayar da kan jama’a ta yadda za a kare kai daga shiga hadarin gobara, musamman a wannan lokaci na hunturu da ake samun matsalar tashin gobara a birane da kauyuka.

Sudais zai bude Cibiyar yada Musulunci a Damaturu

A tsakiyar shekara mai zuwa ne, ake sa ran Limamin masallacin Ka’aba da ke Saudiyya, Shaikh Sudais zai kaddamar da wata katafariyar Cibiyar yada addinin Musulunci ta duniya a Damaturu, hedikwatar jihar Yobe.

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji bukar Abba Ibrahim ne ya furta haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano.

Ya ce, Cibiyar ta kunshi wani masallaci wanda duk Afirka ta Yamma babu mai girmansa domin a cewarsa, masallacin zai dauki masallata a lokaci daya har mutum 8,000, yayin da harabar za ta dauki masallata kusan 100,000.

Alhaji bukar Abba ya ci gaba da cewa, Cibiyar ta kunshi babban dakin taro da kuma shaguna wadanda za su rika samar wa Cibiyar kudin shiga don amfanin yau da kullum.

“Wani abu da ya fi ba ni sha’awa shi ne babu taimako ko da na sisin kwabo da muke samu daga kasashen waje,” in ji Gwamnan.

Ya ce, gwamnatin Yobe da sauran gwamnatocin jihohi makwabta da kuma sauran jama’a masoya Allah ne suka tattara kudin da aka gina Cibiyar.

Gwamnan, wanda ya zo Kano domin halartar bikin rufe gasar karatun Alkur’ani na kasa karo na 20 da aka yi, ya ce, a halin da ake ciki yanzu a jihar ta Yobe, gwamnati ta bude makarantun Islamiyya na zamani a duk mazabar dan Majalisar Dattijai na jihar.

Ya ce, gwamnati ta yanke shawarar bude makarantun ne don koyar da ilimin zamani da kuma na addinin Musulunci don bunkasa addini a jihar.

Da yake amsa wata tambaya, Gwamnan ya ce, domin dorewar dimokuradiyya a kasar nan dole ne a rika yin karba-karba na shugabancin kasa a tsakanin Kudu da Arewa.

“Amma ni a fahimtata za a yi hakan ne na wani lokaci, idan dimokuradiyya ta zauna da gindinta, sai a bar tsarin ya rika fitar da Shugaban kasa ba tare da la’akari daga ina ya fito ba,” in ji bukar Abba.

Sabuwar dabarar sata ta bayyana

Daga Zakariyya Umar Sanda

A wata rana ne wasu matafiya da suka fito daga yankin Abuja suka fada a motar hayan ’yan damfarar nan da ake wa lakabi da ’yan 419 a wajen tashar shiga motoci ta Dan Kogi da ke Zuba ta yankin Karamar Hukumar Gwagwalada, Abuja.

Matafiyan da suka tsaya kan bakin hanya don samun saukin abin hawa sun kunshi daliban FCOE da ke Zuba, masu kai-komo wajen neman aiki a Abuja, ’yan kasuwa da sauran matafiya zuwa Lokoja da Okene. Suna ganin sun yi sa’a da nasarar tare wata mota kiran fijo mai daukar mutane 10, tare da ganin za a sami saukin kudin motar.

Kamar yadda daya daga cikin wadanda suka fada hannun ’yan damfarar ke shaida wa Wakilin gidan rediyon birnin Tarayya Abuja, bayan sun shirya da mai motar ne sun zuba kayansu da manyan akwatina sun kama hanya, sai direban ya tsaya kamar zai dan duba wani abu a jikin motar, ko da matsala. “Muna cikin tafiya mun wuce Tungan Maja kawai sai direban ya tsaya ya dan dudduba tayoyin motar, can sai yana tsaki ya bude bonet din motar yana ’yan tabe-tabensa, sai muka sauka. Masu zuwa fitsari sun je suna yi, masu neman gindin inuwa sun je sun zazzauna muna jiran tsammani. bayan mun gama hada masa kudin motar kawai yana kulle bonet din motar sai ya ta da ita ya tsare.”

Mutumin ya ci gaba da shaida wa Wakilin gidan rediyon Abuja din cewa, “haka kawai muka tsaya muna kallon ikon Allah, muna ta ihu, amma direban don rashin imani ya tsere mana da kaya tare da jakunkuna cikin sauki.”

Daga karshe matafiyan da suka fada wannan sabuwar dabarar satar sun yi kiyasin kayan da ke cikin jakukunansu, tare da wayar tafi-da-gidanka (hand set) guda shida, wadanda suka yi jimillar kayan sun kai kimanin kudi Naira dubu 300, banda kwalayen shaidar kammala makarantu da wasu takardunsu na daban masu muhimmanci ga matafiyan.

A wani labarin makamancin wannan kuma, a dai wannan garin na Zuba ne, wasu mutane suka yi wa wani dan uwa mazaunin Kaduna, Malam Abubakar fashi mai kama da zamba cikin aminci.

Kamar yadda Malam Abubakar ya shaida mana, bayan sun yi nufin tare mota da wani mutum da shirin zuwa Kaduna, sai direban da ya yi alkwarin kai su ya waske da su ya kai su wani gida, inda kiri-kiri aka kwace masa kudadensa har Naira dubu 50.

Sai dai kuma bayan wata gajeruwar fafatawa da arangama da aka yi tsakanin mafasan da kuma ’yan uwan wannan gari na Zuba, Allah ya fitowa da Malam Abubakar kudadensa ba tare da ko sisin kwabo ya yi ciwon kai ba.

Wani da muka zanta da shi a wannan garin na Zuba ya ce, Hukumomin ’yan sanda suna sane da zaman gungun wadannan mutane da suke cutar da jama’a ba tare da sun taka masu burki ba, “saboda idan sun samo su ma suna ba su nasu kason,” in ji shi.

Da aka tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda na wannan yankin, kira ya yi ga al’umma da su san irin motocin da za su rinka shiga.

’Yan fashi sun farmaki wani banki da ke Abuja

’Yan sanda uku tare da wani dan fashi ne aka tabbtar sun rasa ransu, yayin da wasu gungun ’yan fashi da makami suka kai wani hari da rana tsaka cikin wata mota kirar Toyota Carina a harabar bankin ‘STANDARD CHARTERED bANK’ reshen Wuse a birnin Tarayyar Nijeriya Abuja.

Rahoton jaridar DAILY TRUST da ake bugawa da harshen Turanci, ya bayyana cewa an kai harin ne da misalin karfe 2:00 na rana, kuma ’yan fashin suna cikin kayan ’yan sandan mobayil ne, sanye da riguna masu kare su daga harbin harsashi.

Wani wanda ya gane wa idanunsa abin da ya faru, ya tabbatar da cewa, motar Toyota Carina mai lamba bZ 570 AbC da ke dauke da ’yan fashin hade da wata yarinya da ba ta wuce kamar shekaru 20 ba sune suka fara zuwa bankin, sannan daga baya sauran suka je suka hade da su.

Mutumin, wanda yake mai gadin bankin ne, kuma ya nemi da a boye sunansa, ya kara da cewa, da farko dai su ’yan fashin tunda yake suna cikin kayan ’yan sanda ne an zaci sun rako wani ne mai neman ya fitar da kudi masu yawa kamar yadda aka saba a al’adan bankin, amma daga baya sai ta bayyana cewa ’yan fashi ne.

Labarin ya nuna cewa ’yan fashin sun kashe wani maigadin bankin da kuma wani farin kaya da ba a san ko waye ba da ya zo bankin.

Sannan kuma wani dan sanda da ke aiki a bankin ya yi kokarin fafarar ’yan fashin ta hanyar bude musu wuta, amma ’yan fashin suka harbe shi a hannu.

’Yan fashin da suka fito daga bankin cikin motarsu Tayota, sun ci karo da wata motar a kan titi yayin da suke kokarin tserewa, abin da ya jawo suka kwace wata mota suka tare titi da bindigoginsu har suka sake wa kudin da suka sato mazauni daga motarsu zuwa motar da suka kwata.

Ganau sun ba da labarin cewa an ga ’yan fashin sun dauko dayansu da shi ma aka kashe a ba-ta-kashin da suka yi da wancan dan sanda daga motarsu sun sa a sabuwar motar da suka kwata. Daga nan suka arce a guje.

’Yan fashin dai sun tsere ba tare da ’yan sanda sun ci nasarar kame su ba. Kuma ko nawa suka sata? Allahu a’alamu.

Fashi dai yanzu ya zama kamar wani abu da aka saba da shi a Nijeriya kan hanyoyi ko bankuna, ko kuma ma cikin gidan jama’a, da dare, ko kuma da rana tsaka.

Da yawa na ganin irin bambancin da ke akwai tsakanin talaka da masu hannu da shuni, a bangare guda da kuma irin halin matsatsi da jama’a ke ciki sune ke sa yawan wannan mummunan aiki na fashi da makami da ya gagarin hukumomin tsaron Nijeriya.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International