Almizan :Mutane 50 sun rasu a wajen zaman makoki a Iraki ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Duniya Labari

Mutane 50 sun rasu a wajen zaman makoki a Iraki

Daga Aliyu Saleh

Adadin mutanen da suka rasu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wajen jana’izar wani babban Malamin addinin Musulunci a Iraki a kwanakin baya ya haura mutane 50. Likitoci sun ce wannan harin ya biyo bayan wasu jerin hare-haren da aka kai ne, wadanda suka yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 150.

Kamfanin dillancin labarai na REUTERS, ya habarto cewa; wasu mutane 75 sun jikkata bayan wani maharin kunar bakin wake ya tarwatsa wata mota da yake ciki a cikin dandazon jama’a da suke zaman makokin wani Shehin Malamin a garin Abu Sayda, wani karamin kyauye da ke garin baqouba mai nisan kilomita 65 a arewacin bafadaza.

Ma’aikatan lafiya a garin baqouba da suka bukaci a sakaya sunansu, sun ba da labarin cewa mutane da yawa ne suka samu munanan raunuka.

babban jami’in ’yan sanda a garin, Kanar Sabah Salih ya ce, ya ga gawawwakin jama’a yaryashe a gefen hanya, masu miyagun raunuka, kuma jini yana ta kwarara ba tare da an iya shawo kan halin da suka samu kansu a ciki ba. “Mun je wajen da ’yan sanda mun ga gawawwakin jama’a barkatai a ko’ina. Abubuwan da muka gani sun munana,” in ji shi.

Wannan harin dai da aka kai ya zo ne a wani mako da jinanen jama’ar Iraki da kuma na sojan mamaya na Amurka suka kwarara.

Jami’an mamaya na Amurka suna danganta wadannan hare-haren da ake kai wa ne a wuyan mayakan Larabawa da suke haurowa daga waje domin yakar Shi’awa da Kurdawa da suke zargi da hada baki da masu mamaya da nufin dakushe shirin zaben ’yan Majalisa za a yi a kasar ranar 15 ga wannan watan na Disamba.

A ranar Asabar ma wani harin kunar bakin wake da aka kai a kasuwar ‘The Diyala bridge’ da ke dab da kudancin bagadaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13, yayin da 20 suka jikkata. A garin baiji kuwa, a ranar Asabar din dai, soja biyar ne suka rasu bayan wani hari da aka kai wa kwambar motocinsu da suke sintiri a garin.

Cibiyar sojan mamaya ta Amurka a Iraki, sun sanar ranar Lahadi cewa wani sojansu daya ya tunkuyi burji a wani harin bom da aka kai masu a kudu da garin Haditha da ke nisan kilomita 200 a arewa maso kudancin bagadaza. Dakarun kuma sun fuskanci ruwan wuta a garin Anbar, daya daga cikin garuruwan da suka yi kaurin suna a zama sansanin masu fafutika.

Kashe-kashen da ake yi wa sojan mamayan na Amurka dai a ’yan kwanakin nan sai dada karuwa yake yi duk da rarakar da suke kai wa a garuruwan da Larabawa-Sunni, wadanda suke zargi da kai masu hare-haren bama-bamai da kuma ta da kayar baya.

Mutane 77 ne suka rasu ranar Asabar bayan wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin Shi’a da ke garin Khanaqin da ke arewa maso yammacin bagadaza.

Haka nan kuma wasu maharan kunar bakin wake biyu sun kashe mutane shida sun kuma jikkata 40 bayan wani hari da suka kai ranar Juma’a a jikin wani hotal da ’yan jarida da ’yan kwangilar kasashen waje suka fi zama a bagadaza.

Shugaban Amurka, George W. bush, ya ce ba zai janye dakarunsu sama da 135,000 da ke Iraki ba, har sai sun kammala aikin da ya kai su na fatattakar ’yan ta’ada. Sai dai kuma masu adawa da yakin sai dada karuwa suke yi, ciki kuwa har da tsaffin sojojin da suka halarci yakin da ake yi a Iraki.

A wani hari na kunar bakin waken da aka kai a Iraki a ranar Talatar makon jiya a bagadaza, ya kashe mutane 30, wasu sama da 30 kuma suka jikkata.

Wannan harin da aka kai dai ya biyo bayan wasu manyan hare-haren kunar bakin wake da ake ta kai wa a babban birnin na Iraki ’yan kwanaki kafin zaben ’yan Majalisa a aka yi, da kuma shari’ar Saddam Husaini da ake ci gaba da yi.

Kazalika kuma, wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, George bush yake sanar da irin sanarwa da suke samu a Iraki, musamman a kan sake gyaran garuruwan Najaf da Mosul, da kuma garkuwa da aka yi wani bayammaci mai yada busharar kiristanci, Mista briton Norman Kember da mayakin da suke kame da shi suka yi barazanar kashe shi matsawar ba a sako wasu mayakan da ake tsare da su ba.

’Yan sanda sun ce harin da aka kai a cikin wata motar ba sa tashar Nahda da ke garin Nassiriya a kudancin bagadaza, ya yi kaca-kaca da motar, sannan kuma mutane masu tarin yawa suka rasu.

“Konannun hannaye da jikkuna da suka yi kaca-kaca, lalatacciyar motar da aka kai hari a cikinta, da kuma kayayyakin fasinjojin da ke cikin motar ne mutum zai fara gani idan ya isa wajen, yayin da kuma motocin daukar marasa lafiya na ’yan sanda suka yi wa wajen kawanya,” in ji wani dan jarida da ya isa wajen da aka kai harin.

“Ina kusa da wajen lokacin da aka kai harin,” wani mutum yana shaida wa kamfanin dillacin labarai na REUTERS a kusa da lalatacciyar motar. Ya kara da cewa, ya ga wasu fasinjojin da raunuka a lokacin da aka kai harin. “Duk wani mutum da ka ga ya saura a cikin motar nan ya rasu,” in ji shi.

A cikin watan Agusta ma dai sai da wasu motoci uku suka yi bingida a daya daga cikin manyan tashoshin mota da ke bagadaza. Wani harin mai kama da wannan ma ya faru a garin basra, daya daga cikin manyan garuruwan Shi’awa da ke kudanci.

Wani harin ma da aka kai a ranar Talatar a Ma’aikatar horar da ’yan sanda ya kashe wasu mutane 36, kamar yadda wasu manyan jami’an wajen suka sanar.

“Hare-hare za su ci gaba matsawar mai aikata laifin yaki (Shugaban Amurka George W.) bush ya ci gaba da nuna girman kai da dagawa. Duk wani abu da ya faru a bayan haka, sun biyo bayan girman kan da yake nunawa ne,” in ji wani bayani da ‘Islamic Army in Iraq’ suka fitar a shafinsu na sakar sama bayan sun yi garkuwa da Ronald Schulz, 48 a makon jiya.

Yayin da Irakawa suke juyayin yawan mutanensu da a kullum safiyar Allah ake kashewa, su kuwa Amurkawa suna can suna ta zanga-zangar nuna kin amincewa da yakin da ake yi a Iraki, musamman saboda ’ya’yansu da suke ta rasu ransu a karin kawai duk da bayanin da bush yake yi na cewa suna samun nasara a yakin. Ko a ranar Juma’a da Asabar ma sa wasu sojan Amurka biyar suka mutu.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ASSOCIATED PRESS ya fitar, yanzu yawan sojan Amurka da aka kashe ya zuwa ranar Talata, sun haura 2, 1400, kuma fiye da 1,680 sun mutu ne a fagen daga. Yayin da ita kuma birtaniya ta rasa sojojinta 100, Italiya rasa 27, Ukraine, 18, Poland, 17, bulgaria, 13, Spain, 11, Slovakia, 3, Denmark, El-Salvador, Estonia, Netherlands, Thailand, suka rasa bibbiyu, su kuma kasashen Hungary, Kazakhstan, Latvia suka rasa dai-dai kowannensu.

Tun daga 1 ga watan Mayu, lokacin da Shugaban Amurka, George bush ya sanar da kammala kai manyan hare-hare a Iraki, sojan Amurka 2,000 suka mutu a hare-haren da masu adawa da mamaya suka kai masu.

Sojan mamaya na Amurka na baya-bayan nan da aka kashe, sun hada da Kanar Joseph P. bier, 22, Sajent, Michael C. Taylor, 23, Laftanar-Kanar Kevin J. Smith, 28, a ranar Talatar nan da ta gabata a garin Ramadi.

Yahudawa sun yi kokarin kashe Husain Assaf

A ranar Jumu’ar nan ne Yahudawan Sahayoniya suka aiwatar da wani yunkuri na kashe daya daga cikin manyan jami’an Kungiyar Hizbullah da ke Leabanon. Majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da cewa an saka wani bom ne da ake iya tayar da shi daga nesa a cikin motar Malam Husain Assaf babban jami’in.

Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa; cikin ikon Allah da kuma kariyarsa, sai ya zama bom din ya fashe ne ’yan dakikoki bayan jami’in ya fita daga motar, tare da mai tsaron lafiyarsa.

Shaikh Muhammad Yazbek, shi ma wani jami’i a Kungiyar ta Hizbullah ya nuna cewa wannan wani shiri ne da Yahudawan Sahayoniya suka tsara. Sannan ya kara da cewa Malam Husain Assaf yana cikin gidansa a lokacin da motar tasa ta tarwatse bayan an tayar da bom din.

Hizbullah ta fitar da wani bayani wanda yake Allah wadai da wannan yunkuri, sannan ta nuna cewa za ta ci gaba da bin dukkanin hanyoyin da suka kamata don kare shugabanninta.

A gefe guda kuma, haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa ba ta da hannu cikin wannan yunkuri da aka yi na kashe Malam Husain Assaf.

Sai dai da ma jami’an leken asirin Yahudawa sun saba aiwatar da irin wannan aika-aikar a Lebanon da Palasdinu, inda suka kashe jami'ai da yawa, ciki har da Shaikh Ahmad Yassin da Dakta Abdul’aziz Rantisi da dai sauran su.

Mutane 130 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Iran

A ranar Talatar makon jiya ne da la'asar wani jirgin saman sojoji kirar C130 na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya fado a kan wani gini mai hawa goma na Ma’aikatar sojojin saman kasar, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 130, wasu kuma suka jikkita.

A wata hira da aka yi da Magajin garin birnin Tehran, Malam Muhammad bakir Kalibaf, ya bayyana cewa dukkanin fasinjojin da ke cikin jirgin su 94 sun rasa rayukansu hade da dukkanin matukansa. Tashar Rediyon Tehran ta nuna cewa sakamakon fadowar da jirgin ya yi a kan ginin da ke kusa da shi, wasu mutane 25 sun mutu, sannan kuma wasu 15 sun jikkita.

Wani wanda ya gane wa idonsa abin da ya faru a lokacin faduwar jirgin, ya bayyana cewa irin karfin sautin da ya ji a lokacin faduwar jirgin tamkar wata girgizar kasa ce.

Filin jirgin saman Mehrabad dai shi ne filin saukan jirgin sama da ya fi kowanne dadewa a kasar Iran, kuma a da can yana bayan gari ne. Amma a yanzu ya koma cikin garin birnin Tehran saboda fadadar birnin.

bayanai dai sun shaidar da cewa hatsarin, wanda ya faru a lokacin da jirgin ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman bandar Abbas daga filin jirgin saman Mehrabad, ya yi wannan karon ne bayan da ya fuskanci wasu ’yan matsaloli da ke da nasaba da injin jirgin.

Rahotanni dai a lokacin hada rahoton nan na nuni da cewa ma’aikatan bayar da agajin gaggawa na kasar na can na ci gaba da aikinsu na ceto a gurin da wannan abu ya faru, yayin da aka yi jana’izar wadanda aka gano gawawwakinsu.

An haramta wa kasashen OIC kafirta ’yan Shi’a

Daga Aliyu Saleh

Shugabannin kasashe 57 ne na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) suka yi babban taronsu na shekara-shekara karo na 22 a birnin Makka, kasar Saudi Arabiyya a makon jiya, inda suka tattauna matsaloli daban-daban da suka shafi kasashen Musulmi.

Wannan taro dai ya dauki tsawon kwanaki biyu ana gudanar da shi, wanda ya fara da taron Ministocin harkokin wajen kasashen, kafin daga bisani shugabannin kasashen suka shiga nasu taron kamar yadda aka saba.

babban abin da taron ya fi mai da hankali a wannan karon, kamar yadda aka bai wa manema labarai rahoto, shi ne irin yadda lamarin duniyar Musulmi ta shiga a wannan lokaci da kuma yadda ake bakanta Musulmi da sunan ta’addanci.

Haka nan kuma bayan taron an fitar da kuduri, wanda aka yi wa suna da ‘Mecca Declaration,’ wanda ya fayyace komai game da halin da duniyar Musulmi ke ciki a karni na 21. Kuma an tattauna kan lamarin kasar Iraki da Palastinu da kuma wasu lamurra da suka shafi Gabas ta Tsakiya.

Taron ya kuma amince da cewa ’yan Shi’a da a da wasu suke yi masu kallon kamar ba Musulmi bane da cewa su ma Musulmi ne na gidi. An kuma haramta wa duk wata kasa da ke cikin kungiyar kafirta su.

A wani labarin kuma, sama da mintina 40 aka kwashe ana tattunawa tsakanin Shugaban Iran, Dakta Ahmadinajadi da kuma Sarki Abdallah na Saudiyya a kebe kafin a kammala wannan taron na OIC.

bayanan da muka samu daga zauren tattaunawar, sun bayyana cewa Shugabannin biyu sun tattauna ne a kan abubuwa da suka shafi al’ummar Musulmi na duniya, da kuma batun samun karin dankon zumunci da hadin kai a tsakanin kasashen biyu da suke da tasiri a tsakanin Musulmin duniya.

Dukkan kasashen biyu sun yi ittifaki a kan cewa za su hada hannu waje daya don ganin sun shawo kan matsalolin da al’ummar Musulmin duniya suke fuskanta.

Tun bayan da ya dare kan karagar mulki bayan rasuwar dan uwansa, Sarki Fahad, Sarki Abdalah ya mika hannun zumunci a tsakaninsa da Iran. A makon jiya ma sai da Ayatullahi Sayyid Ali Khemene’i ya aika masa da wata wasika ta musamman, inda yake yaba masa da irin yadda yake sakar wa mabiya mazhabin Ahlul baiti sama da miliyan hudu da suke Saudiyya mara.

Sarki Abdallah ya mika sakon ta’aziyyarsa da jaje ga mutanen Iran, sakamakon hatsarin jirgin saman da aka yi a kasar, wanda ya jawo hasarar rayukan mutane masu tarin yawa da suka hada da ’yan jarida da sojoji.

A ganawar, sun kuma yin nazarin irin abubuwan da aka cimma a wajen taron da Kungiyar kasashen Musulmi ta duniya ta gudanar a Makka. A rana ta biyu ta taron da aka yi dai tare suka shiga zauren taron, abin da ya bai wa mahalarta sha’awa da karin karfin gwiwa a kan cewa ba wata hayaniya ko rashin fahimta a tsakanin kasashen biyu.

Lokacin da Dakta Ahamadinajadi yake ganawa da manema labarai a rana ta biyu ta taron na OIC, ya jadadda bukatar da ke akwai tsakanin Saudiyya da Iran da su hada hannu waje daya don yin maganin duk matsalolin da Musulmin duniya suke fuskanta.

Tuni dai Shugaban kasar Iran, Dakta Mahmood Ahmadinajad ya koma Tehran bayan zuwan da ya yi Saudi Arebiyya don halartar wannan taron.

Dakta Ahmadinajadi da Sarki Abdallah na Saudiyya a wajen taron OIC da aka yi a Makka

Rudami a shari’ar Saddam

Daga Hasan Muhammad

Ranar Litinin din makon jiya ne aka ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa hambararren Shugaban Iraki, Saddam Husain bayan da a farko lauyoyin da ke kare shi suka fice daga zauren kotun don nuna rashin jin dadinsu da shawarar da Alkalin kotun ya yanke ta kin saurarensu. Sun kuma bayyana damuwarsu dangane da halascin kotun.

Alkalin da ya jagorancin zaman kotun, Rizgar Muhammad Amin ya fusata lauyoyin ne lokacin da ya hana su su yi magana don bayyana fahimtarsu ta cewa “ita kanta kotun,” a cewarsu, “haramtacciya ce.” Amma daga baya Alkalin ya bar su sun yi magana bayan da aka dawo daga hutu na minti 90.

bayan dan gajeran lokaci da aka saurari shari’ar kafin janyewarsu har sau biyu, jami’an kasar sun ce suna fatan kwanaki hudu da za a yi ana sauraron karar zai bai wa shaidu 10 da ake da su damar bayyana gaban kotun kafin a sake dage ta don ba da damar gudanar da zaben da za a yi ranar 15 ga watan Disamba.

Daya daga cikin lauyoyin, kuma tsohon Ministan shari’a na kasar Katar, Najib Al-Nuemi, ya bayyana shakkunsa kan halascin kotun. Shi ma tsohon Antoni-janar na kasar Amurka, Ramsey Clark, ya fada cewa, “matukar ba a yi adalci ba a shari’ar, to za ta raba kan kasar Iraki ne a madadin ta hada kanta.”

Daga nan sai ya yi kira da a kara tsaurara matakan tsaro ga lauyoyin Saddam bayan da aka kashe wasu lauyoyin nasa biyu a makon da ya gabata.

Masu aiko da rahotanni sun ruwaito cewa an sami rudani a yayin zaman kotun, inda lauyoyi suka rinka yi wa Alkalin kotun ihu, shi kuma yana daka masu tsawa. Shi kuwa gogan naka Saddam sai guna-guni yake yi a inda yake tsaye yana fuskantar tuhuma.

Lokacin da aka dawo zaman kotun, Alkali Amin ya tabbatar da cewa kotun za ta karbi rubutattun bayanai ne kawai a matsayin shaida, yana mai barazanar cewa in har lauyoyin suka sake fita, to zai nemi sauyin su. Shi dai Saddam da dan uwansa barazan Ibrahim al-Tikriti sun yi wasu kalamai na jaddada kaunarsu ga Iraki da kuma yin tir da sojin mamaya.

Hambararren Shugaban na Iraki tare da wasu mukarrabansa bakwai suna fuskantar tuhuma ne dangane da zargin da ake yi musu na kashe musulmi ’yan Shi’a a garin Dujail na arewacin Iraki bayan da ya gano wani shiri na yunkurin kashe shi a shekarar 1982. Kuma in har an tabbatar da wannan zargin, suna iya fuskantar hukuncin kisa.

Shaida na farko da ya fara bayyana a gaban kotun, Ahmad Hasan Muhammad al-Dujaili, ya fada cewa an tsare mutane da daman gaske a wancan lokacin kuma da dama daga cikinsu an kashe sune. “Wani abin tausayi, domin har da mata da yara aka kama aka tsare,” in ji shi. Haka kuma ya fada cewa ya ga wasu daga cikin makwabtansa da ya

tabbatar an kashe su.

Kimanin shaidu goma ne aka gayyato don su ba da shaida a kan kisan na Dujail kuma da damansu an bukaci da su boye kansu don saboda dalilai na tsaro.

A yayin da yake kare kansa daga zargin da ake yi masa na kashe mutane 148 a garin Dujail a shekara ta 1982, Saddam Husain ya yi watsi da dukkan zargin, tare da cewar wata makarkashiyar juyin mulki ce mutanen garin suka bukaci shirya masa, “kuma duk Shugaban kasar da aka yi wa yunkurin juyin mulki, ya zama wajibi a kansa ya dauki matakan hukunta wanda ke da alhakin makircin,” in ji Saddam Husain.

A yayin da mai shari’ar ya bukaci dakatar da Saddam lokacin da ya ke bayani, tsohon Shugaban ya mai da masa martani da kakkausar harshe, cewa shi fa ba ya tsoron hukuncin kisa, a game da haka, a bar shi ya barje guminsa dalla-dalla a game da abubuwan da ya sani cikin wannan harka.

bayan sa-ín-sar da aka yi tsakanin Alkalin da Saddam Husain, an dage shari`ar har zuwa ranar 21 ga wannan watan na Disamba da muke ciki.

A yayin da aka dage shari’ar da ake yi wa Saddam Husaini, an ci gaba da samun tashe-tashen hankula a cikin kasar, inda aka ruwaito cewa sojojin Amurka 14 suka rasu sakamakon wasu hare-hare guda uku da aka kai masu a kasar ta Iraki.

Mafi muni daga cikin hare-haren shi ne wani harin bam da aka dana a gefen hanya a kusa da birnin Falluja, wanda ya halaka sojojin Amurka 10, sannan 11 suka samu raunuka.

birnin Falluja dai ya kasance wani dandalin wani mummunan gumurzu tun bayan kifar da gwamnatin Saddam Husain shekaru biyu da rabi da suka wuce. To amma a ’yan watannin nan zaman lafiya ya dawo a birnin. Sauran sojoji hudu kuma sun mutu ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai masu.

A halin da ake ciki dai, da yawa daga cikin shugabannin siyasar Amurka na kira ga Shugaba bush da ya janye dakarun kasar daga Iraki.

A kuma can yamma da birnin bagadaza sojojin Amurka da na Iraki sun kaddamar da wani farmaki a kan masu fafutika.

An kashe Daraktan fim din ‘OMAR MUKTAR’

Daraktan shahararrun Fima-fiman nan guda biyu da aka shirya kan tarihin Musulunci, wato 'The Message' da kuma 'Omar Muktar:’ ‘Lion of the Desert,' ya riga mu gidan gaskiya. Darakta Mustafa Akkad yana daga cikin mutane akalla 67 da suka mutu sakamakon wani harin bam da wasu ’yan gwagwarmaya suka kai a wasu otal-otal guda uku a birnin Amman na kasar Jodan a ranar Laraba, 9 ga Nuwamba, 2005.

Kamar yadda Mujallar Fim da ake bugawa da Harshen Hausa a Nijeriya ta watan Disamabar nan ta ruwato, Akkad dan asalin kasar Siriya ne, kuma yana daga cikin kalilan din daraktocin fim da suka yi tasiri a masana’antar shirya majigi ta Hollywood da ke Amurka. Ya rasu a ranar Juma'a, 11 ga Nuwamba, a wani asibiti da aka kai shi don ceton ransa bayan ya ji munanan raunuka lokacin da bam din da ’yan gwagwarmayar suka dana ya tashi a daidai lokacin da ake yin wani bikin aure a daya daga cikin otal-otal din.

Diyar Al-Akkad, mai suna Rima Akkad Monla, ’yar shekara 34, tana daga cikin mata ’yan bikin, kuma ita ma ta mutu a harin da aka kai, in ji Mahaifiyarta, Patricia, wacce matar Akkad ce a da.

Al-Akkad ya shirya fim dinsa na farko cikin harshen Turanci a kan tarihin rayuwar Manzon Allah (SAW) a cikin 1976, ya sanya masa suna ‘The Message,’ wanda jarumin fim din shi ne shahararren baturen nan Anthony Quinn. babban kalubalen da ya fuskanta wajen shirya fim din shi ne hanin da aka yi a Musulunci a nuna wata fuska da sunan fuskar Annabi Muhammadu (S). Jarumi Anthony Quinn ya fito ne a matsayin Kawun Annabi, wato Sayyidina Hamza.

Al-Akkad ya ba da umurni a fim dinsa na biyu, wato ‘Lion of the Desert,’ a cikin 1981, inda a cikinsa har ila yau jarumi Quinn ya fito a matsayin wani barde dan kasar Libya mai yakar mulkin-mallaka, mai suna Shaikh Omar Mukhtar. Kowanne daga cikin wadannan Fima-fiman ya yi tasiri matuka a kasashen Musulmi da ma wadanda ba na Musulmi ba. banda wadannan Fima-fiman biyu, har wa yau Akkad ne babban Furodusan wani fim din Turanci na ban tsoro mai suna ‘Halloween.’

An haifi Al-Akkad a garin Alippo da ke arewacin Siriya a cikin 1935. Amma tun lokacin da ya gama karatun sakandare a cikin 1950 ya koma Amurka da zama. Hasali ma dai har zuwa mutuwarsa shi dan Amurka ne. Ya rasu yana da shekara 68 a duniya.

Kanwar Akkad, wato Laila, ta ba da tabbacin cewa Akkad ya mutu a harin kunar bakin waken da aka kai a otal din. An dauki gawar Rima aka kai ta Libya, aka bizne ta a babban masallacin Juma'a na birnin Tripoli. Mijinta Ziad Monla da sauran danginsa sun halarci jana’izar, wacce tsohon Firaministan kasar Lebanon, Najib Mikati, ma ya halarta.

Majiya kwakkwara ta ruwaito cewa; Akkad yana da kishin shirya fima-fimai kan rayuwar Larabawa irin ta zamanin da. Misali, ya shafe shekaru yana son ya samu kudin da zai shirya fim kan rayuwar gwarzon Musulunci din nan mai suna Saladin, amma ya rasa wanda zai ba da kudin. Manufarsa a fim din ita ce ya nuna cewa birnin Kudus birni ne na Larabawa ba na Yahudawa ba. Ya ce ya kai shekara 20 yana neman wanda zai dauki nauyin fim din, amma ya rasa. Ya ce, Shugaba Saddam Husaini na Iraki ya taba nuna sha’awarsa ta daukar nauyin shirin, amma sai Amurka ta hambarar da shi daga mulki. bugu da kari, Al-Akkad yana da burin shirya fim kan yadda dabi’un Musulunci suka yi tasiri a tsohon lardin Andalusiya, inda kasar Spain take a yau.

Mutuwar Daraktan ta girgiza jama’a a kasashen Musulmi da dama. Saboda yadda aka zubar da jinin fararen hula wadanda ba su ji ba ba su gani ba, jama’a da dama sun yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi da sunan ana so a kori sojojin mamaya na Turawa daga yankin Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar Alka’ida, a karkashin jagoranta na Iraki, wato Abu Mus’ab Al-Zarkawi, ta yi ikirarin cewa ita ce ta dauki nauyin kai hare-haren a otal-otal din. Al-Akkad yana cikin otal din ‘Radisson SAS Hotel’ lokacin da bam din daya ya fashe.

Sarki Abdullah II na Jordan ya sha alwashin kama wadanda ke da hannu wajen nasa bam din.

A wata hira da ya yi da gidan rediyon Muryar Amurka makonni kadan kafin rasuwarsa, Daraktan ya ce, “Akwai fa lokacin da dukkan sarakunan Turai suke turo ’ya’yansu zuwa kasashen Musulmi, musamman yankin Kodoba, don su koyi kimiyya, da ilmin hada magunguna, da lissafi, da kiwon lafiya, da ilmin taurari. A lokacin mu Musulmi wata tsiya ne; mu muka ba duniya wani abu da take tinkaho da shi. Zan so in yi fim kan wancan zamanin don na nuna wa jama’a cewa shi fa Musulunci ba Taliban bane ko kuma ’yan ta’addan nan.”

