Almizan :Wakilcin addini da al’ada a fima-fiman Hausa ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Wakilcin addini da al’ada a fima-fiman Hausa

Daga Nasiru Wada Khalil na kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci da ke Kano (Shari’a Court Of Appeal, Kano) (nasiruwada@yahoo.co.uk ).

Ya gabatar da wannan takardar ne a taron kara wa juna sani na kwana daya da Hukumar “A Daidaita Sahu” ta shirya mai taken Wakilcin Al’adu Da Addini A Fima-fiman Hausa, ranar Asabar, 23 ga Safar 1426 (2/4/2005) a dakin karatu na Murtala Muhammad, Kano.

GAbATARWA

ba za a yi maganar wakilcin addinin Musulunci ba sai da ilimin addinin, don mutum ba zai iya wakiltar abin da bai sani ba, musamman abu mai ka’ida wanda ba kara-zube yake ba, kamar addinin Musulunci. Malam Zarnuji ya fada cewa; “Gudun duniya da tsoron Allah ba sa yiwuwa tare da jahilci. ” A nan akwai bukatar masu shirya Fima-fiman Hausa su san hukunce-hukuncen addininsu, sannan ne za a iya tabbatar da wakilcinsu, don in ba ilimi ko an samu wakilci to katari sunansa.

baya ga haka akwai maganar niyya, don dukkanin aiki sai da niyya, kamar yadda ya zo a cikin hadisi mai tsarki daga Ma’aiki tsira da aminci su tabbata a gare shi, cewa: “Dukkan aiki sai da niyya, kuma kowa da abin da ya niyyata, wanda hijirarsa ta zamo don Allah da Ma’aiki to ladan hijirarsa yana ga Allah da Ma’aiki. Wanda kuma hijirarsa ta zamo don duniya ko wata mace da yake son ya aura, to ladan hijirarsa yana ga wanda ya yi hijirar saboda shi.”

Ma’ana a nan shi ne wadanda suka yi fim don Allah, wato suka wakilci Musulunci, to wadannan sune suka yi wakilci na gaskiya, kuma ladansu yana wajen Ubangiji, amma wadanda suka yi don kurum amfanin da za su samu a kasuwa, ko kuma suka dan tsarma wani abu na Musulunci don kada a ce ba su saka ba, ko tunanin rashin sawar ya shafi yanayin cinikinsu ko wani abu, to wadannan ko an samu wakilcin addinin Musulunci a fim dinsu ba sunansa wakilci ba, kuma ladan abin da suka yi yana wurin wannan abin. In kasuwa ce yana cikin ribarsu ta kudi, in don neman suna ne hakan yana ga sunan da suka samu da sauransu.

KORAFE-KORAFE: KO AKWAI DALILI?

Idan muka dubi sauran sana’o’i na bahaushe a wannan zamanin za mu ga cewa babu sana’ar da aka fi saka wa ido kuma aka fi yi wa korafi irin ta Fima-fiman Hausa. To wannan korafe-korafen jama’a na menene? Dalilin dai abu ne guda daya; su ’yan fim wakiltar rayuwar Hausawa suke yi, su kuma Hausawan ba haka suke son a wakilce su ba, domin yanayin wakilcin akwai sirki a ciki da ba Hausar ba, kamar rawar kan titi, mata da miji ko saurayi da budurwa da sauransu. Amma idan muka yi waiwayen fima-fiman talabijin na ’yan shekarun baya irin su KULIYA MANTA SAbO, TASKIRA, SAMANJA da sauransu, za mu ga ba a samun irin wadannan korafe-korafen, saboda suna kokarin wakiltar hakikanin rayuwar bahaushe ne.

