Almizan :Ba zamu yarda Obasanjo yayi tazarce ba ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426                 Bugu na 694                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Ba za mu yarda Obasanjo ya yi tazarce ba

In ji Gwamna Shekarau


o.
i

   

A ranar Talatar da ta gabata ne, Editanmu ya kasance cikin wata tawagar Editocin manyan jaridun Turanci na Arewa, wato jaridar Weekly Trust da Leadership, inda suka yi hira da Malam Ibrahim Shekarau, Gwamnan jihar Kano a fadar gwamnatin ta jihar, wanda kuma aka watsa shi kai tsaye ta gidan rediyon jihar da kuma talabijin na jihar. A yau somin tabin hirar za mu kawo saboda tsawonta. Wanda ya shirya hirar shi ne Dakta Mahdi Shehu. Masu rufa masa baya a hirar sune Garbadeen Muhammad, wanda da Editan Weekly Trust ne, amma yanzu likkafa ta yi gaba ya zama Manajan jaridun Trust, sai kuma Editan Leadership, Ibrahim Sheme.

A sha karatu lafiya.

EDITOCI: Yanzu ka yi shekaru biyu kana Gwamna, akwai bambanci a tunaninka kafin ka zama Gwamna da abubuwan da ka gani a kasa?

GWAMNA SHEKARAU: Alhamdu lillah kamar yadda ka fada tun kafin Allah cikin ikonsa in yi ritaya, har ma bisa shawarwari da kuma nufi na Allah (T) in tsinci kaina cikin harkokin siyasa, na yi aiki na Hukuma na gwamnati tsawon shekaru 26. Daga cikin shekarun nan, kusan sama da shekaru goma na karshe ina cikin harkar shugabanci da gudanarwa na sashi daban-daban na gwamnati, har na tsinci kaina a tsololuwar cibiya wadda aka fi sani da ‘Cabinet office’ na Sakataren gwamnati. Wannan ya ba ni dama na san me gwamnati take ciki a aikace.

Sad da na shiga harkokin siyasa, na soma hada-hadar yin takara, duk wadannan abubuwa sun dada bijirowa a karjina, har kuma ina tunanin in Allah ya ba ni nasara ga irin abin da zan sa a gaba.

Bahaushe yana cewa hangen dala ba hawa dala bane Mun sani abubuwa da dama sai ka zo za ka kara fahimtar su. Tabbas bayan na zama Gwamna, Allah ya ba ni wannan nauyi na samu karin haske a kan abubuwan da na sani da. A gwamnatance da ma yawancin abubuwan nan na riga na san su, illa yadda mu’amalarsu take a gwamnati na siyasa da kuma irin yadda bukatun mutane na birni da kauye da matsalolin da suke kasa, wadanda za ka gan su kuru-kuru, gaskiya sai bayan na zo wannan mukami na dada ganin su a fili, kuma ya zama wani kalubale. Illa na yi godiya ga Allah cewa ina da waccan masaniya na ya za a tafi da wadannan al’amura.

EDITOCI: Gafarta Malam an ce in dai kana gari, kusan a kowane mako kakan ziyarci wata Karamar Hukuma, shin me ka gano, ina zargin cewa kashe-mu-raba ake yi a Kananan Hukumomi kan kudaden al’umma?

GWAMNA SHEKARAU: Gaskiya ne cewa muna yin kokari kwarai wajen ziyartar Kananan Hukumomi, ziyara ta gani da ido kan ayyukan da suke yi. Mukan sa su a sikeli mu auna da irin kudaden da suke samu da kuma ayyukan da muke amince musu su yi. Har zuwa yau sai dai mu ce alhamdulillahi, don ba mu ci karo da wani abin assha wanda zai ta da hankali ba. Zan iya cewa iya gwargwado mun gamsu da irin yadda Kananan Hukumomin nan suke hobbasa wajen aiwatar da ayyuka na ci gaba na raya yankunansu. Wani abin da yawancin mutane ba su sani ba shi ne, yawancin ayyukan nan Kananan Hukumomi da Kansilolinsu, duk da sune doka ta ba dama su zauna su zartar da hukuncin wane aiki za su yi. Akwai wata ka’ida da in suka wuce sai sun kawo wa Ma’aikatar Kananan Hukumomi a ba su izini. Haka in kudin sun yi yawa. A Ma’aikatar nan akwai sashe sukutum da aka ware wa wannan aiki. Wannan gaskiya yana taimaka mana kwarai wajen bin diddigi. Yanzu muna shirin inganta ‘zonal Inspecorates’ dinmu don su sa ido su ga me ake yi. Duk da cewa mun gamsu da ayyukansu, wannan ba yana nufin ba za ka samu kurakurai nan da can ba. Amma duk inda aka samu ana bin sawu a ja kunne, a tabbatar an gyara. In ma ya kama a dau mataki na ladabtarwa ta hanyar aiki, duk ana yi.

EDITOCI: Kamar yadda kowa ya sani, akwai rade-radin wani shiri na Shugaba Obasanjo na ta-zarce a karo na uku, za mu so mu ji ra’ayinka a kan wannan al’amari.

GWAMNA SHEKARAU: Ina ganin kafin mu kawo kan menene ra’ayina kan Obasanjo ya zarce ko kar ya zarce, ko ya kara shekara uku ko hudu nan gaba, ina ganin kusan a dunkule zan iya cewa Gwamnonin jihar Arewa sun ba da amsa kan wannan matsayi. Domin mun yi taro gaba dayanmu, kuma da ma can mun taba yi a bara, cewa mu a matsayinmu na Gwamnoni na Arewa mu 19 na PDP da ANPP, mun zartar cewa lalle mulki na kasar nan, lalle ya dawo wannan sashe na Arewa, an samu wannan yarda a tsakaninmu, in ya so kowannenmu ya koma jam’iyyarsa ya yi rigimar dan Arewa ne zai yi musu takara na Shugaban kasa.

Wannan ma ya ishe mu ba sai mun fito mun ce mun yarda ko ba mu yarda ba Obasanjo ya zarce, tunda dai dan kudu ne. Mako daya da ya wuce mun sake yin taro, mun sake jaddada wannan matsayi a matsayinmu na Gwamnoni, mun ce duk abin da za mu yi a bisa tsarin mulki, bisa doka da ta ba da dama, za mu hada kai da wadanda suke da ra’ayi irin namu a nan Arewa da kuma kudu, adalci shi ne bayan an shekara takwas dan kudu yana mulki, to mulkin nan ya dawo Arewa. In mun samu wannan fahimtar sai a dawo Arewa a ga su waye za su yi takarar. Kuma kowace jam’iyya ya rage nata ta yanke hukunci. Zancen shekara ta 2007, ko yana so ko ba ya so mun zartar cewa ba ma bukatar dan kudu ya yi takara. Ka ga za a iya fassara wannan da cewa matsayarmu ita ce ba mu yarda da ya zarce ba. Da a Arewa yake, sai a ce watakila wata dabara ce, amma tunda dan kudu ne tilas ya hakura, mulki ya dawo Arewa. Wannan shi ne matsayarmu, kuma shi ne matsayina.

EDITOCI: Sau da yawa wasu na kukan cewa ana samun jinkiri wajen aiwatar da ayyukan gwamnati, musamman idan Gwamna ya ba da umurnin a yi kaza a rubuce. Gwamna na sane da haka? In yana sane, me ke jawo haka?

GWAMNA SHEKARAU: Ba za a ce ba a jin koke-koke ba. Sa’ar da muka ji duk wani korafi muna bin sawu, illa abin da zan yi bayani a kai shi ne ta yiwu wanda yake daga waje, abin da yake ganin cewa jinkiri ne ko rashin tafiyar abin da gaggawa yadda yake so, ya gan shi bai da illa, amma mu kuma a cikin gida muna ganin wani taka-tsantsan ne don a tabbatar komai an sa shi a muhallinsa. Na farko dai yana daga cikin sharuddanmu, abin da muke kira ka’idoji guda goma da muka tsara wa kanmu tun zuwan gwamnati, duk abin da za mu yi a tabbatar da shi a tsare. A tabbatar da nufinsa da ma’anarsa da dalilin yin sa. Sannan na biyu a tabbatar da cewa, musamman abin da ya shafi kashe kudi, akwai tanadinsa a cikin kasafin kudi, domin mu dawo da abin da ake cewa ‘budget dispiline’. Ba kawai Gwamna ya wayi gari kurum ya ce a kashe kaza, a je a yi aiki kaza, tunda tare muke da ’yan majalisar nan.

Ta kai ga duk wanda zai rubuto daga wata Ma’aikata yana neman ko kwabo ne, sia ya gaya mana sunan ajin da za a samu wannan kudin a cikin littafin kasafin kudi. Don ma mutane su gamsu kuma kowace ma’aikat ta gamsu ana bin wannan, sama da shekaru goma kafin mu zo ba a buga littafin kasafin kudi a Kano. In Gwamna ya yi jawabinsa a rediyo ya sanar shi kenan. Ta yiwu kasafin na Ma’aikatar kasafin kudi a ajiye, kila Gwamna ma bai damu ya ajiye a kusa ba, amma zuwanmu ne muka dawo da tsohon tsari, kuma shi ne daidai. A buga kwafi na kasafin kudi, sai da shi ake. Don mutum ya ga me Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta yi a shekara ta 2005?

Na gaya wa Ma’aikatar kudi da kasafin kudi cewa ko na ba da ‘approval,’ takarda ta zo, in suka ga cewa akwai kuskuren ajin kudin ko kuma akwai ayar tambaya, kar a ce tunda Gwamna ya sa hannu a je a biya, a dawo da shi. Shi ne kima, shi ne girma, kuma ni shi ne amanar da na ba su.

Yawancin abin da ke jawo wannan korafin bai wuce mutum yana son a gaggauce wannan abin ya fita ba, amma aka zo aka ci karo da wancan jinkiri da tsatsuba ta bincike, wani sai ya ga kamar ko kin bin umurni ne.

Yanzu misali mutum ya rubuto cewa yana da korafi a Ma’aikatar filaye misali, ga wani filina can an zalunce ni. Wani zai ga ai takardarsa ta shigo ofishin Gwamna, so yake kawai in yanke hukunci in ce da Kwamishinan filaye a mayar masa da filinsa. Shi bai san abin ba haka bane. Sai na ce da Kwamishinan filaye a binciki maganar nan gaskiya ne abin da mutumin nan ya fada? Ku fadi naku labarin, shi ga abin da ya ce. To in ya ga sati daya biyu ba bayani, shi bai san cewa Kwamishina sai ya ga Perm. Sec, shi kuma sai ya ga Darakta, shi kuma ya ga Surveyor. Mai yiwuwa Kwamishina ba zai yanke hukunci ba sai ya sake dawo min, sannan ne zan yanke hukunci.

Komawa babban shafinmu        Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International