
Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426
Bugu na 694
| Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Hatsarin jirgin sama a Kaduna
Mutane biyu ne suka rasa rayukan su a sanadin wani hatsarin jirgin sama a Kaduna. An sake samun hatsarin wani karamin jirgin sama mallakin wani dan kasuwa na garin Maiduguri Alhaji Mohammad Ndimi a filin saukan jiragen sama dake Kaduna wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu ciki harda wata mata fasinja. Rahoton jaridar 'This Day' ta harshen turanci da ake bugawa a Nigeria ta bayyana cewa mutane biyun da suka rasa ransu sune matukin jirgin saman captain Shuaibu Ali da kuma wannan matar wadda ba'a gane ko wacece ba har ya zuwa wannan lokacin. Wata majiya ta tabbatar da cewa jirgin ya tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja inda ake jin zai dauko wani surukin tsohon shugaban kasr ne Ibrahin Badamsi Babangida. Koda yake dai har yanzun ba'a tabbatar da dalilin wannan hadari ba amma an bayyana cewa jirgin ya shafe tsawon shekaru takwas yana zirga-zirga a cikin gida kuma na nuna cewa ba'a dade da yiwa jirgin gyara ba. Akwai dai wasu rahotanni dake nuna cewa jirgin ya sami matsala ne yayin da yake gudu a kan titin da yake bi wajen tashi, wanda dama jama'a keta korafin cewa wadannan titunan suna da matsala kuma gwamnati taki kokarin gyarawa. Dama dai a baya ma an sami wani hatsarin na jirgin saman wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
An yi wani mummunan hadarin mota a AdamawaMutum 19 sun rasu nan take a wani mummunan hadarin mota da ya afku a kauyen Kwanar Mai-Saje a Karamar Hukumar Lamurde ta Jihar Adamawa. Wakilin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya ruwaito cewa, hadarin ya afku ne a ranar Talata makonjiya da misalin karfe goma na safe lokacin da wata tirela dauke da siminti ta hau kan wadansu motocin tasi kirar dafa-duka guda biyu. Wadannan motocin tasi kamar yadda Wakilin jaridar ya samu labari, sun yi lodi ne daga Yola, daya za ta Kano, daya kuma za ta je Jos, sai suka tafi suna bin juna. Da suka zo Kwanar Mai-Saje, sai ga wannan tirela da ta dauko siminti daga Gombe za ta je Yola. A nan ne tirelar ta kwace wa direbanta ta hau kan wadannan kananan motoci guda biyu. Da farko an sami gawarwaki 18 ne, 16 na manyan mutane, biyu kuma na kananan yara, amma daga baya aka ce mutum daya daga cikin wadanda aka kai asibiti shi ma ya rasu. A yanzu haka dai gawawwakin na nan a babban asibitin garin Numan, sannan kuma wadanda suka yi rauni ana nan ana yi musu magani. Mataimakin babban Kwamandan shiyya na Hukumar kiyaye hadurra na jihar Adamawa, Alhaji Umaru Abdullahi shi ya jagoranci jami’an Hukumar da na ’yan sanda zuwa inda hadarin ya afku. Don haka ya roki jama’ar da suka san ’yan uwansu sun yi tafiya a wannan rana su je asibitin Numan don su duba ko akwai ’yan uwan nasu cikin wadanda wannan hadari ya rutsa da su. Alhaji Umaru Abdullahi ya yi amfani da wannan dama ya jaddada kiransa ga gwamnatin Tarayya game da gyaran hanyar Yola zuwa Gombe, wadda ya ce ta lalace ainun. Ya ce a wannan shekara kawai, an yi hadari akalla goma a wannan hanyar saboda munin ta. Ya ce hanyar da ta tashi daga Numan zuwa Guyuk ta lalace, haka ma wadda ta tashi daga Yola zuwa Fufore zuwa Gurin, kuma ana yawan samun hadari. Haka kuma ya yi fatan za a ci gaba da aikin gyaran hanyar Yola zuwa Mubi. Mataimakin babban Kwamandan ya jaddada bukatar da ke akwai ga direbobi su rika bin dokokin tuki. Ya ce ya kamata masu motoci su rika kula da inda suke ajiye motocinsu. Da ya juya kan masu tuki da hawa babur kuwa, ya tunatar da su ne kan doka da ke tafe ta sanya hular kwano. Ya ce daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa, za a ci tarar Naira 5,000 ga duk wanda ya karya wannan doka ko wanene shi. Ya ce dokar ta shafi duk mai hawa babu hular kwanon, na haya ne, ko na kashin kai, ko kuma na gwamnati. Kamar yadda ya ce, za su yi amfani da kudin tarar wajen gudanar da ayyukan da suka sanya a gaba kamar bude asibitoci a kan hanyoyi da biyan likitocin da za su dauka.
Yara 500 sun mutu a KatsinaYara 500 ne suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar kyanda daga farkon wannan shekarar zuwa yau a jihar Katsina. Darakta mai lura da kiwon lafiyar yara na ma’aikatar lafiya a jihar Katsina, Dakta Ahmad Muhammad Kabisiyu ne ya sanar wa manema labarai haka. Ya ce, wannan adadin yara da suka mutu daga cikin yara fiye da 2000 ne da suka kamu da wannan cuta a wannan shekara. Dakta Ahmad ya ce, haka ne ya sa hukumarsa ta tashi haikan wajen fadakar da jama’a muhimmancin allurar da za a fara wa yara a farkon wata mai zuwa. Ya ce ana son a yi wa yara kimanin miliyan biyu da rabi wannan allura. Wannan adadi zai kai fiye da kashi 40 cikin 100 na adadin yaran da ya kamata a yi wa allurar. Daraktan ya kara da cewa, an zabi cibiyoyin gudanar da allurar guda 190 a jihar. Wuraren in ji shi sun hada da makarantu da kasuwanni da gidajen masu unguwanni. Haka kuma Dakta Ahmad Muhammad ya ce, an dauki jami’an da za su gudanar da wannan allura har su 13,000, wanda tuni suka fara samun horo. Yaran da za a yi wa wannan allura, ’yan daga wata tara ne zuwa shekara 15. Za a fara daga ranar 6 zuwa 10 ga watan gobe. Ya ce, hukumarsa ta tanadi allurai har kusan miliyan uku. Dokta Kabisiyu ya bayyana cewa, wannan cutar ta kyanda ta fi tsanani a arewacin kasar nan. Daga nan sai ya yi kira ga iyayen yara su fito da yaransu domin a yi musu allurar. |
| Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |