Almizan :Wadanda suka soma hana karanta hadisan Manzon Allah (S) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Wadanda suka soma hana karanta hadisan Manzon Allah (S)


Duk da cewa suna dukan kirjin cewa sune shugabannin musulmi, amma aka sami wadansu daga cikinsu suka koma kwankwadar giya a fili, da zinace-zinace, kana suke holewa, da buga ganguna, da raye-raye. Kai abubuwan suna da yawan gaske.

Idan har dabi’ar lalacewar al’ummar musulmi ta kai ga wannan matsayi, musamman a wancan lokacin, babu shakka da akwai dalilai wadanda suka haifar da haka. Wannan kuma shi ne bayanin da za mu duba a bayanan da za mu yi a gaba, tunda muna magana ne a kan Ma’asumancin Manzon Allah (SAWA).

Abu na farko da za mu soma dubawa da mayar da hankali a kai shi ne; a kan shugabannin musulmin nan, Khalifofin nan uku, Abubakar, Umar, da Uthman. Sune suka soma haramta rubutawa, da kuma bayyana hadisan Manzon Allah (SAWA).

Ya zo a cikin littafin Tadhkira Al-Huffaz, na Al-Dhahabi, juzu’i na 1, shafi na 2-3, an ruwaito cewa, Wata rana a zamanin Abubakar, ya tara mutane ya ce musu “Kuna bayyana hadisan Manzon Allah, kuma kuna bambanta da su. Mutanen da za su zo bayanku za su fi ku canzawa. Kada ku sake kawo wani zance da kuka ji daga Manzon Allah (SAWA). Duk wanda ya tambaye ku, ku ce masa, “Muna da Kur’ani a cikinmu.” Don haka, ku yi abin da na umarce ku, kuma ku kaurace wa abin da na hana ku.”

Haka nan kuma, Al-Hakim ya ruwaito a cikin littafin Mustadrak, juzu’i na 1, shafi na 110, da kuma littafin Kanzil-Umma, juzu’i na 5, shafi na 239, sun ruwaito cewa, Umar Bin Khattab ya hana mutane bayyana hadisan Manzon Allah (SAWA). Karza Bin Ka’ab ya ce: “A lokacin Umar Bin Khattab ya aike mu Iraki, ya biyo bayanmu, kuma ya ce mana ‘kun san abin da ya sa na biyo ku?’ Muka amsa masa da cewa, ba mu sani ba. Sai ya ce…. ‘Bayan haka kuma, kun san za ku je ga mutanen kauyuka ne, wadanda Kur’ani ke kewaye da su, kamar yadda zuma take kewaye duk abin da ta sauka a kai. Don haka, kada ku yarda ku gaya musu hadisan Manzon Allah (SAWA). Ku sa su himmatu da karanta Kur’ani kawai, kuma ku rage yawan gaya musu zantukan Manzon Allah (SAWA). Ni ma ina tare da ku a kan haka.”

Karza ya ci gaba da cewa: “tun daga wannan lokacin da Umar ya hana ni bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA), ban sake furta su ba.” Ya zo a cikin littafin Ibn Majah, juzu’i na 1, shafi na 12, da kuma cikin littafin Al-Dirimi, juzu’i na 1, shafi na 85, da kuma cikin littafin Tadhkira Al-Huffaz, na Al-Dhahabi, juzu’i na 1, cewa, “a lokacin da Karza ya je Iraki, mutane suka yi ta tambayar sa a kan hadisai, shi kuma yakan gaya musu cewa, Umar ya hana a bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA).”

Haka nan kuma a cikin littafin Mustadrak na Al-Hakim, juzu’i na 1 shafi na 110, da littafin Kanzul-Umma, juzu’i na 5, shafi na 239, an ruwaito cewa, Abdulrahman Bin Awf, ya ce, Umar Bin Khattab ya taba tara Sahabban Manzon Allah (SAWA), daga yankunan kauyuka domin ya haramta masu bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA) ga mutane. Da suka taru, sai Umar ya ce musu; “ku tsaya a kan abin da na ce muku (na rashin bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA) matukar ina raye.” Ba su kuma rabu da shi ba sai da ya mutu.

Su ma Al-Khattab Baghdadi, da kuma Al-Dhahabi, a cikin littafin Tadhkira Al-Huffaz, sun ruwaito cewa, Umar Bin Khattab ya taba saka mutane uku a cikin gidan fursuna saboda yawan ruwaito Hadisan Manzon Allah (SAWA) da suke yi. Wadannan mutane sune: Abu Darda, Ibn Mas’ud, da kuma Abu Mas’ud Al-Ansari.

Haka nan kuma, a cikin littafin Tabaqat Kubrah, na Ib Sa’ad, juzu’i na 5, shafi na 140, da kuma littafin Taqdim Al-Ilm, na Baghdadi, sun ruwaito cewa; da akwai lokacin da Umar Bin Khattab a zamaninsa ya umurci Sahabbai da kowannensu ya kawo tarin Hadisan da yake da su a ajiye. Su a tsammaninsu Umar yana so ne a hada wadannan hadisai a wuri daya, don haka kowa ya je ya kawo nasa. Amma abin mamaki, bayan sun kawo masa, sai ya hada su gaba daya ya cinna musu wuta.

Bayan Umar Bin Khattab, a lokacin Uthman Bin Affan ma, shi ma ya kawo nasa salon na hana bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA). Ya zo a cikin sharhin Muntakhab, daga cikin littafin Kanzul-Umma, da kuma a cikin littafin Musnad na Imam Hambal cewa; Uthman Bin Affan ya tara Sahabbai da sauran jama’a a lokacinsa ya ce masu: “Ba mu amince wani ya kawo wani sabon Hadisi na Manzon Allah (SAWA) ba, wanda ba mu san shi a lokacin Umar da Abubakar ba.”

Haka nan kuma, a cikin littafin Al-Khatib na Al-Baghadadi, da littafin Sharaf Al-Hadith, shafi na 91, an ruwaito cewa, a lokacin da Mu’awiya dan Abu Sufyanu ya zama Shugaban musulmi, ya tara jama’a, ya hau kan mumbari ya ce: “Na haramta wa kowa gabatar da wani sabon Hadisi, sai wadanda muka sani a lokacin Umar.”

Ko shakka babu, da akwai wata makarkashiya da ya sa aka haramta bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA), da kuma bayyana wadanda ba a riga an bayyana su ba. Wannan ya faru ne domin da akwai Hadisai da yawa, da suka soki irin abubuwan da wadannan mutane suke yi a wancan lokacin. Idan ba haka ba, me ya sa aka haramta furtawa, da bayyana irin wadannan hadisan a duk tsawon zamunnansu, har sai a zamanin Umar Bin AbdulAziz (RA)?

Babu shakka, haramtawa da hana bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA) da su Abubakar da Umar suka yi yana da nasaba da maganar Khalifanci, saboda Manzon Allah (SAWA) ya bayyana wanda zai zama Khalifansa bayan ya yi wafati, kuma a gaban dubban musulmi. A saboda wannan dalili ya sa suka haramta yada irin wadannan hadisai zuwa ga sauran lardunan Larabawa. Wannan ya tabbatar da cewa ba sune Khalifofin Manzon Allah ba (SAWA), sai dai sune suka haye kan Khalifancin a bisa Ali Bin Talib, wanda Manzon Allah (SAWA) ya Khalifanta.

Wani abin mamaki dangane da Umar Bin Khattab shi ne, matsayin da ya dauka dangane da al’amarin Khalifanci, domin dukkanin matsayan da ya dauka suna karo da juna. Domin shi ne ya umurci jama’a da su yi wa Abubakar mubayi’a, har kuma wadanda suka ki yarda su yi mubayi’ar ya yi musu barazana. Shi ne kuma ya ce wannan zabe da suka yi wa Abubakar wani al’amari ne daga Allah, domin ya kange al’umma daga fadawa cikin rikici. Haka nan kuma, shi ne ya tsayar da mutum shida domin su yi takarar Khalifanci, har yana cewa: “Idan wannan mutumin mai tsanantawa (yana nufin Ali Bin Abi Talib) ya zama Khalifa, zai takura mana a kan addini.”

Abin tambaya a nan shi ne: Tun da har Umar Bin Khattaba ya san cewa Ali Bin Abi Talib, shi ne zai daidaita sahun al’ummar musulmi, me ya sa bai gaya wa al’umma gaskiya su zabe shi ba (tunda sun ce zabe suke yi)? Amma maimakon haka, sai maganganunsa da matsayan da ya rika dauka suka rika karo da juna. Sai kuma daga baya ya sake karkata ga ra’ayin da Abdulrahman Bin Awf ya gabatar, har kuma yake cewa “Da a ce Salim bawan Abu Hudhayfa yana raye, da kuwa shi zan nada ya jagorance ku.” Wannan ruwaya ta sama, Abu Hanifa ya kawo ta, wanda ke cewa za a iya nada ’yantaccen bawa a matsayin Khalifanci: Wannan ruwaya ta yi karo da Hadisin Manzon Allah ingantacce, wanda ya ce “Khalifanci na tare da Kuraishawa.” Saboda wannan dalilin ne ya sa Turkawa suka fito da Mazhabar Abu Hanifa, a lokacin da aka sami Khalifa daga cikinsu, kuma suka bai wa Abu Hanifa matsayin Shugaban masu Mazhabar.

Wani abin mamaki kuma da Umar Bin Khattab ya aikata shi ne, yadda ya hana Abu Hafs bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA), kuma su ma sauran Sahabban da ke Madina ya yi musu wannan hanin. Haka nan kuma, wakilansa da ya tura larduna daban-daban su ma ya ja kunnuwansu cewa, kada wanda ya kuskura ya furta wani hadisi ga mutanen da aka tura shi gare su. Ya kuma amshe Hadisan da suke hannun Sahabbai ya kona.

Tambaya a nan ita ce; an manta ne cewa Hadisan Manzon Allah (SAWA) sune suke fassara Alkur’ani? Ko kuma an manta ayar Alkur’ani ne wadda take cewa; “MUN SAUKAR DA AMBATO (KUR’ANI) DOMIN KA YI BAYANI A KAN ABIN DA MUKA SAUKAR A GARE SU (16:44). Ko kuma an fi wanda aka saukar wa ambaton sanin yadda fassarar Kur’ani take ne?

Wannan al’amari ne yake rudar da mutane da yawa, har suke yin tatsuniyar cewa wai wani lokaci ayoyin Alkur’ani kan sauka, kuma su gaskata maganar Umar, sannan su yi jayayya da maganar Manzon Allah (SAWA).

Hakika jikina ya yi sanyi a lokacin da na karanta a cikin littafin Sahih Bukhari, yadda Umar ya ki yarda da Hadisan da Ammar Bin Yassir ya ruwaito, musamman a kan hadisin da ya yi bayanin yadda ake yin taimama. Kuma na yi mamakin kalmomin da shi Ammar ya gaya wa Umar, inda ya ce masa; “Idan ka ce na yi shiru, shi kenan ba zan sake bayyana wannan hadisin ba.” Ammar ya fadi haka ne ba domin komai ba, sai saboda tsoron Umar. Wannan kuma ya sake nuna mana yadda Umar ya kasance mai tsanani a kan duk wanda ya bayyana Hadisan Manzon Allah a wancan lokacin.

Abin lura a nan shi ne, idan Sahabbai Kuraishawa suna tsoron Umar a lokacin, kuma suka kasa barin Madina, sannan wadanda suka kaurace wa Madina su ma sun kaurace wa bayyana Hadisan Manzon Allah (S), haka nan kuma duk an kona hadisan da aka tattara, amma a cikinsu babu wanda ya iya fitowa, ya nuna rashin yardarsa. A saboda haka, ya kuke ganin matsayar da Ammar Bin Yassir ya dauka, a matsayinsa na bako a cikinsu, wanda saboda kauna da kuma matsayan da ya dauka a kan Ali Bin Abi Talib duk suka kyamace shi?

Bari mu koma baya kadan a kan abin da muke tattaunawa a baya, musamman kan abin da ya faru a ranar Alhamis, kafin wafatin Manzon Allah (SAWA). Rana ce wadda Ibn Abbas ya kira ”Ranar Tashin Hankali.” A wannan rana ce Manzon Allah (SAWA) ya umurci Sahabban da suke tare da shi, kuma suka zagaye shi, ya ce su kawo masa takarda da abin rubutu domin zai rubuta musu abin da idan suka bi ba za su taba karkacewa daga gaskiya ba. A wannan rana ce, Umar Bin Khattab ya kalubalanci Manzon Allah (SAWA), yake cewa; “Manzon Allah ba ya cikin hayyacinsa,” (Wa’iyazu Billahi). Kuma Umar ya sake cewa “Muna neman tsarin Allah. Mu littafin Allah (Alkur’ani) ya ishe mu.” Wannan al’amari da ya faru Malaman Ahlus Sunna, irin su Bukhari, Muslim, Ibn Majah, Al-Nisa’i, Abu Dawud, da Imam Ahmad, duk sun kawo shi...

Za mu ci gana insha Allah

Hausa da Hausanci a karni na 21: Kalubale da madosa (2)

Abdalla Uba Adamu (auadamu@gmail.com)

Ci gaba daga makon jiya

DABI’A, TADA (GARGAJIYA) DA KUMA AL’ADAR BAHAUSHE

Sau tari in an yi maganar “al’adar Bahaushe” ana maganar dabi’u da tadar Bahaushe ne. Babban abin da ke kawo wannan muhawarar shi ne ganin yadda kusan duk nazarin da ake yi wa Hausawa, ana yi ne daga turbar harshe, ba daga turbar mu’amala da tarbiyya ba.

Wannan ya saba da yadda manazartar rayuwar al’umma ke nazarin sauran al’ummatan. Kuma kasancewar masu nazarin Hausawa na farko-farko sun yi daga wannan kusurwar ta nazarin harshe, sai aka ci gaba da wannan turbar. Ina mai fatan bude wata hanyar nazarin rayuwar Bahaushe a bisa alkiblar nazarin rayuwar dan Adam, ba kawai ta harshe ba.

Hanya ta farko ta barin waccan kusurwar nazarin ita ce bambanta dabi’ar Hausawa, tada (ko gargajiyar) Hausawa, da kuma al’adar Hausawa. Wadannan rukunayen rayuwa dole a bambanta su kamar yadda masu nazarin salsalar al’umma (Anthropologists) suke yi wa sauran al’ummatan. Domin a samu kyakkyawar fahimta. Dabi’a dai ita ce, ‘social behavior;’ tada ko gargajiya kuma, ‘customs and traditions;’ sannan al’ada kuma ‘mores and midsets.’

A bisa wannan ma’aunin, dabi’a tana nufin; yanayin zaman mutum, tada da gargajiya kuma na nufin; yanayin da aka gada kaka da kakanni, wanda zai iya bambanta da yanayin zaman mutum a yanzu, ko kuma halin da mutum ya samu kansa. Al’ada kuma tana nufin; sinadarin mu’amalar mutum, ko kuma; tarbiyyarsa. Al’ada a gaba take da dabi’a, kuma za ta iya jagoranta. Idan an ce mutum ba shi da al’ada mai kyau, ana nufin ba shi da tarbiyya mai kyau, domin al’adar ko tarbiyyar sune suke gina shi a kan fasalin mutumin kirki, ko kuma “dan asali.”

Za a iya aron dabi’a da ma gargajiya, amma ba za a iya aron al’ada ba, domin ita al’ada tana tattare da ruhin mai ita; bayan dabi’a kuwa takan canza bisa yadda yanayin zama ya kama; kai har ma aron ta ake yi, amma ba za a taba aron al’ada ba. Saboda haka za a iya aron abubuwan sarrafa dabi’a, a gyara su, a canza su, in kuma an gaji da su a zubar da su. Amma ba a aron al’ada, domin ita al’ada tana like ne da ruhin mai ita a matsayin sinadari. A duk inda ake nazarin zamantakewar Bahaushe, dole sai ka ji ana ta cakuda wadannan rukunayen zaman mutum -- dabi’a, tada, da kuma al’ada.- Wani lokaci in an ce al’ada, to ana nufin dabi’a; sannan kuma in an yi maganar dabi’a, sai ka ji lalle ba al’ada ake magana ba, ana maganar tada ne. Ya zama wajibi a bambanta kowanne da kawo bayanai da hujjoji domin su tallafa wa bayanin.

DABI’A DA ZAMANANCIN BAHAUSHE

Duk da ana ganin kamar Bahaushe Bagidaje ne, ba na jin akwai kabilar da ta fi Bahaushe rungumar zamanin da ya sami kansa. Wannan ba zai zama abin mamaki ba, domin kasar Hausa dadaddiyar matattara al’ummatai ce. Su kansu Hausawan ba mazauna ne ba, akwai su da yawon kasuwanci da fatauci. Ta haka sukan ci karo da abubuwa baki da yawa, daga yare da are-aren kalmomi, zuwa ire-iren abinci da kuma tufafi, kai har da ma sigar gine-gine. A duk lokacin da Bahaushe ya ci karo da wani abu sabo, nan da nan yake karbarsa, in har ya yi daidai da abin da ya saba da shi. Idan kuwa bai daidaita sahu da rayuwarsa ba, to bijire masa yake yi, komai kyaunsa. A bisa wannan tarihi na Bahaushe, babu wanda ya fi Bahaushe karbar zamani.