LARURAR LAbARI

Kamar yadda aka sani, larura tana nufin bukatuwa da ba za a iya kauce mata ba. Komai yana da irin tasa larurar, haka zalika labari yana da tasa larurar ta matsalolin da tilas sai an fade su. A Fima-fiman Hausa wasu abubuwan da ake sa wa labari, labarin ba bukatar su yake ba. Misali a cikin fim din GIDAUNIYA, an nuno Jamila Haruna tana yi wa su Farida Jallal da Maryam da kuma Rukayya fada a kan saka kananan kaya, to amma sai ga shi da aka ci gaba da fim din ba su canza irin wannan shigar ba, kuma babu wani abu da ya faru a gare su banda ita Maryam (kanwar wacce ta yi musu fadan), amma ga su sauran babu wata illa da suka fuskanta a fim din ta saka irin wadannan kayan.

A cikin fim din bAKAR ASHANA an nuna irin abubuwan da karuwai, Hausawa suke yi, wannan a iya cewa larurar labarin ce, to amma yanayin yadda aka nuna shi ne abin da ba a bisa ka’ida ba. Misali an san karuwai suna biki ko a ce ajo, haka a fim din bakar Ashana an nuna mana irin wannan biki, to amma yadda kyamara ta dauko hoto makusanci na Fati Yola tana rawa da duwawu, irin yanayin wannan hoto ba wani sako da zai isar sai dai ya tayar da sha’awa. Haka a dai wannan wakar aka nuno magajiyar (A’ishatu Dan Kano) tana juya mazaunai har aka rage saurin motsawar hoton don mutane su sami damar kallon rawar a tsanaki. Duk wadannan, ko da akwai bukatar su, an yi fajirci wajen nuna su.

HUJJAR SAKA bATSA A FIMA-FIMAI

Mafi yawancin batsar da ake saka wa a fima-fimai ba don larurar labari bane, sai don larurar kasuwa, domin in ba su yi hakan ba mutane ba za su sayi abin da suka yi ba. Misali a kwanan nan an samu Furodusan da ya yi fim babu irin rawa da waka da sauran shiririta na ba gaira ba dalili, amma labarin yana da ma’ana matuka kuma ya samu aiki mai kyau a wajen hoto da sauran abubuwan da fim yake bukata, da ya je wajen mai sayen ‘CD right’ sai ya ce masa, shi wallahi fim in ba rawa da waka ba zai iya siyen sa Naira dubu 20 ba. Hakan kuwa aka yi, bai sayi fim din ba, amma ya sayi wani wanda bai kai wannan din kyan aiki da labari ba a kan kudi mai yawa, saboda ya san shi mutane suke son saye.

WANENE WAKILI?

Tsayawa a kan abin da za a wakilta shi ne wakilci, ba kawai mai nuni da umurnin a yi abu ba, wannan abin na addini ne ko kuwa na al’ada. Saboda shi wakili har kullum abin koyi ne na abin da yake wakilta. Wakilci a wajen Malaman fikihun Musulunci biyu ne; akwai wakilci na ‘tafwili’ (a jibinta maka komai), akwai wakilci ‘takyeed’ (a iyakance abin da za ka wakilta).

Idan muka dubi cewa da yawa daga cikin masu Fima-fiman nan yara ne matasa wadanda shekarunsu ba su isa su sa su wani hange mai nisa ba, tara karatu mai yawa ba ya ga cewa a manyan ma ba duk ne suke da wadataccen ilimin addini ba da za su fadakar, to za mu iya cewa ko fa za a wakilci Musulunci, to wakilcin zai zamo nakisi (tauyayye)

MENENE ADDINI?

Addini a gurin Allah guda daya ne, wato Musulunci, wani abu wanda ba Musulunci a Hausance akan ce masa “Tada.” Wannan ya tabbata cikin Alkur’ani mai girma: “Hakika Addini (yardajje) ga Allah shi ne Dinil-Islam, wanda aka aiko Manzanni da shi, aka gina shi a kan harsashin kadaita Allah,” surah Al-imran :19.

MENENE MUSULUNCI?

