Almizan :Yunkurin da aka yi na rage darajar Imam Ali (AS) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Yunkurin da aka yi na rage darajar Imam Ali (AS)


Daga Aliyu Saleh

Dalilin Mu’awiya na farko na kokarin rage darajar Dan Abu Talib, (Abu Turab) kamar yadda yake kiransa shi ne, domin ya rage masa daraja a idanuwan al’ummar da za su zo daga baya, sannan kuma ya cusa musu a cikin zukatansu cewa, Khalifofi uku da suka gabaci Ali sun fi shi matsayi da fifiko.

Dalilinsa na biyu kuma shi ne, domin ya karkatar da umurnin da Manzon Allah (SAWA) ya yi na cewa, khalifanci yana tare da Ahlul baitinsa, musamman kuma Hasan da Husaini (AS), wadanda su sun riski zamani da shi (Mu’awiya). Tunda kuwa shi Mu’awiya ya ga yadda Abubakar da Umar, da kuma Uthman suka yi dangane da umurnin da ya yi musu na yin biyayya ga Ali a matsayin Khalifansa bayan ya yi wafati, shi ne shi ma ya sami damar wulakanta wannan umurni a kan ’ya’yan Ali (Hasan da Husaini).

babu shakka hakar Mu’awiya ta cimma ruwa na kokarin da ya yi na ganin ya dusashe darajar Ali a idanuwan al’ummun da za su zo daga baya. Domin kuwa a wannan zamanin da muke a ciki a yanzu, idan mutum ya soma yi wa wasu Musulmi bayani a kan gwarzantakar Ali, kusancinsa da Manzon Allah (SAWA), da kuma fifikon da yake da shi fiye da sauran sahabbai, sai ka ji sun ba ka amsa da cewa; “wai ai Manzon Allah (SAWA) ya ce; ‘Idan za a hada imanin dukkan muminai na duniya baki daya, idan aka kawo na Abubakar aka hada da nasu, wai na Abubakar zai rinjayi nasu baki daya.” Shi kuma Umar za ka ji sun ce wai lakabinsa shi ne “Faruk,” wanda yake bambance karya da gaskiya, sannan shi kuma Uthman, wai shi ne ya mallaki haske guda biyu, kuma shi ne wai Mala’iku suke jin kunya.

Duk wanda ya karanta wannan matsayi wanda aka kirkira aka bai wa wadannan sahabban uku, zai ga cewa Umar aka fi bai wa fifiko a cikinsu. Hakika wannan al’amarin ba a bisa hatsari aka tsara shi ba, domin kuwa sun yi haka ne, saboda su saka wa Umar dangane da irin gudummuwar da ya ba da, musamman saboda irin rawar da ya taka, wajen nisanta Ali bin Abu Talib, Shugaban Muminai da hakkinsa na Khalifanci, wanda Allah da Manzonsa suka dora shi a kai. Daga nan ya share wa wasu Kuraishawa wadanda suka yi mulkin da suka ga dama, sannan su kuma suka bai wa mutanen da aka ’yantar a ranar da aka ci Makka da yaki, da su da ’yantattun bayi, da kuma wasu daga Umayyawa, suka ci gaba da gasa wa al’ummar musulmi gyada a hannu.

Su Kuraishawa, musamman dai Abubakar, yana sane cewa, dukkan jinjinar da ake yi musu dangane da yadda aka ce sun jagoranci musulmi, yabo mafi tsoka ya tafi ne ga Umar, domin shi ne ya jima yana mulkin. Shi ne ya jagoranci kange Manzon Allah (SAWA) daga rubuta hujjar tabbatar da Ali a matsayin Khalifansa. Shi ne kuma ya jefa kokwanto a zukatan al’ummar Musulmi bayan da Manzon Allah (SAWA) ya yi wafati, saboda ya kange su daga yi wa Ali mubaya’a. Haka nan kuma shi ne ya yi ruwa ya yi tsaki a Sakifa (dakin taro da ke Madina), ya tabbatar an yi wa Abubakar mubaya’a. Haka nan kuma a zamanin Abubakar yana Khalifa, Umar shi ne ya zama mai zaben Gwamnoni da rabon mukamai. Kai, a takaice dai, Umar shi ne ainihin Shugaba a lokacin Abubakar.

Tarihi ya ruwaito yadda Umar ya rika hana tabbatar da Sunnar Manzon Allah (SAWA), a zamanin Abubakar yana Khalifa. A cikin littafin Al-Jawhara Al-Naira Fi Fiqh Al-Hanafi, juzu’i na 1, shafi na 164, an ruwaito cewa; da akwai sunnar da Manzon Allah (SAWA) ya bari na yi wa wadanda suka rungumi Musulunci ‘Ihsani’, ta yadda za a karfafa zukatansu ga addinin. Don haka, a lokacin Abubakar na Khalifa, wadansu da suka shiga Musulunci sun same shi domin ya ba su irin wannan ‘Ihsanin’ da Manzon Allah (SAWA) ya sunnanta. Shi kuma Abubakar sai ya rubuta musu wasika, ya umurce su da su je ga Umar domin ya ba su wannan hakki nasu wanda Manzon Allah (SAWA) ya sunnanta. Da suka kai wa Umar, suka ba shi ya karanta, sai kawai ya kekketa wasikar, sannan ya ce wa wadannan mutane; “ba mu da bukatar ku, domin Allah ya tabbatar da addininsa. Ko dai ku shiga Musulunci, ko kuma takobi ya shiga tsakaninmu da ku.” Da Umar ya gaya musu haka, su kuma wadannan mutane sai suka koma ga Khalifa Abubakar, suka gaya masa yadda suka yi da Umar, kuma suna masu tambayar sa cewa ‘wai shin kai ne Khalifa ko kuma Umar ne?” Shi kuma ya ba su amsa da cewa; “shi ma zai iya zama idan Allah ya so.”

Haka nan kuma a cikin wata ruwaya daga cikin littafin Al-Isab Fi Ma’arifa Al-Sahaba, da littafin Al-Asqalani a cikin ruwayar Uyayna, da kuma cikin littafin Nahjul-balagha, juzu’i na 3, shafi na 108, an ruwaito cewa; Khalifa Abubakar ya taba bai wa wadansu Sahabbai filaye. Don haka nan ya rubuta takarda ya ba su ya ce su kai wa Umar. A lokacin da suka kai masa, nan take ya tofa wa takardar yawu, kuma ya mutsuttsuke ta. Su kuma nan take suka fusata da abin da ya yi musu, suka gaya masa bakaken maganganu, sannan suka koma suka sanar da Khalifa Abubakar abin da Umar ya yi musu, sannan suka tambaye shi cewa; “wai shin kai ne Khalifa ko kuma Umar?” Nan take Abubakar ya ba su amsa da cewa; “shi ma zai iya zama.” Daga nan sai ga Umar ya je ga Abubakar a fusace, ya ce masa; “ba ka da hurumin da za ka bai wa wadannan mutanen filaye.” Shi kuma Abubakar ya ba shi amsa da cewa; “na gaya maka ka fi ni karfin ba da umurni a cikin wannan al’amari.”

Daga ’yan wadannan bayanan na sama, za mu ga irin babban matsayin da Umar bin Khattab ya samu daga Kuraishawa da banu Umayya, har suna masa kirari da cewa; “shi gwarzo ne, kuma sadauki.” Kuma shi ne mai bambancewa a tsakanin gaskiya da karya. Har kuma suke fifita shi fiye da Manzon Allah (SAWA).

Ku yi dubi ku gani, irin halayyar da Umar bin Khattab ya rika nuna wa Manzon Allah (SAWA) tun daga lokacin da aka yi yarjejeniyar Hudaibiyya, har zuwa ranar Alhamis din tashin hankali (ranar da Manzon Allah ya ce su ba shi takarda da abin rubutu zai rubuta wa al’ummansa abin da ba za su taba karkacewa daga hanya madaidaiciya ba). Haka nan kuma shi ne ya ingiza Sahabbai suka yi watsi da sunnonin Manzon Allah (SAWA) (bayan Manzon Allah ya yi wafati). Haka nan kuma Umar bin Khattab, shi ne ya sare itaciyar alkawari ta Ridwan. Haka nan kuma, Umar bin Khattab ne ya nemi kusanci da kawun Manzon Allah (SAWA) Al-Abbas, domin ya shagaltar da Musulmi cewa, tunda Manzon Allah (SAWA) ya bar duniya, babu bukatar a rika tunawa da shi (a rika yin Maulidinsa). Wannan ne kuma sunnar da ya gadar wa Wahabiyawa har zuwa wannan zamanin da muke ciki, suke ta kumfar baki da haramta tunawa da Manzon Allah (Maulidi). Shi ne kuma kan gaba, wajen hana Sahabbai ruwaito hadisan Manzon Allah (SAWA) da kuma kona hadisan (kamar yadda muka yi bayani a baya).

Dangane da haka ne za mu fahimci dalilin da ya sa Ali bin Abu Talib a zamanin wadannan mutane ya yanke shawarar ya kebance kansa a gidansa, ya daina zuwa ko’ina. Idan ka gan shi ya fita, to kuwa ya je ne idan suka nemi taimakonsa, domin ya warware wa Sahabbai matsalolin da suka dabaibaye su, suka rasa mafita.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International