Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Babban Labari

NUJ za ta nemi sojoji su biya diyyar kwace jaridu da suka yi


NUJ

Kungiyar ’yan jarida ta kasa, NUJ, ta ce, za ta nemi sojojin kasar nan da su biya ’ya’yanta diyya saboda sun janyo musu cikas a gudanar da ayyukansu a kwanakin baya...

Sojojin dai sun hana a rarraba jaridu a wuraren sayar da su a garuruwan Kano, Kaduna, Fatakwal da Abuja, “saboda dalilan tsaro,” kamar yadda suka ce.

Duk da cewa a yanzu an kawo karshen lamarin, kungiyar ta NUJ ta ce ya kamata sojojin su biya diyya saboda asarar da suka janyo, kamar yadda Shugaban NUJ din, Malam Muhammad Garba ya shaida wa manema labarai.

Ya ce, “a gaskiya abin ya faru ranar Alhamis da ranar Juma’a ne. To, amma a ranar Asabar zuwa Lahadi zuwa yau din nan, sun dakatar da wannan barazana da kama masu sai da jaridu da hana su sayarwa. Amma duk da haka muna ganin bai kamata a ce mun bar abin haka ba, saboda haka a yau din nan mun yi taron gaggawa da kungiyoyin Editocin Nijeriya da masu kafafen watsa labarai na Nijeriya, mun fito da wata takarda da muke nuna rashin gamsuwarmu da damuwarmu da korafinmu dangane da yadda wadannan abubuwa suka faru. Kuma mun yi kira ga Hukumomin tsaro su tabbatar da cewa abubuwan nan da suka faru ba za a sake yin su a nan gaba ba.”

To, tunda an yi kwanaki biyu ana wannan abin, an jawo muku asarori na miliyoyin Nairori, shin za ku bar wa Allah ne, ko za ku nemi a biya ku diyya? Tambayar da aka yi wa Shugaban NUJ ke nan. Sai ya ce, “Za a biya mu diyya a wannan takarda da muka fito da ita.”

To, diyyar da za ku nema, za ta kai ta nawa? Aka tambaye shi. “Muna nan mun tattauna da wadannan ’yan kungiyoyi daban-daban, kuma mun umurci kowane gidan jarida ya ba mu kiyasin abubuwan da aka yi asara, domin mu hada alkalumma, mu tura wa hukumar soja ta Nijeriya.”

An kuma tambayi, Malam Muhammad Garba, shin a baya an taba amfani da motocin jigilar jaridun nan wajen safarar wasu abubuwan tsaro ne kamar yadda Hukumomi ke cewa, ko ko ina matsalar take? Sai ya ce, “Abin da muke cewa shi ne in ma an taba amfani da su wajen jigilar makamai kamar yadda suke tsammani, to ai sun yi kwana biyu suna wannan bincike, da ranar Alhamis da ranar Juma’a. To, ya kamata a yanzun nan su fito su gaya wa ’yan Nijeriya me suka binciko, me suka gano? Idan har ba su binciko sun gano irin wadannan abubuwan da suke tunani ko zargi ba, to ina so in tabbatar muku cewa ni ban taba samun labarin an yi amfani da motoci domin a yi jigilar makamai ko kuma abubuwa makamantan haka ba.”


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

    GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
    Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
    Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

    Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

    Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
    Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


    Labarai cikin hotuna

    Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron