Almizan :Hanyoyin da Harka Islamiyya za ta sami kudi ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Hanyoyin da Harka Islamiyya za ta sami kudi

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Mai karatu yau muna dauke ne da wani jawabi wanda Malam Ibraheem Zakzaky ya gabatar a karshen taron kwana biyu da ‘Resource Forum’ na wannan Harka Islamiyya suka gabatar a dakin taro na Fudiyya Islamic Centre, Zariya a kwanakin baya. Kamar kullum, Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga Kaset. A sha karatu lafiya.

GAbATARWA

Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’ala wabarakatuh. In na fahimci makasudin taron nan, daga ’yan jawaban da aka gabatar, ya nuna kamar wannan taron ya yi kama da irin taron nan da ake ce wa ‘Seminar’ kenan. Wanda yake manufarsa shi ne a tattauna dangane da hanyoyin da ya kamata a bi wajen habaka tattalin arziki. Amma dai nan kalmar tattalin arziki, ban ga kalmar ta dace bane, kodayake ban san abin da ya kamata ni ma in ce ba.

Mu a wurinmu in muka ce tattalin arziki, gaskiya muna magane dangane da al’umma ne. ba mu ce mutum ya bunkasa tattalin arzikinsa, ko wata kungiya. Muna magana dangane da al’umma ne a kan kanta; shi ne ‘Economy’ kenan. Al’umma take da ‘Economy.’ Kamar ‘Polity’ ne. Na’am Kamfanonika na cikin abubuwan da ke kawo dukiyoyi. Da ma ka ce mani hanyoyin da za a bi a sami kudi ne, da ma ya fi ma’ana, amma ba habaka tattalin arziki ba. Kawai hanyoyin da za mu samu kudi, sassaukar kalma. Amma tattalin arziki, lallai a bar ma al’umma. Kalma ce ta al’umma.

Wannan yana daga cikin abubuwan da har ‘aman’ da suka yi karatu sukan kasa gane ma’anar fannin nan da ake ce wa ‘Economics.’ Sun dauka kamar mutum in ya karanta yana iya sanin dibarorin zai kashe kudi ne ko ya sami kudi. ba su gane cewa kamar yadda ‘Political Science’ yake, haka shi ma yake ba. Shi ma yana nazarin yadda al’umma take gudanar da harkokinta na yau da kullum ne, wanda ya shafi nizamin tattalin arzikinta kamar yadda nizamin siyasarta yake. A bisa gaskiya ma sunan ilimin da farko, ‘Political Economy’ ake ce masa, daga baya ne aka canza masa suna zuwa ‘Economics.’

To, wannan wani abu ne wanda yake shi nizamin tattalin arziki na kasa (Wannan ina amfani da kalmar a yadda ta dace ne), nizamin ‘Economy’ na kasa shi ne ya shafe mu. Shi ne ya sa kuma muke fama da wahaloli. Saboda da a ce sauran ‘Economics da ka sani na duniya ne, to da wuyan gaske ma wannan ya zama mun tsaya muna tunani. Abin da ya kamata mu tsaya muna tunani shi ne kawai yadda za mu bunkasa ayyukanmu wanda yake muka sa ma gaba, la’alla na yada ilimi ne ko na ayyukan jin kai ne na taimakon mutane, musamman dai ma yada fikira. Da sai ya zama kawai mu abin da ya dame mu kenan. ba mu tunanin ta ina za a samo kudaden da za a gudanar da wadannan ayyukan din. Saboda za mu yi tunanin cewa mu namu aiki ne wanda ya shafi harkar addini, su kuma al’umma, aikin al’ummar ne ita kuma ta dauki dawainiyar yin wannan aiki din.

Alal misali duk lokacin da ake bukatar wadansu kudade don gudanar da wadansu abubuwa na yau da kullum, to su masu ra’ayi irin na harka din, to sune za su samar da wadannan kudaden. A wadansu wurare kusan haka nan ne. Wasu, ba ma ma’abotan harka din ba, al’ummar kanta, har da ma irin masu tausayawa din nan, za ka ga su suke ba da gudummawoyi masu yawan gaske ta yadda abin da ya dame su kawai dabarbarin yadda za su yada nasu ra’ayoyin. Alal misali kamar irin kungiyoyin nan da suke cewa masu kare hakkin bil’adama misali, za ka wadansu na da karfin gaske, amma kuma lallai ba suna magana dangane da ina za su sami kudi bane, amma suna samun kudade din daga kungiyoyi da daidaikun mutane da wadansu Hukumomi ma na wajen gudanar da ayyukansu. To mu ma haka din da a ce kamar misali ‘Economy’ din nan yana nan kamar yadda yake a saba’inoni ya mike a haka nan, to da ainihin zai zama sam ba tunaninmu ya za mu yi mu sami kudi bane. Ayyukan da za mu yi kawai muke tunani. ‘Projects,’ mu tsattsara yadda za a yi, sai kawai kudade su fito ta hannun su mutane don suna samun ‘income.’ Daga ‘income’ dinsu za su yanke wani abu su rika bayarwa, saboda mutane, wasu ma’aikata ne, wasu ’yan kasuwa ne, wasu manoma ne, wasu suna wadansu sana’o’i daban-daban. To sune kuma za su ba da kudade din.

Amma yanzun sai ya zama ma’aikata ba su samun komai. Yanzun albashi a kasar nan ya zama ba shi da ma’ana. ba inda ma albashi ya zama ba shi da ma’ana, kila ma a duk duniya in banda nan. Da can abin da aka sani albashi shi ne ma’aikaci ya dogara da shi. Shi ne hanyar samun kudinsa, a dinga biyan sa wata-wata. Kuma in ya yi aiki kamar na kimanin shekara talatin ya yi ritaya, za ka ga an ba shi wani dimbin kudi na ‘gratuity,’ sannan an yanka masa fansho. A daidai wannan lokacin yau da kullum ya iya biyan bukatunsa na duk shekarun nan talatin da yake aiki, abubuwan da yake yi na rayuwarsa da na iyalinsa (bai fasa ba). Kuma a yayin da ya daina aikin ma akalla yana da gida, yana da abin hawa, yana da wani dan jari ma kila da ya zuba a wani wuri, wanda zai mike masa har zuwa karewar rayuwarsa, in ma ya yi tsawon rai.

Amma yanzun a nan ba haka bane. Yanzun albashin da yake a rubuce, ainihin ba zai isa mutum cefane na mako guda ba, kyakkyawan mako. Kai ma in abin ya yi bushasha ne ma, kamar ya yi wani irin tuwon Salla na a zo a gani, to albashin ma dai shi kenan sai labari, ya riga ya tafi. To sai ya zama yanzun su ma’aikata ba za su iya ba da gudummawa ta wannan janibin ba kenan. Ka ga an fid da su, alhali kuma a kowane ‘economy’ su ma’aikata sune kamar kashin bayan abin da ake ce ma ‘comsumption.’ In sun karbi kudadensu su suke zuwa kasuwa, saboda haka kasuwa ta dogara da su ne. In za ka lura ma ’yan kasuwan nan irin ’yan kananan ‘traders’ din nan su ma kamar suna karbar albashi ne. Su ma sukan ce maka ka saurara sai karshen wata. Saboda sun san karshen wata za a ba ma’aikata kudi, su kuma za su zo su yi siyayya. Su kuma lokacin ne suke samun nasu. Kuma bilhasali ma su ma sukan ba ma’aikata ’yan basussuka na wadansu abubuwan yau da kullum na masarufi, in wata ya yi su biya su. Saboda haka su ma kamar suna samun albashi din ne. Duk karshen wata kowanne zai san cewa wata ya zo karshe, sawa’un yana sai da kwai ne ko kaji ko shinkafa ko tufafi ko tela ko sauransu lallai ya san dai wata ya cika.

To amma yanzun sai ya zama su wannan janibin an kawar. Saboda haka ba wata gudummawar da za su bayar. Ta nan kuma ka ga wato kenan, wannan shi zai sa sauran bangarori su ba da nasu gudummawowin, kamar ’yan kasuwa alal misali. Sai ya zama su ma kukan ake ta yi. Yanzu ba inda kudi yake sai a wurin mai mukami na siyasa, zababben mukami, su suke da kudade a hannunsu, kuma sun dauka kudin kayansu ne, saboda haka su suke debe kashi 90 su yi abubuwan da suka yi, sauran kuma kashi 10 a raba wa ragowa tsakanin albashi da sauransu. Duk sauran ragowar nasu ne. Yanzu in ba ainihin zababben ‘office’ ba, wanda yake kuma in wannan ne, ka ga wato kenan ba za mu taba tsammanin harka Islamiyya (za ta samu rabo ba). Inda a ce akwai wani mai zababben ‘office,’ kuma ya zo ya ce shi ma dan harka din ne, za mu ce gaskiya ya sauka lafiya kawai. Ya ce zai debo kashi 90 ya kawo mana na dukiya, za mu ce a’a don ainihin irin su daman muke so mu rusa. Ka ga ba zai yiwu ya zama mun dogara da su ba. Kafin nan ka ga yanzun kugiyar siyasa ita za ta iya tafiya lafiya lau, saboda ita daman kulob din wadannan mutanen ne. Yanzun sune kawai suke da kudi a kasar nan, masu zababbun mukamai. banda wadannan ma’aikata ba su da kudi, ’yan kasuwa ma ba su da kudi, ballantana masu kananan sana’o’i. To wannan shi ne ya shafe mu. Duk lokacin da muka shirya wani abu, sai ya zama sam ba zai iya yiwuwa ba. To, amma dai daidai gwargwado tunda akwai ‘’yan bizines da suke ta dan ‘managing’, ana dan yi dai ana bubbugawa, kuma wasu sukan mike, akan dan ci riba; komai lalacewa akwai wasu abubuwa dai da dole mutane sun dogara da su a rayuwarsu, kuma suna yi yau da kullum. Kodayake in an samu abin da aka dogara da shi, sai ka ga har su ma masu zababben mukamin ma sun shiga ana yi da su, kamar sayar da mai. Sai da ta kai tun daga Janar har zuwa mara igiya, kowa yana sai da mai ne.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International