A kan soyayyarsa ga shirin fim tun yana yaro, Al-Akkad ya ce, "Lokacin muna matasa, babu abu mafi alfahari kamar a ce ka zama Daraktan fim a Hollywood. Ni a gurina babban abin yin mafarki ne. Abin ya kasance na ban dariya lokacin ina zaune a Alippo. Ina so in je in koyo aikin ba da umurni a fim, kuma sai ya kasance abin ban dariya domin idan har kana son ka yi aikin Darakta, to sai dai ka tafi Masar ko Faransa, to amma ni sai na nace kan cewa sai na je Hollywood.”

Ya kammala karatu a Jami’ar Kalifoniya, inda ya karanci hikimomin wasannin kwaikwayo. A 1976 ya shirya ‘The Message,’ wanda shi ne fim na farko da aka yi a Holywood mai nuna labarin Musulunci a ko'ina a fadin duniya.

A cikin 1978 ya yi fim din ban tsoro mai suna 'Halloween,' wanda ya samu karbuwa nan da nan, ya kuma sa daraktoci da dama suka shiga koyon yadda ake yin fim din ban tsoro a Amurka.

A cikin 1981 ya saki ‘Lion of the Desert’ a kasuwa, inda ya nuna yadda Omar al-Mukhtar ya jagoranci tawayen da Larabawan kasar Libya suka yi wa Turawan mulkin- mallaka ’yan kasar Italiya.

Rundunar sojojin Amurka ta sayi kwafe 100,000 na kowanne daga cikin wadannan Fima-fiman biyu kafin ta kai wa Iraki hari, don sojoji su fahimci yadda Larabawa da kasar Larabawa suke.

Al-Akkad ya cakuda al’adar rayuwar Turawa da ta Larabawa, yana more kowacce daga cikin su har ya rasu. A cewar sa, a cikin gidansa shi balarabe ne, amma yana fita kofar gida sai ya rikide ya zama ba'amurke.

Al-Akkad ya rayu a matsayin mai kare addinin Musulunci, to amma abin juyayi shi ne yadda wasu masu ikirarin kare Musulunci ne suka halaka shi. Allah ya jikansa, amin.

An sake kai wani mummunan harin bom a Lebanon

Wani harin bom da aka kai a yankin arewa maso gabashin birnin beirut na kasar Lebanon ya yi sanadiyyar mutuwar Jebran Tueni, wani dan jarida mai tsananin kin jinin manufofin kasar Syria a Lebanon, yayin da aka kai hari kan jerin wasu motoci da yake ciki.

Rahoton tashar talabijin ta AL-JAZEERA ya tabbatar da cewa; akalla motoci goma ne suka kone kurmus sakamakon wannan hari da aka kai, sannan kuma wasu mutane da dama sun jikkita.

Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa; inda bom din ya fashe wani yanki ne da mabiya addinin kirista suke da yawa da ke kusa da ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke bincike kan kisan gillar da aka yi wa tsohon Firaministan kasar, Rafik Hariri.

Wani dan Majalisa ya fada wa manema labarai cewa cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai Niqola Fluti daya daga cikin masu gadin shi Jebran Tueni.

Tuni dai har wasu daga cikin ’yan siyasar kasar Lebanon sun fara nuna yatsan zargi kan kasar Syria dangane da wannan kisan gillar. Sai dai ita kuma Syria ta nisanta kanta da hannu a wannan al’amarin.

Kamar dai yadda aka sani ne, rahoton da Mehlis yake harhadawa kan binciken wanda ke da alhakin kashe Rafik Hariri shi ma ya nuna cewa jami’an kasar Syria na da hannu dumu-dumu; zargin da Syria ti yi Allah wadai da shi.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International