
Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426
Bugu na 694
| Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
Mu’ujizar hubbaren Imam Ridha (AS) ta sake bayyanaDaga Hasan MuhammadA tsakiyar makon shekaranjiya ne, wani abin ban mamaki ya faru a hubbaren Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad na lardin Khurassan. Rahoton kafar watsa labarai na 'Intikhab' daga Mashhad ya nuna cewa; wani kare mai kiwon shanu ne ya shiga hubbaren na Imam Ridha (AS) duk da tsananin yawan jama’a da suke ta dafifi suna son shiga. Karen yana shiga, sai ya nufi kusa da hubbaren, sannan ya sunkuyar da kansa kasa ya shiga kuka tamkar yadda masu ziyara mutane suke yi. Yayin da daya daga cikin masu gadin kofofin shiga hubbaren yake amsa tambayoyin manema labarai kan wannan lamari, ya nuna cewa shi kansa ya yi mamakin yadda wannan karen ya wuce ya shiga hubbaren, domin kuwa shi kansa ya yi kokarin hana shi yayin da ya ga ya nufo wajen don shiga ta kofar da yake tsaye, amma ba tare da wani haushi ko hayaniya ba, sai kawai ya ketare shi ya wuce. Haka nan kuma yayin da wannan kare ya shiga hubbaren ya rika kaucewa hawa kan shimfidar da aka yi cikin natsuwa har ya zuwa lokacin da ya isa inda yake bukata. Masu lura da harkokin hubbaren sun bayyana cewa, yayin da ya rika kuka, an ga yana zufa kamar ruwa ya jika shi, sai suka dauke shi suka dora shi a kan wata shimfida, sannan suka dauke shi gaba daya suka fitar da shi wajen masallacin. Wannan abu ya bai wa masu ziyara mamaki dwarai da gaske, sannan kuma hotunan da kamarori suka dauka na Karen, yanzu haka an sanya su a jaridu da mujallun kasar Iran.
Bush ya yi yunkurin kai hari kan ofishin ALJAZEERA da ke DohaA yanzun haka dai ofishin gudanarwa na tashar talabijin na ALJAZEERA sun fara wani kokari na gudanar da bincike kan rahoton jaridar ‘DAILY MIRROR’ ta Britaniya, wanda ke nuna cewa Shugaban Amurka, George W. Bush na shirin kai hari kan ofishinsu da ke Doha. Jaridar ta ‘DAILY MIRROR’ ta kara da bayyana cewa a wata ganawa ta asiri da Bush ya yi da Tony Blair ne a ranar 16 ga watan Afrilu ya gabatar da wannan magana, kodayake a lokacin shi Blair ya nuna shakku. Rahoton ya nuna cewa karkashin yunkurin na Bush, yana son ne ya kai hari kan ofishin ALJAZEERA da ke Doha da kuma sauran manyan birane na duniya. Bayan bayyanan rahoton, bangarori daban-daban na jama’a na ta mai da martani, inda wasu ke ganin cewa Amurka da ke sahun gaba wajen nuna ’yancin fadin albarkacin baki bai kamata ta yi wannan yunkuri ba. Tashar talabijin ta ALJAZEERA dai mallakin gwamnatin kasar Katar ne, sannan akwai dimbin sojojin Amurka yanzu haka jibge a kasar ta Katar. ALJAZEERA tana cikin tashoshin talabijin da ake kama su ta hanyar tauraron dan Adam da ke sahun farko a duniya. |
| Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |