
Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426
Bugu na 694
| Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
Amurka ta soma tunanin ficewa daga Iraki |
|
|
A wani jawabi da ya yi game da halin da ake cikin a kan yakin na Iraki a ‘US Naval Academy,’ Shugaban Amurka, George W. Bush ya ambata cewa nan da wani lokaci za su fara tunanin janye wani bangare na sojansu da suke jibge a Iraki.
Wannan jawabin na Bush ya zo ne makonni biyu kafin zaben ’yan Majalisar dokoki da za a yi a Iraki, kuma ya yi wannan jawabin ne a daidai lokacin da masu gwagwarmyar korar Amurkan daga Iraki suka kara zage damtse wajen kai hare-hare ba kakkautawa.
George W. Bush ya ce, za su fita da Iraki ne domin kammala abin da ya kai su, amma ba don matsin lambari da ake yi masu ba. Kuma ko kusa ba za su fita su bar ladansu ba a Iraki ba, don kuwa ba yadda za a yi su fice daga kasar sai sun karyar lagon ’yan ta’adda.
“Yanzu haka dakarun tsaron Iraki da muka horar sun fara tsayawa da dugadugansu. Don haka duk lokacin da burinmu na fatattakar ’yan ta’ada daga Iraki ya kawo karshe, dakarunmu za su dawo gida da alfaharin ’yan kasa,” in ji Shugaba Bush.
Ya ce, “idan nasarar da muke samu a wannan ja-in-ja da muke yi tsakaninmu da ’yan ta’adda kawo yau ta ci gaba a haka, muna ci gaba da ganin nasara, za mu dawo da dakarunmu gida a 2006. Sai dai kamar yadda bayanan da fadar ‘White House’ take da shi yake nunawa za a dauki lokaci kafin a kai ga wanann nasarar da muke nema.”
Shugaban Amurka Bush, wanda a baya ya yi dagewa a kan ba zai bayyana ranar ko lokacin da zai dawo da dakarunsa gida ba, ya ce, “za mu ci gaba da rarakar ’yan ta’adda a duk inda suke a duniya. Za mu ci gaba da matsa kaimi a kan abokan gabarmu a duk inda suka buya. Muna kara matse su (’yan ta’adda) a Iraki, muna rage adadinsu da kuma lalata maboyarsu da suke amfani da ita wajen yi wa duniya barazana.”
Ya ce, “nasara na kara samuwa a daidai lokacin da ’yan ta’adda da kuma madugunsu da ke Iraki, (Saddam Husani) suke ta shiga hannu, ga kuma mulkin dimokradiyya da ’yanci suna ta ci gaba da samun gindin zama a Iraki. Dakarun tsaron Iraki kuma suna ta samun karin kwarewa wajen cin dunun ’yan ta’adda. Idan har ba a kakkabe dukan gyauron ’yan ta’addan da ke Iraki ba, muka yi gangancin janye dakarunmu duniya na cikin hadarin fuskantar karin hare-haren ta’addanci.”
Bush ya ci gaba da cewa, “kodayake babban burinmu a Iraki shi ne fatattakar ’yan ta’adda, amma muna fatan horar da dakarun Irakin da za su yake su da kansu. Sai dai kuma wannan zai dauki lokaci mai tsawo da kuma dauriya da karin hakuri.”
A yayin da George W. Bush yake wannan jawabin kuma, sai ga shi wasu mutane sun kai wani hari a garin Bakuba, inda har mutane 10 da suka hada da wasu fararen hula tara suka rasu, tare da jikkata wasu guda biyu.
George W. Bush dai yana fuskantar matsin lamba a gida da waje dangane da wannan yakin da ya kaddamar a Iraki a cikin watan Maris na 2003 ba tare da amincewar duniya ba.
Bush ya ce, idan har sun kammala aikin da ya kai su Iraki ba za su tsaya suna boye ranar da za su bar kasar ba. “tilas mu daraja lokaci, dole mu daraja kokarin dakarunmu,” in ji shi.
Duk da yake ya kwashe lokaci mai tsawo yana jawabi a kan Iraki, amma wannan shi ne wani sako da ya fito daga fadar ‘White House’ da ya je kunnan Irakawa, Amurkawa da kuma sauran mutane duniya da suke adawa da yakin da ake yi a Irakin, tun bayan mamaye kasar da suka yi a Maris 2003.
A makonni biyu da suka gabata dai sama da Irakawa 200 ne suka rasa rayukansu a hare-haren konar bakin wake daban-daban da aka kai, mafi yawan hare-haren ya rutsa ne da Shi’awa ne, abin da wasa suka bayyana shi da neman jefa kasar a cikin basasa. Wannan adadin shi ya mai da adadin rayukan faren hular da suka rasu a wanann yakin ya haura dubu 120.
Wannan jawabin na Bush ya zo ne daidai lokacin da wani babban jami’in tsaron Iraki ya yi kira ga Washington da ta janye sojan mamaya na Amurka 155,000 da suke Irakin. Yanzu dai an yarda za a soma janye sojan na Amurka 30,000 nan da shekara mai zuwa.
Sama da sojan mamaya na Amurka 2,200 ne dai aka kashe, yayin da aka jikkata sama da 16,000, a wannan yakin da aka kaddamar da shi da sunan neman makaman kare dangi da tsohon Shugaban kasar Saddam Husani ya mallaka, sai dai bayan tsawon lokaci sun bayyana cewa babu wannan makamin.
| | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |