Almizan :Asalin rikicin Izala (1) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tattaunawa

Asalin rikicin Izala (1)


Daga Aliyu Saleh

Tun farkon kafuwar Kungiyar Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah, a tsawon rubu’in karni, Alhaji Abdulkarim Dayyabu yana da cikin na farko-farkon da suka fara shiga kungiyar a Kano. Ba ma kawai ya shiga kungiyar bane, shi ne Shugaban kungiyar na farko a jihar Kano bayan ya tsaya tsayin daka wajen kafuwar ta a Kano da suka dade suna adawo da shiga kungiyar da suka ce ta yi hannun riga da abin da gada iyaye da kakanni.

Kafin shi ma a kore shi daga kungiyar, Alhaji Abdulkarim Dayyabu cike yake da masaniyar duk wani rikici da kungiyar ta shiga a tsawon kafuwar ta. Hasali ma ta hanyarsa ne rikicin da ya taso a kungiyar a shekaru 14 da suka gabata.

A salin rikincin da ya dabaibaiye kungioyar wanda ya yi sanadiyar rabewar kungiyar gida biyu, za a iya cewa ya samo asali ne daga ranar Asabar 16/91989 bayan kammala wani taro da Kungiyar Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kira a Kano a lokacin da shi Alhaji Abdulkarim Dayyabu ne Shugaban kungiyar a Kano, inda suka yi Allah wadai da wani shirin na yin katin zama dan kasa mai alamar gicciye na kiristoci (cross) da gwamnatin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta bollo da shi, inda suka fitar da wata takardar bayan taro da aka buga a shafi na shida na jaridar AMANA ta Oktoba 1989. Ga ma abin da takardar ta kunsa:

“JAWABIN BAYAN TARO. Raddin Musulunci a kan katin da Janar Badamasi Babangida ya kaddamar a Abuja mai gicciyen kafirci wato (cross) da nufin shi ne shidar ’yan Nijeriya.

“A karshen taron na Majalisar zartawa na ranar Asabar 16/9/1989 a ofishinta na jihar, Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatuss Sunnah reshen jihar Kano, ta yi tir da Allah wadai da wannan katin mai gicciyen kafirci (croos) kamar yadda kowa zai ya gani a shafi na 14 na jaridar GUADIAN ta ranar Juma’a 4 ga Agusta 1989, wanda tuni Shugaban kasa ya fara cike nasa kamar yadda yake nufin kowanne dan Nijeriya yaro da babba mace da namiji zai cike sannan ya tabbata dan Nijeriya, inda aka rubutu Ibrahim Badamasi Babangida cikin tsakiyar ‘cross’ din daga hannun dama da kuma hotonsa daga hagu, kamar yadda yake a wannan kwafin shafin jaridar na hade da wannan takardar tamu.

“Mun lura tuni ’yan uwa musulmi sun rubuta wa Shugaba Babangida budaddiyar wasika tun ranar 25/81989 a kan wannan cin kashi da Shugaban ya yi wa Musulunci da Musulmin Nijeriya, wato ‘The Islamic Study Group of Nijeriya’ da ke a Suru Lere a can jihar Ikko, wacce aka sake bugawa a jiridar THE TRIUMPH shafin baya ta ranar Lahadi 17/9/1989.

“A hakika muna mutukar mamakin irin Musuluncin Shugaba Babangida, tatte da irin cin kashin da yake yi wa Musulunci da Musulmin kasar nan komai karacin ko raunin imanin Musulmin da ke cikin gwamnatinsa.

“A tarahin Nijeriya tun kafin zuwan Turawan mulkin-mallaka ba mu taba samun labarin wanda ta taba yi wa Musulunci da muslunmi karan tsaye da cin kashi irin wannan ba. Don haka a kokarin mu na farkar da Shugaba Babangida da gwamnatinsa tatilas, muna shaida masa mu Musulunci fa a gare mu shi ne karshe imani, matukar biyayyarmu da kowanne irin Shugaba iyakar ta yayin da wannan Shugaban yake a kan hanyar Allah (SWT), kamar yadda Shugabanmu Annabin Muhammad (SAW) ya umurce mu da mu yi wa Shugaba biyayya ko da ya kasance bakin bawa ne Bahabashe mai huje-hujen hanci, matukar ya shimfida Alkaur’ani mai tsarki da Hadisin Annabi Muhammad (SAW) a tsakaninmu.

