
Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426
Bugu na 694
| Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Malam Turi ya ziyarci Shehunnan Malamai a Kano
A kokarinsa na ganin kan al’ummar musulmi ya hadu sun zama abu guda ta hanyar kusantar juna da sada zumunci, Malam Muhammad Mahmud Turi, Wakilin Shaikh Ibraheem Zakzaky a Kano, ya ziyarci wasu Shehunan Malamai wadanda suka hada da gidan Kadiriyya, yayin rufe karatun Ashafa na bana da kuma Shaikh Isah Waziri, Wazirin Kano, da Shaikh Idris Kuliya, babban Limamin Kano. Malam Muhammad Turi, yayin da ya ziyarci gidan na Kadiriyya, ya samu kyakkyawan tarbo da nuna matukar farin ciki daga Khalifa Karibullah da ’yan uwansa da sauran mabiyan Darikar ta Kadiriyya. Shi kuwa Shaikh Isah Waziri, Malam Turi ya ziyarce shi ne ranar Juma’a ta farko bayan sallar Edil-Fitr a gidansa da ke unguwar Tudun Wazirci a cikin birnin Kano. Kuma a karo na uku ya ziyarci Shaikh Aliyu Harazumi da Shaikh Idris Kuliya, babban Limamin Kano. A yayin ziyarce-ziyarcen, Malam Muhammad Turi ya rika bayyana ziyarar tasa da cewa a madadin Harka Islamiyya da ’yan uwa musulmi ya yi domin cika umurnin Allah (SWA) da Manzo Muhammad (SAW) cewa; Mumunai ’yan uwan juna ne, a wani wurin kuma yake cewa su kasance abu guda kada su rarraba. Wakilinmu ya shaida mana cewa irin wannan ziyara da Malam Turi yake kai wa ya biyo bayan Bikin Makon Hadin Kai da Shaikh Zakzaky ya fara shiryawa a kasar nan ne a cikin watan Rabi’ul Awwal (Maulud). |
| | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |