Almizan : A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693 ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693

OBASANJO ALLAH YA SO MU

Kudin talakawan Nijeriya da ’yan kwallon kafa na Super Eagles za su tafi su kashe a Jamus ba tare da yin abin kirki ba, to sai ga shi Allah ya sa ba za su je ba. To sai a fito mana da su a saya mana magungunan a asibitocinmu da takin zamani, da kuma fatan Allah ya yi ta maimaita mana haka daga nan har zuwa illah masha Allahu.

Daga 0802 310 4109

ALMIZAN ALLAH SAKA DA ALHAIRI

Assalamu alaikum. ALMIZAN Allah ya saka da alhairi, domin yanzu kowane mako muna samun ALMIZAN a Yola.

Daga Abubakar A.M.B Yola 0802 672 1893

DANGOTE KA ZIYARCI DANGOTE CEMENT

Assalamu alaikum. Alhaji Aliko Dangote ya kamata ka ziyarci ‘Dangote Cement’ da ke NPA na Fatakwal, idonka ya nuna maka irin cuwa-cuwar da ake yi.

Daga Muhammad Bello Maiduniya Lafiya 0806 245 0055

RANAR TALAUCI A DUNIYA

Ranar 17/10/2005, za mu iya kiran ta da sunan ranar PDP, don Majalisar danne talakawan duniya ta kira ta da ranar abinci ta duniya. Amma a Nijeriya PDP ce ta talauta mu, don ita ce ta saka mu cikin talaucin da ba mu taba gani ba. Saboda haka daga yau har zuwa karshen mulkin PDP a duk lokacin da wannan rana ta zagayo, za mu kira ta da ranar PDP ta duniya, don ita ce ta saka mu a talaucin da muke ciki.

Daga 0802 310 4109

KOBON WUSHISHI KA YI RAWAR GANI, AMMA…..

Assalamu alaikum. Kobon Wushishi ka yi rawar gani da ka gayyaci Shaikh Dahiru Bauci don bude masallacin da ka gina a gidanka fisabilillahi, haka ake so masu kudi su rinka yi. To sai dai ina kira gare ka da ka rinka tausaya wa talakawa masu haya a gidajenka. Ta haka ma za ka zama mai taimakon jama’a na gaskiya.

Daga Muhammad Ali Kademi, Kaduna. 0804 494 2398

TAKEN TAFSIRIN BANA

Taken tafsirin bana; “raba kan musulmi.” Allah wadaran naka ya lalace.

Daga Ummar Abbas Buhari No.18 Gidan Dogo, Unguwar Bishar, Zariya. 0803 587 6715

IZALA ADDINI CE?

Assalamu alaikum. Zuwa ga ma’aikatan ALMIZAN, ra’ayi na shi ne, kai mai cewa Izala ce jirgin tsira, to Izala addini ce? Ka yi addini shi ya fi maka.

Daga Sabo Laji, Bididan. 0803 364 8598

MALAMAI A YI KOYI DA MALAM ZAKZAKY

Assalamu alaikum. Ina so in yi kira ga Malaman Izala da Darika masu tafsiri cewa su yi koyi da Shaikh Ibraheem Zakzaky a wajen tafsirinsu. A rinka karanta aya ana fassarawa, tare da yin bayanai masu amfani ba tare da batanci ga wani musulmi ba. Su kuma ’yan Shabbabu masu neman fada da musulmi, su sani yanzu zamani ne na fada da kafirci ba Musulunci ba.

Daga Musa Aminu Kurerya.

SAKONA GA MALAMAN NIJERIYA

Sakona ga Malaman Nijeriya shi ne cewa ba batanci ga Shi’a ne sauke nauyin da ke kanku ba. Ku yi wa gwamnati wa’azi ta wadata al’umma da abinci, ruwan sha da sauransu.

Daga 0802 469 3262

MUTUWAR STELLA OBASANJO

Ta rasu a Spain wai ta je kwaskwarimar jikinta. Dole ta je kwaskwarima mana tunda suna danne dukiyar talakawa.

Daga Bala Ahmad Mariri Lere LG 0803 601 5040

RIBADO KA KAWO ZIYAR GOMBE

Nuhu Rabado ya kamata ka kawo ziyara a jihar Gombe don a bai wa talakawa hakkinsu. Kwangilolin wuru-wuru da ake yi na jawo koma baya a jihar baki daya.

Daga Musa Dadin Kowa Gombe 0802 574 3265

YAZIDU YA KA SA GAMAWA DA SHI’A

Haba Babayo Musa ina son ka sani cewa zancen Izalatul Shi’a, su Yazidu ma sun yi ba su yi nasara ba.

Daga Murtala Salihu Kano 0802 692 5682

LA’ILAHA ILLALLAH AKA SA BA SHI’A BA

Ya kamata Malam Babayo Musa ya gane cewa Hakeem Raji fa, La’ilaha illallah ya ce, ba wai Sha’a ba a jikin jirgin tsiran da ya yi, kuma ita muke so Allah ya tabbatar da mu a kanta ba wata kungiya, ko wata mazahaba ba.

Daga Yusuf Ibn Musa Markaz Bauci Motar Park Jos 0803 593 6498

A JIRGIN SAMA MA BA A TSIRA BA!

To masu gudun shiga mota suna hawa jirgin sama saboda munin hanyoyi, ko gudun ’yan fashi, to saman ma ga yadda ta zama. An guduje wa mutuwa, an fada kabari. Saman da kasan duk a Nijeriya daya ne, domin barayi da gafiyoyi su ke rike da madafu a kasar nan. Sai dai mu roki kariya a wajen Allah.

Daga Idris A. Bajoga. 0806 526 9509

JAMA’A MU HADA KAI

Jama’a a shirya a hada kai kafin Amerikawa su zo.

Daga Adamu Azare 0806 526 9883

SHEKARAU A YI HATTARA

Gwamna Ibrahim Shekarau ka yi taka-tsantsan da wadanda ba sa son zaman lafiya a Kano kada su zuga ka. Domin da yawansu ba ma ’yan Kanon bane, balle ma su damu da zaman lafiyarta. Da zarar wani abu ya taso tserewa za su yi su bar ka. Allah ya la’anci masu ta da fitina. Allah ya sa ku gane, amin.

Daga Haruna M. Haruna Kano 0803 687 5702

’YAN UWA MU DAGE DA ADDU’A

Assalamu Alaikum. Ina kira ga ’yan uwa musulmi mu tashi tsaye da addu’a.

Daga 0803 788 5899

A INA KA SAMO WANNAN?

Assalamu Alaikum. Malam Babayo a ina ka samo cewa wasan kwallo ko buga labarinsa haramun ne a Musulunci?

Daga 0803 469 0159

’YANTO KUDUS WAJIBI NE

’Yan uwa mu sani fa cewa ’yanto Masjidul Aksa shi ne ’yanto duk masallatai. Kasancewarsa a hannun Yahudu shi ke nuna cewa sauran ma su ke rike da su.

Daga 0806 548 2850

MU CIRE HASSADA MU BI GASKIYA

Assalamu Alaikum. ’Yan Nijeriya ya kamata mu kawar da hassada mu binciki wasiyyar Danfodiyo na zuwan Mujaddadin wannan karnin, ko ma sami mafita daga halin da makiya Allah suka sa mu a ciki. Wassalam.

Daga Shehu Maraban

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International