Almizan :Ba wata fitina tsakani na da Mataimakina ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tattaunawa

Ba wata fitina tsakani na da Mataimakina

In ji Malam Ibrahim Shekarau

Mai karatu, ga ci gaban hirar da Editocin wasu manyan jaridun Arewa – Weekly Trust, Almizan da Leadership – suka yi da Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, wanda kuma aka watsa shi kai tsaye ta gidajen rediyo da talabijin na jihar a kwanakin baya. A sha karatu lafiya.

Shaikh Hasan Saffar

EDITOCI: Da ka dawo daga hutu an ji kana yabon Mataimakinka, sai mutane suka yi ta mamaki, musamman yadda wasu ke ganin akwai rashin jituwa tsakaninku. An warware duk wata rashin jituwar da take tsakaninku ne, ko ko maganar ba daidai bane?

GWAMNA SHEKARAU: Gaskiyar magana babu zancen wata fitina. Abin da kullum nake fada shi ne ba za ka hana mutane jita-jita ba. Akwai wadanda su ribarsu ita ce a yi wannan jita-jita ta karya, a yi ta raba kan mutane. Ni, ko Mataimakin Gwamna babu wanda ya taba jin mun fito mun ce muna rigima. babu wanda taba jin ko ni ko shi wani ya fito ya ce wani yana tauye wa wani hakkinsa cikinmu.

Da zan tafi na ce masa ga gwamnati nan, ga Jama’ar Kano. Kai ne yanzun da riko kar ka waiwaye ni da komai. bai wuce in ya yi waya mu gaisa ba. Sai dai ya ban labari, amma ba wai zancen neman izini ko wani abu ba. Ya rike har na dawo. Ko da na dawo ban ji wani labari na laifi ba. Shi ya sa ma na ce jama’a su taya ni yi masa godiya.

EDITOCI: Sanin kowa ne cewa akan samu matsala tsakanin Gwamna da Mataimakinsa ko Shugaban kasa da Mataimakinsa, kai a taka fahimtar me kake ganin yake jawo haka?

GWAMNA SHEKARAU: Kodayake ba zan ari bakin sauran Gwamnoni in ci musu albasa ba, amma ga wanda ya yi aiki na rayuwa da mutane, ba wani bambanci tsakanin Gwamna da Mataimakinsa ko Shugaban kasa da Mataimakinsa, ko Ciyaman da Mataimakinsa da sauransu. Duk ya danganci yaya suke mu’amala da juna. Duk su biyun sai an samu amana da yarda a tsakaninsu. Idan aka samu wani gibi saboda wani yana ganin an tauye masa hakkinsa, to dole sai an samu matsala. Amma in aka sa hakuri da fahimta, sai ka ga an zauna lafiya an rabu lafiya.

Kuma babban jigon abin, ni ga fahimtata a siyasance, wanda kuma ya kamata ’yan uwana ’yan siyasa su yi la’akari da wannan, shi ne, mafi yawan abin da ke faruwa inda aka ce an tsai da Shugaban kasa ko Gwamna ko Ciyaman takara, to a siyasance sai a samu wasu su ce mune za mu ba ka Mataimaki. Yawancin Shugabannin ba su suke zaben wanda zai rufa masu baya ba. To yawanci sai ka ga an yi abin saboda ana so a saka wa mutum don a kwantar da hankalin magoya baya. ba fahimta ce tsakanin shi Shugaban kasa ko Gwamna ko Ciyaman da Mataimakinsa ta sa ya ce ga wane can fahimtarmu daya, ya san inda za ni, na san inda za shi, fahimtarmu daya, zo ka raka ni mu tafi ba. Amma duk lokacin da aka samu irin wannan, to ba za a taba samun fitina ba.

EDITOCI: Akwai lokacin da aka ce an samu sabani tsakanin ka da wasu ’yan jam’iyyarku ta ANPP a nan Kano kan batun goyon bayan kowannenku ga dan takaranku na Shugaban kasa, Janar bahari, shin an sasanta an zama daya ne, ko ya abin yake?

GWAMNA SHEKARAU: Zan sake komawa baya, jita-jita ce. Shi mai son ya bata, duk iyawarka sai ya yi kokarin ya bata din. Kamar irin labarin da Marigayi Aminu Kano ya taba bayarwa na dan Akuya da kura ta ce za ta cinye shi. To irin wannan shi ake mana. An yi rantsuwa an ce muna fada da bahari, an ce mun guje shi. buharin nan ya fada da bakinsa, ya gaya wa duniya, ya fada wa ’yan jarida ya ce ba wata rigima da ni, amma wasu sun ce atafau da rigima! To ya za ka yi da su? Wallahi babu wata rigima. Har gobe kuma, maimakon ni in fada, an tambaye shi, ya ce babu. To me ake nema kuma in ce? Akwai wasu sun makalkale cewa ana rigima da su ne, ko kuma a ce a’a muna rigima da buhari Organazation. To su waye buhari Organazation din? Misali in ka dauki wani dan buhari Organazation ba wanda zai ce ma ana wata rigima da gwamnatin Kano ko Ibrahim Shekarau; karewa ma ofishinmu na kamfe daya da na buhari Organization a nan Kano. Kuma ina so in tabbatar maka a cikin Jam’iyyar ANPP babu wata rigima. A ciki ba wanda ake rigima da shi. Dauki-ba-dadin da ake ta yi ta masu neman mukami ne na ’yan takara. Kuma wannan wani abu ne wanda yake sababbe; duk sad da aka ce za a yi zabe ko ga wata kujera kai kana so, shi yana so, kowa ya fita talla, magoya bayanka kokari suke yi naka ya samu, nawa kar ya samu. Su suke zuwa su dinga rigima a tsakankaninsu, kai ba ka sani ba, shi bai sani ba. Amma sai a dinga cewa ai wane da wane rigima ake yi. To amma alhamdulillahi duk ta yi kai, duk wani matakan da aka dauka na sasanta rigingimun takaran da waye, komai ya zama tarihi. Fatanmu Jam’iyya ta zama a dunkule uwa daya uba daya.

EDITOCI: Ko me Malam zai ce dangane da takaddamar filin da ke Kofar Na’isa? Shin na gwamnatin Tarayya ne kamar yadda wasu ke da’awa ko kuwa na gwamnatin jiha ne a yanzu?

GWAMNA SHEKARAU: Gaskiyar wannan magana dai a halin da ake ciki yanzu, wannan fili na Gwamnatin jihar Kano ne. Kuma ko ba komai ma a doka ta ‘Land Use Decree’, dokar da ta ba da izinin mallakar filaye, duk filayen da ke Kano suna hannun Gwamnan wannan jihar. Saboda haka duk wani wanda aka ba, aro aka ba shi. In aka tashi karba za a kawo dalili, kuma dalilin ya shafi al’umma, sai a karba. In aka ba ka fili ko ka yi gini, sai Hukuma ta ga ya kamata a yi makarantar firamare, sai a biya ka don filin kawai ake so. Abin da ba a yarda da shi ba shi ne in kwace wa Malam Ibrahim (Editan Almizan) in bai wa Sheme (Editan Leadership) babu hujja, misali.

Shi wannan fili da ake batu kafin mu aiwatar da wani abu sai an yi masa tsari, za a fid da fuloti-fuloti, a yi tituna, a yi lambatu, a sa fayif-fayif na ruwa, yadda in an ba ka aka ce ka yi gida, kana gamawa sai dai ka ja ruwa da wuta. Ita kanta kasar wurin mun ba da aikin auna ta don a gano irin ginin da ya dace a yi a wurin. Amma a dunkule wannan fili na gwamnatin jiha ne, ta bai wa Hukumar sufurin jiragen sama (Aviation). Su suka rubuto mana cewa ba su da bukata ga kayanku nan.

EDITOCI: Shin ko gwamnatinka na da wani shiri na musamman na rage ratar da ke akwai ta fannin ilimin boko tsakanin kudu da Arewa?

GWAMNA SHEKARAU: To, alhamdullahi gaskiya akwai. Kamar yadda ka fada a kididdiga a kasar nan jihohinmu na nan Arewa sune koma baya a rashin aikin yi, rashin ilimi na zamani, wato makarantun boko - firamare, sakandare, Jami’a, da sauransu. Wannan duk gaskiya ne. Duk da dai gaskiya abin ba za mu iya cewa laifin Shugabanninmu na baya bane. In dai za ka kwatanta mu da kudu ne, to shi ya sa muke cewa kar mu tsaya kawai kan kididdigan karatun boko. Mun ba da muhimmanci kan karatun Islamiyya da makarantun Kur’ani. Domin idan kana maganar ilimi dungurungum, akwai wanda bai taba zuwa ajin karatun boko ba, amma zai rubuta ma takarda da ajami. A zuwa kasashen waje da na yi Libya an kai mu wani wajen aje kayan tarihi, aka nuna mana wata wasika da wani dan kasuwan Kano ya rubuta shekaru 700 da suka wuce. Wato wani dan kasuwa ne daga Libya ya zo fatauci Kano, sai ya rasu. Sai wannan dan kasuwa na Kano ya dauki alkalaminsa ya rubuta wasika da ajami cewa wani daga kasa kaza mai suna kaza ya zo da kaya kaza, amma ya rasu. Ga kayansa kaza da kaza. Ya hada wannan wasika da kayan ya ba fatake suka maida wa masu su. Kuma Farfesa babs Fafunwa ya rubuta a littafinsa mai suna Tarihin ilimi a Nijeriya cewa, da a ce Turawan mulki sun kyale musulmin Arewa a kan tsarin ilimin da aka tarar da su a kai sun tafi kafada da kafada da na Turancin da ya zo, da an sha mamaki, da yau Allah kadai ya san irin matsayin da ilimi ya kai. A shekaru biyun nan muna ta kididdiga, yanzu haka mun gano cewa a jihar Kano muna da tsangaya, ba makarantar je-ka-ka-dawo ba sama da dubu 25. Mun san da zamansu, yawan daliban, yawan Malaman da inda suke da sauransu. Za mu dinga tallafa musu don a dago darajar makarantun da na Malaman. So muke nan gaba in za ka yi lissafin masu ilimi a Kano da yaran da ke zuwa makaranta, to a lissafa da yaran da suke zuwa tsangaya. Yanzu kuwa sai a ce yara kaza ne suke zuwa makaranta, alhali ana nufin na boko ne, a yayin da kashi casa’in na yaran suna zuwa tsangaya ne.

Abu na biyu da muke kokari a kai shi ne sama wa jama’armu aikin yi. Ni ma na gani a wata jarida cewa wata kungiyar kididdiga aka ce ta yi bincike ta gano cewa Kano ita ce ta fi yawan mutane marasa aikin yi. A gaskiya ba mu da cikakken bayanin mai suka dogara da shi har aka yi binciken. Abin da dai muke cewa shi ne ko gaskiya ne ko ba gaskiya bane, wannan na nuna cewa akwai wata illa tana nan. Kuma mun tasar wa abin ta hanyar sama wa matasanmu sana’a. Duk da mun dauki sama da mutun dubu talatin aiki, amma mun san wannan cikin cokali ne cikin wadanda suke bukatar abin yi. Kuma ba zai yiwu gwamnati a ce ta dau kowa aiki ba. Muna ta dai kokarin dawo da masana’antunmu don a samu aikin yi. Kuma da yake masana’antun sun dogara da samun isasshen wutan lantarki, to mun riga mun shiga yarjejeniya na samar da wutar lantarki mai yawan 600 Megawatt, alhali Kano in ta samu 300 Megawatt ma, za ta wadatu. Wannan zai taimaka in kamfanoni sun tashi, sababbi sun samu, aikin yi zai samu. In ana da aikin yi, talauci zai ragu.

Aikin noma kuwa, da ma mun dukufa a kansa, duk da shi ma aiki ne da zai dau shekaru. Amma duk wanda ya bi diddigi, yana mu’amala da masu aikin gona a cikin shekaru biyun nan, ya san mun yi hobbasa. A takaice dai muna daukar matakai wajen ganin mun fid da al’ummarmu daga wannan talauci da rashin aikin yi da kuma jahilci.

Sai mun hadu a mako na gaba insha Allah, za mu ci gaba.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International