Kafin mu san ma’anar Musulunci a tsinkayance akwai bukatar mu kalli kalmar kanta “Islam” mu ga ma’anarta a lugga; tana nuna mika wuya ko sallamawa, saboda haka za mu iya cewa mika wuya ga dukkanin abin da Allah ya shar’anta shi ne Musulunci. Za mu iya cewa wannan ya nuna mana cewa Musulunci ya kunshi komai na rayuwar jama’a, ba ya ga harkokin ibada. Wani bangaren kuma ya zo a Sahih Muslim daga Sayyadina Umar dan Khaddabi da Mala’ika Jibril ya zo yana yi wa Manzon Allah tambaya cewa: Menene Musulinci? Sai ya ce masa: “Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Ma’aikin Allah ne, da tsai da Salla, da ba da Zakka da Azumin watan Ramadana, da ziyartar Dakin Allah ga mai’ikon tafarki zuwa gare shi.” Abdullahi Dan Umar da ya ruwaito hadisin, ya ambaci wadannan abubuwan a matsayin shika-shikan Musulunci.

MA’ANAR AL’ADA

Bangare na biyu na wannan takarda shi ne al’ada. Al’ada ita ce “wata halayya abar sani ga wadansu mutane.” A wani kaulin kuma al’ada ita ce “jimlar hanyoyin rayuwar mutane. Ta kunshi harsunansu da addininsu da abincinsu da sana’o’insu da yadda suke yin abubuwansu, da kuma yadda suke amfani da su. Za mu duba alakar da ke tsakanin addini da al’ada, ta yadda suka hadu da yadda suka rabu.

AL’ADAR HAUSAWA

bayan zuwan Musulunci kasar Hausa, al’adu da dama sun sauya. Kasancewar kashi 90 na Hausawa Musulmai ne, sai ya zama Musulunci ya yi tasiri a kan al’adunsu. An san bahaushe da kunya da kawaici da girmama na gaba da son baki da jarumta da sauran halaye dai masu kyau. Idan aka yi dubi a kansu za a ga dukkan wadannan halaye addini ya zo da su.

Akwai bakin abubuwa, amma akan karbe su a cikin zamantakewa domin kyawunsu ko amfaninsu ga rayuwar jama’a. Misali bahaushe bai san Garu ba, Danga ya sani, amma daga baya Tubali ya zo ya karba, bulo ya zo shi ma ya karbe shi. Haka shi kansa gini mai kusurwa hudu bakon abu ne a wajen bahaushe, shi ginin da ya sani shi ne kewayayye.

Kasancewar bahaushe zai ci abinci da cokali ko zai hau mota ba ya nufin ya sauka daga kan al’adarsa. Ko amfani da wani abu da zamani ya zo da shi na saukaka rayuwa, kamar injin nika ko na surfe ko hawa, jirgin sama da dai sauransu. Amma akwai abin da shekara 1,000 yadda yake haka yake babu sauyi. Misali kunya da kara da girmama bako da kau da kai da sauransu. Wadannan abubuwa sune hakikanin al’adun bahaushe domin sune halayen da aka san shi da su.

ALAKAR ADDINI DA AL’ADA

Alakar addini da al’ada a bayyane take. Musulunci ba ya hana mutane al’adar da ya same su da ita, mutukar ba ta saba wa dokokinsa ba. Idan al’ada ta saba wa Musulunci, to tilas a bar ta kai tsaye. Amma idan ba ta saba wa shari’a ba, babu laifi a aikata ta idan ana bukata. Kamar yadda Annabi (S) ya fada a cikin Hadisin Daru Kudini, “Ubangiji ya yi shiru game da wadansu abubuwa, rahama a gare ku, ba don mantuwa ba, kada ku yi bincike a kanta.” bahaushe yana yin wankan jego, in an yi haihuwa, garar aure ko taron suna da kaurin haihuwa da kayan lefen aure, amma babu wanda ya ce haramun ne, sai lokacin da Hausawan suka fara kai al’adar matsayin wajibci. Misali a ciyo bashi don a yi gara da sauransu.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International