Ta wannan hanyar, da yawa daga cikin abubuwan da muke amfani da su, wadanda ake ganin kamar aro ne, duk na sarrafa dabi’a ne, kuma da yawa na aron ne. Misali, Bahaushe bai san ya yi gini da kusurwa hudu ba, sai da ya hadu da Larabawa. Kafin wannan lokacin Bahaushe bai san tubali ba, a wajen Larabawan ya gani. Amma ya karbi gini da tubali, daga baya da sauyin zamani ya zo, yake amfani da bulo, da farko da na kasa, daga baya ya koma na siminti. Wannan canjin yana nuna canjin dabi’ar Bahaushe ta gini, wanda dama da aro ya fara shi.

Haka kafin haduwar Bahaushe da Larabawa, abincinsa kusan kayyadadde ne – dambu, tuwo, zogale, dan wake, da sauransu.- Haduwarsa da Larabawa sai ya canza dabi’ar cin abincinsa, ya fara cin gurasa, alkubus, algaragis, da sauransu. Yau in ya ce ya daina cin dambu – ra’ayi ne, ba Hausanci ba, domin takan yiwu a haifi Bahaushe a kasar da babu dambu, ko kuma kayan sarrafa shi, kamar a ce Australiya – shi kenan kuma sai a ce ba Bahaushe bane don ba ya cin dambu?

Sannan kuma babban abin da ya kawo ake ganin kamar ma babu wata kabila Hausawa, kuma Hausanci ai yare ne, ba wani abu bane illa ganin yadda tabbas kam Bahaushe na da saurin aron abubuwa. Kusan duk abin da aka ga Bahaushe ya ara, to ya yi ne a matsayin makami domin hulda da wadanda ya ara daga wajensu; kuma in abin bai yi masa ba, zubar da shi zai yi; in kuma ya yi masa, zai narkar da shi ya zama nasa, ta yadda ko shi kansa wanda ya bai wa Bahaushe aron abin, ba zai iya gane shi ba. Amma duk abin da ya ara, abin sarrafawa ne – daga tufafi, zuwa dabarun dafa abinci, zuwa ire-iren abinci, kama zuwa kalmomi. Duk wadannan an aro su, ana kuma amfani da su, kuma in ba su dace da al’ada ba, to zubar da su ake yi ta yin Allah-wadai da su.

Babu inda Bahaushe ya nuna gwanintarsa ta aron abubuwa suka zama masarrafai gare shi kamar harshe. Bincike ya nuna cewa har ya zuwa 1960 kusan kashi 20 daga 100 na kalmomin Hausa da Fulatanci daga Larabci suke. Sannan kuma daga 1960 zuwa yanzu, an samu karin wadansu kalmomin da Bahaushe ya ara a cikin Larabci yadda abin zai kai kusan kashi 40 ko fiye daga cikin 100 daga kalmomin da aka ara.

Sannan sauran yararraki sun shigo cikin Hausa sosai ta yadda Bahaushe ya ari abubuwansu ya mayar nasa. Amma kusan duk abin da aka ga Bahaushe ya ara, to kamar yadda na ce, abin sarrafawa ne, ba tsarin mu’amala ba. Misalai daga cikin yararrakin da Bahaushe ya ci karo da su, sannan kuma ya ari kalmominsu sun hada da Azbinanci, Fullatanci, Barbanci, da Nufanci. Ga jadawalin da ya nuna misalai daga cikin wadannan are-aren kalmomin daga wadansu yararrakin cikin Hausa:

Jadawali na 1: Are-Aren kalmomi a Cikin Hausa

Shi kansa Turanci da ake ganin kamar yaren wadansu kebabbu ne, bai samu ci gaba ba sai da ya ari kalmomi da yawa daga cikin yaren al’ummatan da Turawa suke hulda da su; domin Turawa, kamar Hausawa, ba zaune suke ba, akwai su da yawo da kuma karbar sabon abu. Misali daga cikin al’ummatan da Turawa suka ari kalmominsu domin gina Turanci na jadawali na kasa.

Jadawali na 2: Are-Aren Cikin Turanci.

Saboda haka ashe aro ba wani bakon abu bane a cikin dabi’ar Bahaushe, kuma tunda aron da yake yi yana tafiya da yadda ya samu kansa, dole a yarda Bahaushe na tafiya da zamani, ba wai bagidaje ne ba. Misali, cin abinci da hannun hagu da cokali mai yatsu, dabi’ar Banasare ce. Cin abinci da tsinkaye guda biyu dabi’ar Canis ce. Duk wadannan da kyar za ka raba su da wadannan dabi’un. Amma zaman Bahaushe a Hon Kong zai iya sa ya ari dabi’ar cin abinci da tsinkaye, domin yana ganin zai iya, ko kuma yana sha’awa. Wannan ba zai sa ya zama Canis ba, amma za a iya cewa ya bar tasa dabi’ar (ta cin abinci da hannu, domin ko cin abinci da cokali ma ba dabi’ar Bahaushe bace, don cokalin aro shi ya yi daga wajen Azbinawa), ya ari ta Canis, domin a wannan aron, babu yadda zai nasabanta shi da rayuwarsa. Amma kuma a wani misalin, babbar riga ba tufafin Bahaushe bane, amma yanzu babu Bahaushen da zai yarda babbar riga ba tasa ba ce, saboda yadda ta dace da tsarin dabi’ar rayuwarsa.

TADA KO GARGAJIYA DA ZAMANANCIN BAHAUSHE

Tada, gargajiya, ko kuma customs and practices, tsare-tsaren rayuwar Bahaushe ne da ya gada kaka da kakanni. Da Musulunci ya zo, sai ya kawar da wadansu, kamar tsafi da bautar gumaka, da shan giya da zina, da sauransu, ya kuma kyale wadansu domin ba su yi karo da addini ba, kamar tsare-tsaren haihuwa da sauran bukukuwan da suka hada da haihuwa. Duk da cewa rayuwa wacce aka gada shekara da shekaru, ba dole ne mutum ya yarda da ita ba, domin akwai ra’ayi a wajen inganta tada. Misali, matan Turawa ba sa wankan jego. Wannan sai matan Hausawa. Amma shi ma yanayi ne da kuma ra’ayi. Bahaushiyar da ke zaune a Ingila ba za ta yi wankan jego ba, domin yin haka zai keta ka’idar kiwon lafiyar dan Adam a kasar. Saboda haka idan wannan Bahaushiyar ta ce ba za ta yi wankan jego ba, ba wai ta yar da tadarta bane, kawai yanayin zamanta ba zai kyale ta ta ci gaba da wannan tadar bane. Sannan wadansu matan ba su da karfin halin da za su dinga shekawa kansu ruwan zafi, ko saboda rashin lafiya ba za su iya wannan wankan jegon ba. Wannan ba zai fitar da su daga rukunin Hausawa ba, domin haka abin ya dauro musu.

Duk da haka, wadannan tadodin su ma an yi musu kwaskwarima, tare da hadowa da na wadansu al’ummatan, a shigar da su cikin Hausa. Misali, matar da ta yi haihuwar fari tana zuwa gidansu ta ci gaba da wankan jego daga ranar suna ne. Amma Hausawa sun ari tadar Fulani ta wannan fannin na tafiya gida goyon ciki daga ciki na wata bakwai.

Yin haka ya yi daidai, domin abin duk za a ce kana da zabi a kai, ko dabi’a, ko tada, to kana da hakkin juya shi ta yadda za ka iya aiwatar da shi ta yadda kake so, ko da ya batar da surarsa ta ainihi, to dalilin yin sa na nan. Misali, kaurin jego na daga cikin tadodin Hausawa. A surarsa ta farko da kafafuwan sa ake yi, a yi ganda, sannan a hada da kunun kanwa a aikawa makwabta da abokan arziki. Da tafiya ta yi tafiya, sai wannan ya canza, aka koma yi da naman karamar dabba, daga baya aka koma yin dabino da kuma alewa. Sigar ta canza, amma makasudin, ko kuma manufar yin kaurin, ba ta canza ba.

Saboda haka in akwai wata tada da ta saba wa Musulunci, to wannan bai kamata a daukaka ta ba. In kuwa ba ta saba wa Musulunci ba, to in dai za ta amfani jama’a, ko ta samar da aiki, ko karfafa zumunci, a iya daukaka ta, ko da an canza mata siga ne. A wannan, tadodin Bahaushe sun hada da tsare-tsaren rayuwarsa daga haihuwa zuwa aure, zuwa mutuwa. Kowace kabila a duniya tana da abin da ta tanada na sarrafa wadannan nau’o’in na rayuwa.

Za mu ci insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International