“A yanzu haka muna ci gaba da tsamo dukkan ayoyin Alkur’ani mai tsarki da Hadisan Annabin Rahama Muhammad (SAW) wadanda suka yi bayani a kan illar ‘cross’ ga Musulmi don tunatar da dukkan ’yan uwa Musulmi da kuma gargadi ga duk raunanan Musulunci da ke cikin masu jan ragamar mulkin kasar nan da kuma sauran ’yan uwan halitta. Abokan zama na larura (kafirai) masu kokarin ta da zaune tsaye da fatan kawo karshen kowace irin yaudara da zamba a tsakaninmu.

“Muna sanar da Babangida cewa ya gaggauta soke wannan katin mai alamar ‘cross,’ ya kuma tanadi hukuncin biyan diyyar dukiyar dimbin al’ummar Musulmin kasar nan da aka lalata a kan wannan mummunan aiki ba tare da wani jinkiri ba.

“Daga karshe muna jawo hankulan manyan Malaman kasar nan da Sarakuna masu dawar Musulunci da manyan attajirai Musulmin kwarai da su gagauta fara aikinsu tun gabanin Allah bai saukar musu da azabar duniya ba kafin kuma ta lahira mai jiransu.

“Allah ya daukaka Musulunci da Musulmi, ya kuma kaskantar da kafirci da kafirai.

“A madadin masu kokarin kawar da bidi’a su tabbatar da Sunnah. Jama’atu Izalatul Bidi’a wa Ikamatul Sunnna reshen jihar Kano. Alhaji Abdulkarim Dayyabu.

Kamar yadda Alhaji Abdulkarim Dayyabu ya shaida mana a wata hira da muka yi da shi, wani abu kuma da ya kara zuzuta wutar rikicin da kungiyar ta shiga shi ne wata takarda mai shafi shida mai taken ‘Islam anda the Nijeriyan Population Policy’ da ya gabtar a Aminu Kano Community Commercial College da ke Goron Dute Kano da ke fayyace komai a kan shirin gwamnatin Babangida game da shirin kayyade iyali da kuma shirin alrurar rigakafin shan inna, ya sake fusata gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida kamar inda suka sa kafar wanda daya da kungiyar da kuma shugabanninta, inda daga karshe aka kori Abdulkarim Dayyabu daga kungiyar, bayan an shigo da wasu mutane da ya yi zargin ’yan leken asiri ne. Ga yadda hirar ta gudana:-

ASALIN KAFUWAR KUNGIYAR IZALATIL BIDI’A WA IKAMATIS SUNNAH

To, alhamdu lillahi, zan iya ba ku a takarda, kodayake da Turanci ne. Ni dai na iya tunawa kimanin shekara 10 ko fiye kafin kafuwar Izala ko bayyanar Izala a san ta har a kaddamar da ita, ni Abdulkarim Dayyabu kasancewar mun wa’azantu da karatun Shaikh Abubakar Mahmoud Gumi, Allah Ya gafarta masa, mun zo a cikin rukunin mutane mu biyar in ban mance ba daga Kano. Muka zo a fusace saboda ganin yadda abubuwa suka tabarbare a wancan lokaci.

Muka nemi izini daga gare shi, cewa muna son mu kafa kungiya ta samarin Jama’atu Nasril Islam (JNI), saboda mu rika farfado da abubuwan da aka nukurkushe, kuma mu rika kokarin zaburar da matasa irin mu da masu biye da mu. A wancan lokaci Marigayi Shaikh Abubakar Gumi ya yi mana uzuri da cewa, a’a, ba haka ya kamata ba. Idan wasu abubuwa suna tafiya ba daidai ba, a Musulunce muka ga cewa, ba ma jin dadi da wannan, ga maslaha, mu je mu sami Wazirin Kano na wancan lokaci, Marigayi Alhaji Shehu Gidado, Allah ya ji kan sa, Ya gafarta masa. Ya yi mana cikakken bayani game da shi cewa a Nijeriya ta wannan lokaci babu masani makaranci mai kyakkyawar akida fiye da shi.

Ya ce, shi kansa kasancewarsa amininsa a lokacin da gwamnatin Nijeriya ta nada shi Jakada a Saudiyya da Sudan, ’ya’yansa ya bar su ne a hannun shi Marigayi Shehu Gidado, wanda ya zama Wazirin Kano daga baya, saboda takawarsa da iliminsa, har ma yana karawa da cewa, a lokacin da aka nada shi Wazirin, da mutane suna zuwa suna yi masa murna, shi da ya je jaje ya yi masa cewa, za a raba shi da jama’a saboda ya san shi da son jama’a da son ya yi karatu tare da jama’a, amma yanzu za a kanainaye shi a sarautance, duk da cewa, sarautarsa ta karatu ce ta ilimi ce, kuma Allah Ya sauwake masa.

To, muna nan har ya yi mana waiwaye ya ce in ma muna son kari to, ga Na’ibi Sulaiman Wali, wanda yake a yanzu shi ne limamin masallacin Juma’a na Aliyu Bin Talib (Umar bin Khaddabi) a nan Kano, yana nan shi da ransa.

To, ba a dade ba, sai Allah Ya kaddara cikin shekara 10 da ’yan doriya sai aka ce ga shi an kafa kungiya ta Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunna, sai muka sake dawowa wurin Shaikh Abubakar Mahmoud Gumi, muka ce Allah Ya gafarta Malam, mu mun zo wurinka ne domin mu nemi haske kan abubuwa makamantan wannan ga uzurin da ka ba mu, amma ga wani abu ya bayyana mun ji da ruwanka a ciki. Ya ce, eh, alhamdu lillahi, yanzu lokaci ne ya yi. Saboda haka a yanzu gudummawarku tana da matukar muhimmanci ku je ku taimaka wa wannan tafiya ta yi nasara.

YADDA NA ZAMAN SHUGABAN IZALA A KANO

Ana nan ana nan, Allah da ikonSa ya kasance da ma tun kafin a yi masallaci a Jami’ar Bayero, muka kama wani gareji muke yin salla bisa wa’azantuwa da muka yi don kaurace wa bidi’o’i. Daga karshe, Allah da ikonSa, akwai bawan Allah, Shaikh Ja’afar Mahmoud Adam, Allah Ya yi masa baiwa ta karatu da karantarwa cikin hikima da basira, sai Allah Ya sa bawan Allahn nan ya matse ni da kyau, kusan duk wani abu da ya shafi wannan tafiya ta Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah, yakan ja ni a jika kwarai da gaske. Tarurruka na wa’azi za a yi, lacca ce, duk dai wani abu.

Ana nan har Allah Ya kaddara wani lokaci da muka je cikin irin wadannan tarurruka da daddare a gidan Malam Abbas Hamid, Limamin Jami’ar Bayero Kano (BUK), sai aka zo kawai kwatsam, Ja’afar Mahmoud ya ce ya bayar da sunana in zama Shugaba na riko na wannan kungiya ta Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah a cikin mutane da yawa masu ilimi masu hankali. Na yi mamaki, amma yadda suka ja hankalina sai suka yarda duk aka raba mukaman cewa, za su taimaka a gudanar da wasu abubuwa ne na wani dan lokaci.

To, ba a dade ba, sai aka yi wani gagarumin taro a nan masallacin Jami’ar Bayero, aka samu halartar dubban al’umma ’yan uwa Musulmi Ahlus Sunnah kawai bayan an soma karatu an soma nasihohi abu na gaba sai aka ce an tabbatar da shugabancin kungiyar nan ta Jama’atu Izaltil Bidi’a Wa Ikamatis Sunna (reshen jihar Kano) a kan ni Abdulkarim Dayyabu. Hujja a gare su a yadda suka bayyana babu riko a shugabanci na Musulunci. Na rasa abin da ke mini dadi, na yi mamaki, wannan ba layina bane ni dan boko ne, Malamin makaranta ne a makarantar boko, kuma dan kasuwa ne ni na yi kasuwanci har na zama Shugaban kungiyar ’yan kasuwa da masu masana’antu da ma’adinai da albarkar gona reshen Jihar Kano (Kano Chamber of Commerce, Industry, Mines And Agriculture).

Wannan (shugabanci na Izala) layi ne na hafizai na masu tafsiri na masu hadisai na masu wa’azi, amma sai aka yi mini bayani da cewa, ai shi tsarin da aka dauko na Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah, wani tsari ne irin yadda gwamnati take gudana a kasar Saudiyya, cewa akwai shugabanni na mulki (gudanarwa) masu gudanar da harkokin mulki a kasar, akwai kuma Malamai wadanda suke su suke dora duk wata harka da za a yi a kan doron Musulunci bisa koyarwar Alkur’ani da Sunnar Annabi Muhammad (SAW). Sannan akwai ’yan agaji wato mu a nan kwatankwancin sojoji masu kula da kare kowane bangare na tsaron lafiyar kasa a can.

Saboda haka, tunda sarakunan can ba su suke limanci ba, ba su suke wa’azi ba, ba su suke karantarwa ba, mulki suke yi na siyasar duniya su cakuda da kowace kasa, saboda haka irina ana bukatar mu ne mu je mu cakuda da kowa bisa wakilcin wannan kungiya a zo a ciyar da wannan kungiya gaba.

Za mu ci gana insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International