Almizan :'Yan sanda sun harbe wani magidanci a Kano ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426                 Bugu na 694                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

'Yan sanda sun harbe wani magidanci a Kano


Daga Ali Kakaki

A ranar Litinin din da ta gabata ’yan sanda da ke aikin dare a ofishin ’yan sanda na unguwar Shagari Quarters da ke Karamar Hukumar Kumbotso a cikin jihar Kano suka

harbe wani bawan Allah, Malam Salisu Gambo (Majazubi) har lahira babu laifin fari balle na baki.

Yadda abin ya faru shi ne; shi dai Salisu Gambo mutum ne ma’abocin zikiri (Ambaton Allah), yana tsarkake zuciyarsa da su, har a wani lokaci a baya ya samu kansa

a wani yanayi na ‘Jazbah’ kamar tabin hankali har ya kasance sai da aka kai shi asibitin mahaukata na Goron Dutse ya rinka karbar magani yana sha.

Sai kawai a ranar Litinin din da ta gabata, Malam Salisu Gambo ya sake fadawa cikin wannan hali na ‘Jazbah.’ Da misalin karfe uku na dare ya fita daga gidansa a cikin irin wannan hali ya nufi ofishin ’yan sanda na Shagari Quarters. Yana zuwa a cikin wannan halin na zikiri rike da Alkur’aninsa a hannu da tazbaha, sai kawai ’yan sandan da ke aiki a wannan daren suka yi masa tsawa, ya ki ya bari, sai kawai suka bude masa wuta, nan take ya fadi. Bayan ya mutu ne suka kai shi dakin ajiye gawa na asibitin Murtala Muhammad suka ajiye shi.

’Yan uwan Marigayin sun samu labarin rasuwar dan uwan nasu ne ta bakin wasu wadanda aka saka a sel a safiyar wannan ranar. Kawo gawar Marigayin cikin unguwar ta

Shagari ya ta da hankalin jama’a kwarai da gaske, inda wasu gungun matasa kimanin 2000 suka harzuka suka nemi kai hari ofishin ’yan sandan, sai da ofishin ya samu taimakon ’yan sanda kimanin motoci guda tara suna gadinsa.

ALMIZAN ta halarci suturar Marigayin a gaban gidansa da ke Unguwar Ja’oji. Bayan kammala suturar tasa ne kanin Marigayin mai suna Alhaji Hamisu Gambo, wanda da ganin sa ka san yana cikin bakin ciki da tashin hankali na rasuwar dan uwan nasa, ya shaida wa ALMIZAN cewa gaskiya Salisu yana da tabin hankali. Su kansu wasu daga cikin ’yan sandan sun san shi, kuma sun san yana da tabin hankali domin yakan je ofishinsu su yi wasa da dariya da shi, amma suka kashe shi ta hanyar harbi har sau uku a jikinsa.

Shi kuwa Rufa’i Ahmad, wanda ya ga Marigayin kafin a harbe shi, ya ce wajen karfe uku na dare ne ya ga Malam Salisu ya fito yana salati da tazbaha da Alkur’ani da

kuma Dala’ilu a hannunsa ya yi wajen ofishin ’yan sanda. “Sai dai kawai muka ji wai an kashe shi.

Mutane da dama a yankin unguwar Shagari Quarters sun koka kwarai kan yadda ’yan sandan yankin suke kashe jama’a, inda a cikin shekara daya suka kashe mutane

biyu, don a waccan shekarar, ana gobe salla, a wani gida da yake kallon gidansu Marigayi Salisu, wata mata da abokan hayarta suna wankin salla, sai suka dan watsawa motarta ruwan wanki, sai ta kira musu ’yan sanda. Koda suka je ofishinsu sai suka yi ta dukan wani Malam Dauda da kulki a ka har sai da ya mutu.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International