Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Shaikh Zakzaky ya tabbatar duk wani mai hankali, idan har ya kalli lamarin Imam Khumani, zai fahimci cewa na Allah ne...ci gaba
Da la’asariyyar ranar Lahadin nan da ta gabata ne, ’yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na Da’irar Kano suka je fadar Sarkin Kano yin ta’aziyyar rasuwar Sarkin...ci gaba
Rahotanni daga jihar Borno sun ce, wasu ’yan bindiga sun sace wasu mata Fulani masu yawa a wata Rugar Fulani...ci gaba
Kungiyar ’yan jarida ta kasa, NUJ, ta ce za ta nemi sojojin kasar nan da su biya diyya saboda sun janyo musu cikas a gudanar da ayyukansu...ci gaba
Rahotannimu
A kwanakin baya ne uwar kungiyar dillalan man fetur ta kasa, wato IPMAN, ta gudanar da zaben manyan jami’anta na kasa a birnin tarayyar Abuja, inda aka zabi shugabaninta da za su rike mukamai na kasa a kungiyar...
Shugaban Hukumar kula da ingancin magunguna da kayan abinci, NAFDAC, a jihar Neja, Mista Dadi Nantim Mullah ya bayyana yadda Hukumar ke ayyukanta don muhimmantar da rayuwar al’umma, lokacin da yake zantawa da Wakilinmu a ofishinsa da ke Sakatariyar gwamnatin Tarayya da ke Minna, a makon jiya...
Jawabai da Karatun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H):
Hoton Bidiyo:
Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.
Labaran Harka Islamiyyah
Tunatarwa:
Tare da Sayyid Zakzaky Wannan wani bangare ne na jawabin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a taron Yaumus Shuhada na ranar Asabar 25 ga Rajab, 1435 a filin Polo kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta mana.
IN DA KOWA ZAI BA DA HAKKIN SHUHADA
Sakamakon ’yan uwa suna gyara kaburburan Shahidai har wasu ma sun fara koyo. To, amma inda mutum zai je sauran duniyar musulmi zai ga cewa, wannan abu ne zaunanne. Ana kyautata makwantan mutane, ana kuma tunawa da su ta nan. To, Shuhada’u ‘khasatan’ da ma dukkan sauran wadanda suka mutu. Amma ‘khasatan’ Shuhada suna da wannan hakkin.
Sannan kuma suna da hakki na kula da iyalansu, ainihin abin da suka bari baya - matansu da ’ya’yansu da iyayensu. Har wala yau, wannan yana dan dada sanyaya rai. Ya dan kwantar da hankalin mutum, ya rika tunawa da nasa. Da zafi mun sani. Da zafi! Da zafi, amma kuma zai dan sa shi ya yi tunanin cewa, ran dansa, bai tafi a kawai ba, insha Allah...
A ranar Asabar din nan da ta gabata ne, Madrasatul Fudiyya Zariya ta yi bikin yaye dalibai a bangaren manya da kananan makarantun sakandire, yayin da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya zama babban bako a wajen taron...
Ra'ayin Almizan
Babban labarin mujallar Tell News Magazine na ran 17 ga Yun, 2013 No. 24 da aka yi wa kanu: Sabuwar matsalar tsaro: Rawar Gabas ta tsakiya” (New Security Threat: The Middle East Connection), abin damuwa ne. Wani wai shi ANAYOCHUKWU AGBO ne ya rattaba wannan ‘tatsuniyar” da ...muke magana a kai. A takaicen takaitawa, bangaren makalar tasa da aka yi kokarin nuna cewa Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Shugabanta abin girmamawa, ’yan tashin hankali ne masu mummunar manufa, ya nuna yadda marubucin yake dan baranda, wanda bai san abin da yake magana a kai ba...
Daga Gidan Annabta
Tare da Abubakar Abdullahi Almizan
SALLAR DAREN ASHIRIN DA HUDU NA RAJAB
Salla raka’a 40, kowace raka’a Fatiha 1, Amanarrasulu 1, Kulhuwallahu 1. Allah zai rubuta wa wanda ya yi wannan Sallar ladar kyawawan ayyuka 1000, Ya kuma goge masa laifuka 1000, Ya daukaka darajarsa sau 1000.
SALLAR DARE NA ASHIRIN DA BIYAR
Salla raka’a 20, kowace raka’a Fatiha 1, Amanar-rasulu…1, Kulhuwallahu 1. Wanda ya yi wannan Sallar, Allah zai tsare shi daga kowace irin musifa. Kuma Allah zai azurta shi da kubuta daga sharrukan duniya da lahira...
Katun
Sanarwa
Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Gagarumin majalisin mawaka wanda Alh Mustapha Umar Baba Gadon Kaya jai jagoranta
Gasar fareti da Harisawa zasu gabatar
Akwai walimar bukin Nisfu Sha'aban bayan sallolin Magriba da Isha'i.
Mai karbar fareti: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan yaye daliban makarantar Fudiyyah Zaria na bana
Tambihi:
Tare da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna