Almizan :Me ya jawo boren da fursunoni suka yi a Sakkwato? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426                 Bugu na 694                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Me ya jawo boren da fursunoni suka yi a Sakkwato?

Daga Abu Sumayya

A ranar Lahadi 20, ga watan Nuwamba 2005 ne fursunoni a gidan yarin Sakkwato suka tayar da bore a daidai lokacin da Shugaban gwamnatin farar hula ta Nijeriya, Cif Olushegun Obasanjo yake ziyara ta kwanaki biyu.


Boren, wanda mafi yawan masu yin sa fursunoni ne masu jiran shari’a da ake zargi da laifukan fashi da makami, da kuma kisan kai, ya jawo rasa ran mutane uku, lalata dukiya da kuma ji wa da dama rauni.

Shi dai wannan boren an fara shi ne da misalin karfe 7:00 na marecen wannan

ranar. Bayan fara wannan boren ne kuma ’yan sanda, tare da ma’aikatan gidan yarin suka zagaye gidan suna luguden barkonon tsohuwa tun karfe 7 na yamma har zuwa karfe 1:00 na dare ba tare da sun iya samun nasarar kwantar da tarzomar ba. Daga nan ne fa sai wasu fursunoni suka shiga kunnawa wasu wurare wuta, kamar shagon koyon dinki, wasu ofisoshi da kuma dakin ajiyar abinci, inda suka fasa shi suna kwasar abinci zuwa

dakunansu.

Ganin yadda wutar boren ke kara karfi ne ya sanya aka bai wa ’yan sandan kwantar da tarzoma izinin shiga cikin gidan yarin, inda suka rika luguden harsashe har na

tsawon kusan awa daya kafin a karshe su iya samun nasarar kwantar da boren.

A bangaren ’yan uwa musulmi da ake tsare da su a cikin wannan gidan yarin da yawansu ya kai mutum 70, sun samu yabo da sanya albarka daga ma’aikatan gidan, da kuma wasu fursunonin, ganin yadda ’yan uwa suka taru a daki daya suka rinka yin zikiri a daidai lokacin da ake wannan boren ba tare da sun fito ko da daga dakin da suke ba.

Wannan yabon ya kara fitowa fili ne a kashegarin ranar da aka yi boren lokacin da Kwamishinan ’yan sanda da Shugaban SSS da Shugaban gidan yarin, tare da wasu manyan ma’aikatan tsaro suka shiga a cikin gidan yarin suna zagayawa a kowane daki domin zakulo wadanda ake ganin suna da hannu a wannan boren da aka yi.

A lokacin da suka zo dakin da ’yan uwa suke, sai Shugaban gidan yarin ya ce, “a wuce wadannan, banda su a ciki. Allah ya yi maku albarka, kun nuna tabbas ku addini kuke yi. Mun gode maku kwarai.”

Bakuna dai sun rarrabu a kan musabbabin tayar da wannan boren. A bangaren jama’ar gari suna ganin cewa wannan wata makarkashiya ce wadansu suka hada ta hanyar yin amfani da fursunoni domin janyo wa Gwamna Bafarawa bakin jini ga sauran ’yan Najeriya. Yayin da bangaren fursunoni kuwa suke cewa sun yi wannan boren ne domin su nuna bacin ransu ga irin yadda ake tsare da su shekaru shida zuwa goma ba tare da an yanke masu hukunci ba. Suna kuma zargin cewa ba a ba su abinci kamar yadda doka ta tanada. Sannan suna zargin ma’aikatan gidan yarin na Sakkwato da sace suga da kuma shinkafar da aka bayar a cikin watan azumi domin a raba wa fursunonin.

Sai dai a bangaren ma’aikatan gidan yarin, kamar yadda wani daga cikinsu ya shaida mana; suna ganin wannan boren da fursunonin suka yi, sun yi ne domin tabbatar da wani ikirari da suke yi na cewa babu doka a gidan yari bayan karfe 6:00 na yamma.

Ya ce, yadda wannan boren ya fara, ya yi nuni da haka saboda fursunonin da suka yi boren sun fasa dakunansu a daidai wannan lokacin ne, sannan suka shiga fasa sauran dakuna domin sauran fursunoni su fito su shiga cikin su.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton dai Hukumar ’yan sanda sun bayar da sanarwar mutuwar mutane uku a wannan boren, tare da jikkata wani adadi mai yawa.

Kazalika an kuma an ba da sanarwar samun nasarar fitar da fursunoni mata wadanda aka ce masu boren sun yi barazanar yi musu fyade.

Duk da sanarwar da Hukumar ’yan sanda ta bayar na adadin wadanda suka mutu, mutanen garin Sakkwaton na hangen cewa adadin ya fi haka, suna cewa yawan mutanen ya zarta haka nesa ba kusa ba.

Tun lokacin faruwar abin zuwa wannan lokacin an tsaurara tsaro a gidan yarin, inda aka hana kowa shiga sai ma’aikatan gidan da kuma jami’an bincike wadanda ke binciken wasu fursunoni da ke da hannu a boren.

Yanzu dai gawawwakin wadanda aka kashe da kuma wadanda aka raunata suna

asibitin kwararru da ke Sakkwato.

Mafi yawan mutane sun ido don su ga wane irin sakamako ne masu binciken za su fitar, da kuma irin matakin da gwamnati za ta dauka domin magance sake faruwar makamancin haka a nan gaba.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International