
Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426
Bugu na 694
| Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
Abin da na ji game da Saddam Husaini (2)
Na ji daga cikin kasashen Larabawa ba wadda ta taimaka wa Iraki irin kasar Kuwait. An ce a lokacin yakin, bude kofar baitulmalinta ta yi ta ce Saddam ya yi yadda ya ga dama da ajiyar da ke ciki. Kamar almara, sai na ji Saddam Husaini ya mamaye Kuwait yana fadin wani sashe ne na Iraki. Wani lokaci kuma ya ce yana zargin suna satar masa mai, yana nanata cewa komai zai faru ya faru.
Na ji duk kasashen ’yan uwansa Larabawa sun juya masa baya suna kiran ya ba su kunya, ya kuma kwance masu zani a kasuwa da rana tsaka. Na ji Turawan duniya sun buda bakunansu suna fadin; yaya Saddam zai yi haka? Suna cewa abin da ya yi ba ta sabuwa, bindiga a ruwa. Na ji an fara gangamin yakar Saddam, duniya ta buga kuge an ce kowa ya kawo karo-karo a hada rundunar da za ta kore shi daga Kuwait. Na ji da Saddam ya ga duk duniya ta juya masa baya an nufo shi, sai ya yi kwaikwayo daga Fira’una ya zama na kwarai har ma ya sanya kalmar ‘shahada’ a jikin tutar kasarsa. Na ji an fara nuno shi yana salla a masallaci cikin jama’a har ma yana daura makawiyya. Wani lokaci har yana jan carbi. Na ji an ce wasu Malaman Iraki sun ce za su koya wa Saddam iya zaman salla tun da ya fara yi a gaban jama’a. Na ji Malam Zakzaky (H) yana fadin tsohon ja’iri bai iya komawa Mujaddadi cikin dare daya. Yana fadin kar jama’a su rudu da rudamin Saddam Husaini, su yi bitar rayuwarsa ta baya, don su gano waye shi? Na ji yana fadin yakin Saddam da Amurka da taron danginta fadan kare ne da ubangidansa. Yana cewa ba yaki bane na karya da gaskiya, a’a ubangidan kare ne ke son ladabtar da karensa. Na ji mutane sun yi wa Malam Zakzaky (H) caa a lokacin saboda sun gaza fahimta abin da yake nufui Na ji an kori Saddam daga Kuwait yana kaskantacce. Na ji bayan da Saddam Husaini ya janye daga Kuwait ya koma kasarsa sai ’yan kasar suka lura da cewa yanzu bai da goyon bayan duniya, don haka sai suka ta da bore na kin jininsa da niyyar su tsige shi su kafa gwamnatin jama’a wadda mutane suka kafa bisa shari’ar Musulunci tsantsa. Na ji har ya fara shirin barin kasar domin yana tsoron kada in ya auka wasu sojan duniya da ke Kuwait su auka masa. Na ji cewa sai kasashen kafirai suka lura cewa idan aka bari wancan ta da kayar bayan ta yi nasara, to gwamnatin da za a kafa ba su da hannu a cikinta, kuma ba su iya juya ta. Na ji nan da nan sai suka ba shi sakon cewa duk matakin da ya dauka na murkushe ’yan tawayen ba za a zarge shi ba, za a mai da lamarin matsalar cikin gida ce. Na ji yadda har kwararru aka tura masa ta hanyar wata kasar Larabawa, wadda ake jin Masar ce, a kan yadda zai yi abin salim-alin ba tare da duniya ta ji ba. Na ji nan da nan sai kawai ya aika da tankoki da sojoji, inda suka yi ta’addancin da ba wanda ya san ya aka yi domin ba a bar wata hujja ta fita ba. Na ji abin da kawai kafofin watsa labarai suka rika yadawa shi ne wai ana bore a wasu garuruwan Iraki, amma wai an tura ’yan sandan kwantar da tarzoma, wai ma suna ta samun nasara a shawo kan lamarin. Na ji manyan kasashen Yammaci na cewa boren da ke faruwa a Iraki wai matsalar cikin gida ce, wai Saddam ya kamata ya yi maganin abinsa, wai yana yi. Na ji rahoton da kafofin Turai suka watsa shi ne wai rikicin wai ’yan sanda ke kwantar da shi, wai ana jin mutum daya kawai ya mutu, wai sai wadanda kuma ko an ji wa ciwo? Na ji da Amurkawa suka kama Iraki a bayan nan, kaburburan wadanda aka kashe a wancan bore saka fara tsinkaya, inda suka yi masu alama. Na ji sun ce suna son nuna wa duniya shaida domin wai ta gamsar da duniya cewa dama can Saddam dan ta’adda ne. Na ji sun bai wa kaburburan suna da kisan dabbanci, tare da rufe su a wuri guda cakude da yawa don kau da doyin wuraren domin kar a taba ganewa. Na ji wadannan shaida da tuhuma na daga cikin tuhume-tuhumen da ake wa Saddam, an ce ya kashe ya kuma boye don kar a gane ya aikata. Na ji dalilin da ya sa suka auka wa Saddam karo na biyu shi ne domin sun tabbatar yanzu babu wani amfani da zai kara yi masu. Na ji sun duba sun laluba shin ko yana da sauran mamora, aka ce babu, yanzu saura wurgarwa. Na ji kasashen na iya kashe Saddam ko su sa a yi masa juyin-mulki, ko kuma su tursasa masa ya yi gudun hijira. Na ji sun gwammace su shiga da sunan yaki domin su iya kafa sansani mai karfi a garin. Na ji yanzu amfanin da ya rage wa Saddam a wurin su ya yi taurin kai ya zauna a fadarsa har sojojin Amurka su shigo da sunan yaki. Na san Iraki na da gwanayen sojan kasa, domin an yada cewa duk Gabas ta Tsakiya banda Iran ba wanda ya kai su karfin sojan kasa. Na ji da Amurkawa suka tunkare su, mafiya yawa tserewa suka yi, suka ranta a na kare, ko kuma suna sajewa da mata da tsaffi. Na ji ana tambayar ina dakarun Iraki? Ina ‘Republican Guard?’ Ina sojan musamman din na masu kare Saddam (fidiyen)? Ina sojan sai-kai da aka tsara za su kare Iraki? Na ji a duniya ba wanda bai yi mamakin saurin faduwar Iraki ba, har wasu na cewa abin kamar mafarkin safe? Na ji Saddam ya yi batan dabo har na fara tunanin lalle yana hannunsu za su fito da shi lokacin da suke son sake wani amfani da fitowar tasa, ko kuma sun san inda yake, kuma suna sa ido domin tabbatar da cewa lafiiyarsa ba ta tabu ba. Na ji daidai lokacin da Bush ke wani buki a Amurka, sai aka yayata wa duniya cewa an gano Saddam. Na ji cikin wani ginin karkashin kasa aka gan shi, kai ka ce wani kurege ne, wai da kudi wai ma da bindiga har da gado wai a ramin, ba wani abinci da aka samu wanda yake ci, kamar mai yajin kin cin abinci. Na ji an ce ana ta nuna hotunan don ma kar wani ya sa wani shakku ko tababa, ko kuma ya samu raunin imanin gaskiyar labarin. Na ji wai ana shiga wai sai ya ce, “ni ne Saddam Husaini.” Wai sai sojan Amurka da suka jagoranci shiga ramin suka ce masa, “Shugaba Bush yana gaishe ka.” Na ji wannan ya girgiza shugabannin kasashen Larabawa, wadanda wannan ya isar masu da sakon cewa idan ba su bi yamma ba ga yadda za a yi masu. Na ji kwana daya da gano Saddam a a rami, Libya ta mika wuya, Gaddafi ya sanar da cewa ya yi watsi da shirinsa na makamin nukiliya, har ma ya gayyato Amurkawa su zo su kwashe kayan su yi yadda suke so da su. Suka lafta kayan a jiragen ruwa suka yi na Amurka da su. Na ji Bush ya yabi Gaddafi, har ma ya ce yanzu ya waye ya shigo cikin wayayyu, har yana cewa yanzu kofofin hulda za ta bude da Libiya da Amurka. Na ji an ce amfani da Saddam ya kusa karewa saura su aje shi a matsayin abin misali da kuma nuna darasi. Na ji Amurkawa sun yi kakkyawan tanadi na Saddam kar ya mutu, suna ba shi abinci mai gina jiki da lafiya, ba su aje komai kusa da shi wanda zai yi yunkurin kashe kansa da sunan ba shi kariya kar a kashe shi. Na ji suna son su yi ta yi masa zilla, tozarci da wulakanci, zuwa lokacin da suke jin cewa gawarsa suke son gani. Na ji an watsa wasu hotunan Saddam yana wanka daga shi sai kamfai, ga shi a hoton, ga shi nan yana dauraya a wani hoton, yana yarfewa kafin ya shanya. A wani kuma ya shanya, a wani ya rike kugu yana hutawa kafin ya dauko singileti ya fara wanke ta. Na ji an kai Saddam kotu ana gaya masa laifinsa, amma ya ce bai yarda da kotun ba. Na ji a wani zuwa kotun da aka yi Saddam yana fada cewa har yanzu shi ne Shugaban Iraki; uhu-uhm, Hausawa na cewa mafarin hauka tofar da miyau. An ce har irin zaman nan yake, irin wadda ya saba yi lokacin yana karagar mulki, in yana magana yana amfani da kalmomin iko da ba da umurni. Mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura! Na ji za a rika watsa shari’ar ne kai tsaye a duniya, duk tashohin duniya mallakin Yammacin Turai kai tsaye za su rika nunawa. Na ji ana cewa gaskiyar Imam Khomaini (RA) a kan Saddam ta fito, shekaru bayan rasuwarsa. Duk abin da ya fadi a kansa ga su nan sun fito fili. Na ji ana cewa addu’ar Imam Khomaini (RA) a kan Saddam ta karbu har ta bayyana da rana tsaka muna gani. Na ji ana cewa mai tababar addu’ar bayin Allah ba ta amsuwa tun a nan duniya, to ya tambayi Saddam Husaini ya sha labari. Na ji wani Bafullatanin da ya ji yana rataye da sandarsa ya dage kafarsa guda yake wa wani abokinsa bayanin irin wulakancin da Saddam ke ciki. Yana tambayar dan uwansa cewa zai yiwu mutum yana bisa gaskiya har da tutar La’iha illallah a jikin tutarsa a yi masa haka? Na ji dan uwan nasa yana fadin lamarin da kamar wuya, wai gurguwa da aure nesa. Ai rayuwa akwai jarabawa, akwai kuma tozarci. Allah ba ya taba barin a tozarta nasa ,sai dai ya jarraba shi, wanda daga baya ya ba shi nasara. Na ji yana jaddada masa cewa abin da ke samun Saddam a yanzu sakamako ne na ayyukansa na baya yake gani tun a wannan duniyar. Na ji wasu da suke juyayin lamarin Saddam suna cewa; “ya Allah ka ba mu ikon gane gaskiya, gaskiya ce, kuma ka ba mu ikon bin ta, ka nuna mana karya kuru-kuru, ka kare mu daga gare ta.” Na ji kawai zuciyata ta buga, kai tsaye ta ce, amin. Na ji ta mai karatu ma cewa za ta yi, “amin summa amin.” |
| Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |